Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • km 12/11 p. 1
  • Mu Masu Wa’azin Bishara Ne Kullum

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Mu Masu Wa’azin Bishara Ne Kullum
  • Hidimarmu Ta Mulki—2011
  • Makamantan Littattafai
  • “Ka Yi Aikin Mai-bishara”
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2004
  • Me Ya Sa Hidimar Gida Gida Take Da Muhimmanci Yanzu?
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2008
  • Za Ka Iya Yin Wa’azi Sa’ad da Ka Samu Zarafi!
    Hidimarmu Ta Mulki—2010
  • Kana Cika Hidimarka ga Allah Kuwa?
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2019
Dubi Ƙari
Hidimarmu Ta Mulki—2011
km 12/11 p. 1

Mu Masu Wa’azin Bishara Ne Kullum

1. Ta yaya muka san cewa masu wa’azin bishara a ƙarni na farko sun yi wa’azi kullum?

1 Kiristoci na ƙarni na farko masu yin wa’azin bishara da ƙwazo sun yi shelar bishara ‘ba fasawa’ a duk inda suka ga mutane. (A. M. 5:42) Saboda haka, ba za mu yi tsammani cewa za su wuce mutane a kan hanya ba tare da yi musu wa’azi ba sa’ad da suke wa’azi gida gida. Kuma ba za su ƙyale zarafin yin wa’azi ya shige su yayin da suke sayayya a kasuwa bayan sun gama wa’azi ba. Kamar Yesu, suna wa’azi a ko da yaushe.—Mar. 6:31-34.

2. Mene ne yin rayuwa da ta jitu da sunanmu ya ƙunsa?

2 Kasancewa a Shirye Kullum: Sunanmu, Shaidun Jehobah ba ya nuna abin da muke yi kaɗai amma yana nuna ko wane ne mu. (Isha. 43:10-12) Saboda haka, a ko da yaushe muna a shirye mu kāre begenmu, ko a lokacin da ba ma yin wa’azi gida gida ba. (1 Bit. 3:15) Kana tunani a kan yanayin da zai iya taso da za ka samu zarafin yin wa’azi kuma ka yi tunanin abin da za ka faɗa idan hakan ya faru? Shin kana riƙe littattafai da za ka ba wa waɗanda suke son saƙonmu? (Mis. 21:5) Kana wa’azi gida gida kawai, ko kuwa kana yi wa mutane wa’azi a wasu wurare idan da dama?

3. Mene ne ma’anar yin wa’azi ga jama’a kuma me ya sa yake da muhimmanci?

3 Yin Wa’azi ga Jama’a: Yana nufin yin wa’azi a titi da tashar mota da wuraren shaƙatawa da wuraren sana’a da sauransu. Manzo Bulus ya ce ya yi wa’azi a “sarari” da kuma gida gida. (A. M. 20:20) Hanya ta musamman da muke yin wa’azi ga mutane ita ce yin wa’azi gida gida. Amma, masu wa’azi a ƙarni na farko sun mai da hankali ga mutane ba gidaje ba. Sun yi amfani da kowane zarafi don su yi magana game da gaskiya a fili da lokacin da suka samu zarafi da kuma gida gida. Bari mu yi hakan domin mu cika hidimarmu.—2 Tim. 4:5.

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba