Bitar Makarantar Hidima Ta Allah
Za a amsa waɗannan tambayoyi na gaba a Makarantar Hidima ta Allah a makon 25 ga Yuni, 2012. An saka kwanan watan da za a tattauna waɗannan bayanan domin ku yi bincike sa’ad da kuke shirya makaranta duk mako.
1. Ta yaya ne Jehobah ya nuna ƙaunarsa ga Irmiya a lokacin da aka yi wa Urushalima barazana? (Irm. 37:21) [7 ga Mayu, w08 10/15 shafi na 10, sakin layi na 18]
2. Mene ne ba daidai ba a roƙon da Zedekiya ya yi game da ja-gorar Jehobah? (Irm. 38:14-19) [7 ga Mayu, w03 5/1 shafi na 10, sakin layi na 9]
3. Me ya sa kuma ta yaya Jehobah ya nuna godiyarsa ga Ebed-melek? [14 ga Mayu, w07 2/1 shafi na 19, sakin layi na 7]
4. Waɗanne ‘manyan abubuwa’ ne Baruch ya ci gaba da biɗa? (Irm. 45:5) [21 ga Mayu, w11 6/15 shafi na 30 sakin layi na 1]
5. A waɗanne hanyoyi biyu aka gwada biyayyar Irmiya sa’ad da Jehobah ya umurce shi ya gaya wa Yahudawan da aka kewaye su su ba da kansu ga Chaldiyawa? (Irm. 50:2, 11) [28 ga Mayu, w02 10/1 shafi na 15 sakin layi na 17]
6. Bayan da ’yan Midiya da Farisa suka ci Babila, wane irin gudu ne ya zama dole? (Irm. 51:6, 45, 50) [4 ga Yuni, w08 6/15 shafi na 8 sakin layi na 8-9]
7. Mene ne ‘matashin sawun’ Jehobah da kuma ‘shimgensa’? (Mak. 2:1, 6) [11 ga Yuni, w07 6/1 shafi na 9, sakin layi na 2]
8. Mene ne Irmiya yake nufi sa’ad da ya ce Jehobah zai ‘tuna da shi kuma ya taƙure,’ kuma me ya sa hakan yake da muhimmanci sosai a gare mu? (Mak. 3:20) [18 ga Yuni, w07 6/1 shafi na 11, sakin layi na 3]
9. Me ya sa yake da kyau mutum ya saba da wahala tun yana yaro? (Mak. 3:27) [18 ga Yuni, w07 6/1 shafi na 11, sakin layi na 5]
10. Ta yaya misalin Ezekiyel zai taimaka mana mu yi wa’azi da gaba gaɗi ko da mutane ba sa son saƙonmu? (Ezek. 3:8, 9) [25 ga Yuni, w08 7/15 shafuffuka na 8-9, sakin layi na 6-7]