Tsarin Ayyuka na Makon 11 ga Yuni
MAKON 11 GA YUNI
Waƙa ta 123 da Addu’a
□ Nazarin Littafi Mai Tsarki Na Ikilisiya:
cl shafuffuka na 192-196 (minti 25)
□ Makarantar Hidima Ta Allah:
Karatun Littafi Mai Tsarki: Makoki 1-2 (minti 10)
Na 1: Makoki 2:11-19 (minti 4 ko ƙasa da hakan)
Na 2: A Wace Hanya Ce Mutane Suke “Halaka duniya”?—R. Yoh. 11:18 (minti 5)
Na 3: Nawayar Iyaye Kirista ga Yara—td 7C (minti 5)
□ Taron Hidima:
Waƙa ta 134
Minti 5: Sanarwa.
Minti 10: Mene Ne Muka Cim Ma? Sakatare ne zai yi wannan tattaunawar. Ka ambata abin da aka cim ma a lokacin Tunawa da mutuwar Yesu, kuma ka yaba wa ikilisiya saboda ƙoƙarin da ta yi. Ka ba masu sauraro dama su faɗi labarai masu daɗi na abubuwan da suka faru a lokacin da aka rarraba takardar gayyata na zuwa taron Tunawa da mutuwar Yesu, a lokacin da suka koma ziyara wajen sababbin da suka halarci taron da kuma sa’ad da suka yi hidimar majagaba na ɗan lokaci.
Minti 20: “Dalilai Sha Biyu da Suka Sa Muke Yin Wa’azi.” Tattaunawa.
Waƙa ta 47 da Addu’a