Bitar Makarantar Hidima ta Allah
Za a amsa waɗannan tambayoyi na gaba a Makarantar Hidima Ta Allah a makon 30 ga Afrilu, 2012. An saka kwanan watan da za a tattauna waɗannan bayanan domin ku yi bincike sa’ad da kuke shirya Makarantar Hidima ta Allah duk mako.
1. Me ya sa yake da muhimmanci mu bincika littafin Irmiya? [5 ga Maris, w07 4/1 shafi na 8 sakin layi na 2]
2. Ta yaya Jehobah zai iya cece mu daga tsanantawa a yau? (Irm. 1:8) [5 ga Maris, w06 1/1 shafi na 15, sakin layi na 18]
3. A wane lokaci ne shafaffu suka koma ga “hanyoyi na dā” kuma ta yaya suka yi hakan? (Irm. 6:16) [12 ga Maris, w05 11/1 shafi na 28, sakin layi na 12]
4. Me ya sa sarautar ’yan Adam ba za ta yi nasara ba? (Irm. 8:9) [19 ga Maris, w10 1/15 shafi na 24, sakin layi na 4]
5. Bisa ga littafin Irmiya 17:7, 8, me ya kamata mu yi don mu ci gaba da ba da ’ya’ya? [2 ga Afrilu, w11 3/15 shafi na 14, sakin layi na 9]
6. Ta yaya ne Jehobah ya yi amfani da ‘ƙarfinsa’ a kan Irmiya kuma ya ruɗe shi? (Irm. 20:7) [2 ga Afrilu, w07 4/1 shafi na 9, sakin layi na 3]
7. Shin dokar da ke Irmiya 22:30 ta kawar da ikon Yesu Kristi ne na hawan kursiyin Dauda? (Mat. 1:1, 11) [9 ga Afrilu, w07 4/1 shafi na 10, sakin layi na 1]
8. Ta yaya iyaye za su iya yin koyi da Jehobah sa’ad da suke koyar da yaransu? (Irm. 30:11) [23 ga Afrilu, w07 9/1 shafi na 24, sakin layi na 14]
9. Yaya ake rubuta shari’ar Allah a cikin zuciya? (Irm. 31:33) [23 ga Afrilu, w07 4/1 shafi na 10, sakin layi na 3]
10. Mene ne dalilin rubuta takarda shari’a biyu game da yarjejeniya ɗaya? (Irm. 32:10-15) [30 ga Afrilu, w07 4/1 shafi na 10, sakin layi na 4]