Ayyuka na Makon 23 ga Afrilu
MAKON 23 GA AFRILU
Waƙa ta 45 da Addu’a
□ Nazarin Littafi Mai Tsarki na Ikilisiya:
cl shafi na 169-171 (minti 25)
□ Makarantar Hidima Ta Allah:
Karatun Littafi Mai Tsarki: Irmiya 29-31 (minti 10)
Na 1: Irmiya 31:15-26 (minti 4 ko ƙasa da hakan)
Na 2: Shin Allah Yana Bukatar Kiristoci Su Kiyaye Assabaci Kowane Mako? (minti 5)
Na 3: Ku Kasance a Faɗake Game da Alamun Cewa Muna Kwanaki na Ƙarshe—td 28B (minti 5)
□ Taron Hidima:
Waƙa ta 130
Minti 10: Sanarwa. Ka yi amfani da samfurin gabatarwa da ke shafi na 4 don ka nuna yadda za a iya soma nazari da mutane a Asabar ta farko a watan Mayu.
Minti 10: Yadda Za Ka Mai da Martani ga Wanda ba Ya Son Ya Tattauna Game da Addini. An ɗauko tattaunawar ce daga littafin nan Yadda Za a Soma Kuma Cigaba da Mahawwarai na Littafi Mai Tsarki, shafi na 9, sakin layi na 2, zuwa shafi na 11, sakin layi na 2. Ka sa a gwada ɗaya ko biyu daga cikin waɗannan bayanan.
Minti 15: “Ka Biɗi ‘Tsarki Cikin Tsoron Allah.’” Tattaunawa da aka ɗauko daga Hasumiyar Tsaro ta 15 ga Mayu, 2008, shafuffuka na 26-28.
Waƙa ta 70 da Addu’a