Ku Yi Taka-Tsantsan Sa’ad da Kuke Wa’azi
1. Me ya sa yake da muhimmanci mu yi taka-tsantsan sa’ad da muke wa’azi?
1 “Kamar tumaki cikin tsakiyar kerketai,” bayin Allah suna wa’azi “a zamanin mutane karkatattu, kangararru.” (Mat. 10:16; Filib. 2:15, Littafi Mai Tsarki) Rahotanni masu ta da hankali a kan tarzoma da ta’adanci da sace mutane sun zama ruwan dare, kuma hakan na nuna cewa miyagun mutane suna “daɗa mugunta gaba gaba.” (2 Tim. 3:13) Waɗanne ƙa’idodi na Nassi ne za su iya taimaka mana mu yi taka-tsantsan sa’ad da muke wa’azi?—Mat. 10:16.
2. Wane yanayi ne zai sa mu bar wani yanki kuma mu je wani dabam don mu ci gaba da wa’azi?
2 Ku Mai da Hankali: Misalai 22:3 ta nuna cewa hikima ce mutum ya “ɓuya” sa’ad da muka hangi masifa. Ku kasance a faɗake! Abubuwa suna iya canjawa ba zato ba tsammani a yankin da a dā ake zaman lafiya. Kana iya ganin ’yan sanda da yawa suna yawo ko kuma jama’a suna taruwa a titi. A wasu lokatai, wani mutumin kirki a yankin yana iya gaya mana cewa wani abu zai faru. Maimakon son ganin kwaf ya hana mu tafiya, zai dace mu bar wurin nan da nan kuma mu koma wani wuri dabam.—Mis. 17:14; Yoh. 8:59; 1 Tas. 4:11.
3. Yaya za mu iya amfani da ƙa’idar da ke littafin Mai Wa’azi 4:9 sa’ad da muke wa’azi?
3 Ku Yi Aiki Tare: “Gwamma biyu da ɗaya,” in ji littafin Mai Wa’azi 4:9. Wataƙila ka saba fita wa’azi kai kaɗai, zai dace ka ci gaba da yin hakan ne yanzu? A wani yanki, hakan ba zai zama matsala ba. Amma a wasu wurare kuwa ba zai dace ’yar’uwa ko matashi ya yi wa’azi a gida-gida shi kaɗai ba, musamman ma bayan faɗuwar rana. Abubuwan da suka faru a dā sun nuna cewa samun abokin wa’azi mai hattara yana da tamani sosai. (M. Wa. 4:10, 12) Ku sa ido a kan sauran ’yan’uwanku da kuke wa’azi tare da su a yankin. Sa’ad da kuke wa’azi tare, ku tabbata cewa kun gaya ma sauran kafin ku bar yankin.
4. Ta yaya za mu iya taimakawa wajen kāre dukan ’yan’uwa da ke ikilisiyarmu?
4 A matsayin waɗanda suke ‘yin tsaro sabili da rayukanmu,’ dattawa ne ke da hakkin yi mana ja-gora mai kyau daidai da yanayin yankinmu. (Ibran. 13:17) Jehobah zai albarkace mu idan muka nuna sanin yakamata tare da ba su haɗin kai sosai. (Mi. 6:8; 1 Kor. 10:12) Bari dukan bayin Allah su ci gaba da yin wa’azi mai kyau a yankinmu, amma su riƙa yin taka-tsantsan.