Dalilai Sha Biyu da Suka Sa Muke Yin Wa’azi
Me ya sa muke yin wa’azin bishara kuma muke koya wa mutane Littafi Mai Tsarki? Shin muna yin hakan ne musamman don mu taimaka wa mutane masu zuciyar kirki su samu hanyar rai ne? (Mat. 7:14) Wannan shi ne dalili na farko a jerin da ke ƙasa, amma ba shi ne ainihin dalilinmu na yin hakan ba. A ganin ka, wanne ne cikin waɗannan dalilai 12 da suka sa muke yin wa’azi ya fi muhimmanci?
1. Sa’ad da muka yi wa’azi, muna ceto rayukan mutane.—Yoh. 17:3.
2. Sa’ad da muka yi wa’azi, muna yi wa miyagun mutane gargaɗi.—Ezek. 3:18, 19.
3. Sa’ad da muka yi wa’azi, muna cika annabcin Littafi Mai Tsarki.—Mat. 24:14.
4. Sa’ad da muka yi wa’azi, hakan yana bayyana adalcin Allah. Babu wanda zai zargi Jehobah da cewa ya halaka miyagu ba tare da ya ba su zarafin tuba ba.—A. M. 17:30, 31; 1 Tim. 2:3, 4.
5. Sa’ad da muka yi wa’azi, hakan yana sa mu cika hakkin da muke da shi na taimaka wa mutanen da aka fansa da jinin Yesu, su san kalmar Allah.—Rom. 1:14, 15.
6. Sa’ad da muka yi wa’azi, hakan yana taimaka mana mu guji ɗaukan alhakin jinin mutane.—A. M. 20:26, 27.
7. Muna bukatar mu yi wa’azi idan muna so mu samu ceto.—Ezek. 3:19; Rom. 10:9, 10.
8. Sa’ad da muka yi wa’azi, muna nuna cewa muna ƙaunar maƙwabtanmu.—Mat. 22:39.
9. Sa’ad da muka yi wa’azi, hakan yana nuna cewa muna yin biyayya ga Jehobah da kuma Ɗansa.—Mat. 28:19, 20.
10. Yin wa’azi sashe ne na bautarmu.—Ibran. 13:15.
11. Sa’ad da muka yi wa’azi, muna nuna cewa muna ƙaunar Allah.—1 Yoh. 5:3.
12. Sa’ad da muka yi wa’azi, hakan yana sa a tsarkake sunan Jehobah.—Isha. 43:10-12; Mat. 6:9.
Hakika, ba waɗannan ne kaɗai dalilan da suke sa muke yin wa’azi ba. Alal misali, yin wa’azi yana ƙarfafa bangaskiyarmu kuma ya ba mu gata na musamman na yin aiki tare da Allah. (1 Kor. 3:9) Amma, dalili mafi muhimmanci da ya sa muke yin wa’azi shi ne na 12. Ko da mutane sun saurare mu ko a’a, yin wa’azi yana sa a tsarkake sunan Allah kuma ya na ba Jehobah damar mayar da martani ga wanda yake zarginsa. (Mis. 27:11) Hakika, muna da dalilai masu kyau da suka sa ba ma ‘fāsa koyarwa da yin wa’azi cewa Yesu Kristi ne.’—A. M. 5:42.