Ayyuka na Makon 7 ga Mayu
MAKON 7 GA MAYU
Waƙa ta 120 da Addu’a
□ Nazarin Littafi Mai Tsarki na Ikilisiya:
cl shafi na 176 zuwa 178 da akwati (minti 25)
□ Makarantar Hidima Ta Allah:
Karatun Littafi Mai Tsarki: Irmiya 35-38 (minti 10)
Na 1: Irmiya 36:14-26 (minti 4 ko ƙasa da hakan)
Na 2: Rai na Har Abada ba Mafarki Ba Ne—td 35A (minti 5)
Na 3: Shin Ayyukan ’Yan Adam Za Su Iya Shafan Yadda Allah Yake Ji Ne?—Alƙa. 2:11-18 (minti 5)
□ Taron Hidima:
Waƙa ta 91
Minti 5: Sanarwa.
Minti 15: “Wasiƙa Daga Hukumar Mulki.” Tattaunawa da aka ɗauko daga ’yar ciki mai shafuffuka biyu na Hidimarmu Ta Mulki ta watan Afrilu, 2012. Ka gayyaci masu sauraro su faɗi abubuwa da suka gano daga fannoni na musamman a rahotonmu na dukan duniya da ke ’yar cikin Hidimarmu Ta Mulki ta watan Maris, 2012. Idan zai yiwu, ka yi shiri tun da wuri don wasu su ba da labari mai ƙarfafawa daga 2012 Yearbook. A ƙarshe, ka ƙarfafa dukan waɗanda suke karanta Turanci su karance 2012 Yearbook.
Minti 15: Bukatun ikilisiya. Jawabin da za a gabatar da awutlayin nan mai jigo, Taron Gunduma na Shaidun Jehobah na Shekara ta 2012.
Waƙa ta 14 da Addu’a