Tambayoyi Daga Masu Shela
◼ Me ya kamata mu yi la’akari da shi idan muna son a ba ƙungiyar Jehobah dukan mallakarmu ko wasu daga cikinsu bayan mutuwarmu?
Mutane ba su da wani iko bisa dukiyarsu sa’ad da suka mutu. (M. Wa. 9:5, 6) Saboda haka, kafin su mutu, yawancin mutane suna barin wasiyya wadda take ɗauke da yadda za a raba dukiyar da suka bari. (2 Sar. 20:1) A cikin wasiyyar, mutumin zai rubuta sunan wanda ya ba amanar rarraba dukiyarsa. A ƙasashe da yawa, idan bai bar wasiyya ba, hukuma za ta yanke shawarar yadda za ta rarraba dukiyar mamacin. Saboda haka, idan akwai yadda muke so a bi da dukiyarmu, alal misali a ba ƙungiyar Jehobah duka ko kuma wasu daga cikin dukiyarmu, yana da muhimmanci mu rubuta hakan kuma mu zaɓi wanda zai iya riƙe wannan amanar.
Mutumin da aka ba wannan amanar yana da hakki mai nauyi a kansa. Bisa ga yawan dukiyar, tattara su da kuma rarraba su zai ƙunshi abubuwa da yawa kuma hakan yana ɗaukan lokaci sosai. Ƙari ga haka, sau da yawa hukuma tana kafa dokokin da suka wajaba a bi su. Ba kowane ɗan’uwa a cikin ikilisiya ba ne zai iya riƙe irin wannan amanar ba. Ya kamata mu tabbata cewa wanda muka zaɓa mutumi ne mai aminci wanda zai iya yin aikin, zai riƙe amana kuma zai bi wasiyyar da muka bari.—Ka duba talifin nan “The Wisdom and Benefits of Estate Planning,” a Awake! na 8 ga Disamba, 1998, a Turanci.
Idan Wani Ya Ba Ka Amanar Raba Dukiyarsa: Idan wani ya tambaye ka ko za ka yarda ka yi masa wannan aikin bayan ya mutu, ka tabbata cewa ka zauna ka yi lissafin abin da hakan zai ƙunsa kuma bayan ka yi addu’a sai ka yanke shawarar ko za ka iya yin aikin ko a’a. (Luk. 14:28-32) Bayan mutuwar mutumin, kana bukatar ka sanar da dukan waɗanda za su ci gadon abin da mamacin ya faɗa. Da zarar ka samu izinin yin haka, ka rarraba dukiyar daidai yadda aka umurta a cikin wasiyyar bisa ga doka. Wanda aka ba riƙon amana ya san cewa ko da dukiyar na da yawa ko a’a, bai kamata ya keta dokar da aka ba da a cikin wasiyyar ba. Duk wata kyautar da aka bar wa Watch Tower, sun zama keɓaɓɓun kuɗin ƙungiyar Jehobah.—Luk. 16:10; 21:1-4.