Tsarin Ayyuka na Makon 12 ga Disamba
MAKON 12 GA DISAMBA
Waƙa ta 43 da Addu’a
□ Nazarin Littafi Mai Tsarki na Ikilisiya:
cl shafuffuka na 97 zuwa 99 (minti 25)
□ Makarantar Hidima ta Allah:
Karatun Littafi Mai Tsarki: Ishaya 6-10 (minti 10)
Na 1: Ishaya 6:1-13 (minti 4 ko ƙasa da hakan)
Na 2: Labarin Mawadaci da Li’azaru Ba Tabbacin Shan Madawwamin Azaba Ba Ne—td 29C (minti 5)
Na 3: Dalilin da Ya Sa Ƙauna ba ta Ƙarewa Daɗai—1 Kor. 13:8; 1 Yoh. 4:8 (minti 5)
□ Taron Hidima:
Waƙa ta 36
Minti 5: Sanarwa.
Minti 15: Makarantar Hidima ta Allah ta 2012. Jawabin da mai kula da makaranta zai ba da. Ka tattauna batutuwa da suke cikin tsarin ayyuka na 2012 da ya kamata a mai da musu hankali a ikilisiyar. Ka nanata aikin mai ba da shawara na biyu. Ka ƙarfafa kowa ya yi aikin da aka ba shi a makaranta, ya yi kalami a taƙaitawa na Littafi Mai Tsarki, kuma ya yi amfani da shawarwarin da ake ba da mako-mako a littafin nan Benefit From Theocratic Ministry School Education.
Minti 15: “Mu Masu Wa’azin Bishara Ne Kullum.” Tambayoyi ana ba da amsoshi. Sa’ad da kake tattauna sakin layi na 2, ka ɗan gana da mai shela da ya ƙware wajen yin wa’azi a duk inda aka sami zarafin yin hakan. Ka sa ya bayyana yadda yake shirin yin hakan, kuma ka sa ya ba da fitaccen labarin da ya samu.
Waƙa ta 135 da Addu’a