Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • km 7/12 p. 8
  • Sanarwa

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Sanarwa
  • Hidimarmu Ta Mulki—2012
Hidimarmu Ta Mulki—2012
km 7/12 p. 8

Sanarwa

◼ Littattafan da za a ba da a Yuli da Agusta: Ku yi amfani da kowanne ɗaga cikin ƙasidun nan masu shafuffuka 32: Ka Saurari Allah ko kuma Ka Saurari Allah Don Ka Rayu Har Abada, Za Ka Iya Zama Abokin Allah! kuma ku yi ƙoƙari don ku soma nazarin Littafi Mai Tsarki da mutane. Sa’ad da kuke koma ziyara, ku gabatar da littafin nan Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa? ko kuma ku yi amfani da wata ƙasidar da ta dace da yanayin mutumin. Satumba da Oktoba: Mujallun Hasumiyar Tsaro da Awake! Sa’ad da kuke komawa don ku ziyarci mutane, ku gabatar da littafin nan Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa? ko kuma ƙasidun nan Ka Saurari Allah ko Ka Saurari Allah Don Ka Rayu Har Abada, idan sun dace da yanayin mutumin, kuma ku ƙoƙarta don ku soma nazarin Littafi Mai Tsarki da shi.

◼ Za ku iya saukar da Sing to Jehovah—Vocal Renditions, faifai na 5 daga Yanar Gizo na jw.org somawa daga 1 ga Agusta. Za a fara saka na Turanci a dandalin, sa’an nan daga baya a saka na wasu harsuna. Za ku iya ce a aiko muku da faifan ta wurin ikilisiyarku. Tun da yake saukar da abubuwa daga Yanar Gizo ba ya cin kuɗi sosai kamar buga da kuma aika fayafayan, muna ƙarfafa ’yan’uwa da za su iya saukarwa daga dandalin su yi hakan. An riga an fitar da fayafaye na 1-4.

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba