Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w09 12/15 pp. 24-28
  • Ka Gina Ƙaunar Da Ba Ta Ƙarewa Daɗai

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Ka Gina Ƙaunar Da Ba Ta Ƙarewa Daɗai
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2009
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • Gina Ƙauna ga Jehobah
  • Abin da Ya Sa Muke Ƙaunar Ubangijinmu Yesu Kristi
  • Biɗar Hanya Mafificiya Ta Ƙauna
  • Ƙauna Tana Daurewa da Abu Duka
  • Ƙauna ba ta Ƙarewa Daɗai
  • “Ku Yi Zaman Ƙauna”
    Ka Kusaci Jehobah
  • Ƙauna Ta Gina Ka
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2001
  • Kada Ku Bar Ƙaunar da Kuke wa Juna ta yi Sanyi
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2017
  • Ka Ƙaunaci Allah Da Yake Ƙaunarka
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2006
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2009
w09 12/15 pp. 24-28

Ka Gina Ƙaunar Da Ba Ta Ƙarewa Daɗai

‘Ƙauna tana daurewa da abu duka. Ƙauna ba ta ƙarewa daɗai.’—1 KOR. 13:7, 8.

1. (a) Yaya ake gabatar da ƙauna sau da yawa? (b) A kan su waye kuma a kan menene mutane da yawa suke nuna ƙaunarsu?

AN WALLAFA abubuwa da yawa game da ƙauna. An ɗaukaka wannan halin kuma an rera ta a waƙar soyayya. Ɗan Adam yana bukatar ƙauna sosai. Amma littattafai da silima sau da yawa suna nuna ƙagaggen labaran ƙauna, kuma akwai su da yawa a kasuwa. Duk haka, mutane ba sa nuna tabbataciyar ƙauna ga Allah da kuma maƙwabta. Muna ganin abubuwan da Littafi Mai Tsarki ya annabta game da waɗannan kwanaki na ƙarshe suna faruwa. Mutane sun “zama masu-son kansu, masu-son kuɗi . . . mafiya son annishuwa da Allah.”—2 Tim. 3:1-5.

2. Wane gargaɗi ne Littafi Mai Tsarki ya ba da game da ƙauna ta ƙarya?

2 ’Yan adam suna iya nuna ƙauna, duk da haka Kalmar Allah ta yi mana gargaɗi game da ƙauna ta ƙarya. Kuma Littafi Mai Tsarki ya kwatanta abin da yake faruwa sa’ad da irin wannan ƙauna ta yi jijiya a zuciyar mutum. (1 Tim. 6:9, 10) Ka tuna abin da manzo Bulus ya rubuta game da Demas? Ko da yake yana tarayya da Bulus, Demas ya juya ga ƙaunar abin da duniya take ba da wa. (2 Tim. 4:10) Manzo Yohanna ya gargaɗi Kiristoci game da wannan haɗarin. (Karanta 1 Yohanna 2:15, 16.) Ƙaunar duniya da abubuwan da ke cikinta da kuma hanyoyinta da ke saurin wucewa ba su jitu ba da ƙaunar Allah da kuma abin da ke nasa.

3. Wane kaluɓale ne muke fuskanta, kuma waɗanne tambayoyi ne hakan ya ta da?

3 Mu ba na duniya ba ne, ko da yake muna zaune a cikinta. Saboda haka, muna da ƙalubalen guje wa ra’ayin duniya da bai dace ba game da ƙauna. Wajibi ne mu guji faɗawa cikin tarkon ƙauna ta ƙarya. Saboda haka, ga wanene ya kamata mu nuna ƙauna wadda babu son kai? Waɗanne tanadodi ne za su taimaka mana mu nuna ƙaunar da ke jimre abu duka kuma wadda ba ta ƙarewa daɗai? Ta yaya wannan tafarkin yake da amfani a gare mu a yanzu kuma ya shafi rayuwarmu a nan gaba? Muna bukatar amsoshi da ke bisa ra’ayin Allah don mu sami ja-gora mai kyau.

Gina Ƙauna ga Jehobah

4. Yaya ƙauna ga Allah take ƙaruwa?

4 Ana iya kwatanta gina ƙauna ga Jehobah da ayyuka tuƙuru da manomi yake yi na share ƙasa da shuka iri da kuma kula da ita don ta girma. (Ibran. 6:7) Hakazalika, ya kamata ƙaunarmu ga Allah ta ƙaru. Menene ake bukata don hakan ya faru? Dole ne mu yi aiki a kan ƙasa mai kyau da ke zuciyarmu, inda aka shuka irin gaskiyar Mulki. Za mu iya yin hakan ta wajen yin nazarin Kalmar Allah don mu ƙara iliminmu game da shi. (Kol. 1:10) Halartan taro a kowane lokaci da kuma yin kalami a ikilisiya zai sa iliminmu ya ƙaru. Kowannenmu yana iya ƙoƙarinsa a kai a kai don ya samu sani mai zurfi kuwa?—Mis. 2:1-7.

5. (a) Ta yaya za mu iya koya game da halayen Jehobah na musamman? (b) Menene za ka iya cewa game da adalcin Allah, hikimarsa, da kuma ikonsa?

5 Ta hanyar Kalmarsa, Jehobah ya bayyana halinsa. Ta wurin nazarin Nassosi da kuma ci gaba da samun sanin Jehobah, za mu daɗa so halayensa, wato, adalcinsa, ikonsa, hikimarsa, da kuma mafi girma, ƙaunarsa wadda ba ta da na biyu. Jehobah yana nuna adalci a dukan hanyoyinsa har da kamiltacciyar dokarsa. (K. Sha 32:4; Zab. 19:7) Muna iya yin tunani game da dukan ayyukan halitta na Jehobah kuma mu daraja hikimarsa mafi girma. (Zab. 104:24) Sararin samaniya ya kuma ba da tabbaci cewa Jehobah ne Tushen iko mafi girma da ba ya ƙarewa.—Isha. 40:26.

6. Ta yaya Allah ya nuna ƙauna a gare mu, kuma yaya hakan ya shafe ka?

6 Menene za a iya cewa game da halin Allah mafi rinjaya, wato, ƙaunarsa? Yana da faɗi sosai kuma ya shafi dukanmu. Ya nuna wannan ƙaunar ta wajen yin tanadin fansa don ya ceci ’yan Adam. (Karanta Romawa 5:8.) An yi wannan tanadin ne ga ’yan Adam gabaki ɗaya, amma waɗanda suka yi na’am ga ƙaunar Allah ne kawai kuma suka ba da gaskiya ga Ɗansa ne za su amfana. (Yoh. 3:16, 36) Ya kamata mu ƙaunaci Allah domin ya ba da Yesu don ya fanshe mu daga zunubanmu.

7, 8. (a) Menene ake bukata a gare mu domin mu nuna ƙauna ga Allah? (b) Duk da menene mutanen Allah suke kiyaye dokokinsa?

7 Ta yaya za mu nuna ƙauna ga Allah domin dukan abubuwan da ya yi mana? Hurarriyar amsar ita ce: “Ƙaunar Allah ke nan, mu kiyaye dokokinsa: dokokinsa fa ba su da ban ciwo ba.” (1 Yoh. 5:3) Hakika, ƙaunar da muke yi wa Jehobah Allah tana motsa mu mu kiyaye dokokinsa. Wannan shi ne dalilin da ya sa muke ba da shaida game da sunansa da kuma Mulkin, wadda ke amfanar mutane. Yin hakan da dukan zuciyarmu tabbaci ne cewa muna kiyaye dokokin Allah da muradi mai kyau.—Mat. 12:34.

8 ’Yan’uwanmu a dukan duniya suna nacewa wajen kiyaye dokokin Allah duk da yake an ƙi jininsu kuma an ƙi saƙonsu na Mulki kai tsaye. Amma ba su ja da baya ba a ƙoƙarce-ƙoƙarcensu na cika hidimarsu sosai. (2 Tim. 4:5) Hakazalika, muna gaya wa mutane game da sani na Allah da kuma kiyaye dukan umurninsa.

Abin da Ya Sa Muke Ƙaunar Ubangijinmu Yesu Kristi

9. Menene Kristi ya jimre, kuma menene ya motsa shi?

9 Ƙari ga ƙaunar Allah, akwai dalilai da yawa da suka sa muke ƙaunar Ɗansa. Ko da yake ba mu taɓa ganin Yesu ba, yayin da muke ƙara koya game da shi, ƙaunar da muke yi masa tana ƙara zurfi. (1 Bit. 1:8) Waɗanne abubuwa ne Yesu ya jimre da su? Yayin da yake yin nufin Ubansa, an ƙi Yesu babu dalili, an tsananta masa, an yi masa zargin ƙarya, an zage shi. Kuma ya sha wasu wulakanci. (Karanta Yohanna 15:25.) Ƙaunar Yesu ga Ubansa na samaniya ta motsa shi ya jimre waɗannan gwaje-gwajen. Da yake ƙauna ce ta motsa shi, mutuwarsa ta hadaya ta yi tanadin fansa ga mutane da yawa.—Mat. 20:28.

10, 11. Bisa ga abin da Kristi ya yi dominmu, menene muradinmu?

10 Tafarkin Yesu ya motsa mu mu aikata. Yayin da muke tunani game da abin da Kristi ya yi mana, ƙaunar da muke yi masa tana ƙara zurfi. Da yake mu mabiyansa ne, ya kamata mu gina irin ƙaunar Kristi kuma mu ci gaba da nuna ta domin mu jimre wajen kiyaye umurninsa na ba da shaida game da Mulki da kuma almajirantarwa.—Mat. 28:19, 20.

11 Domin nuna irin ƙaunar da Kristi ya nuna wa dukan ’yan adam, hakan ya motsa mu mu kammala aikinmu kafin ƙarshe ya zo. (Karanta 2 Korantiyawa 5:14, 15.) Ƙaunar da Kristi ya nuna ita ce cibiyar cika nufin Allah don ’yan Adam. Kuma gurbin da Kristi ya kafa mana na bin sawunsa kud da kud ya sa kowannenmu ya sa hannu a wannan hurarren nufi. Hakan yana bukatan mu gina ƙauna ga Allah iyakar yadda zai yiwu. (Mat. 22:37) Ta wajen mai da hankali ga abin da Yesu ya koyar da kuma yin biyayya ga umurninsa, muna nuna cewa muna ƙaunarsa kuma mun ƙuduri aniya za mu ɗaukaka ikon mallakar Allah ko da menene ya faru, kamar yadda Yesu ya yi.—Yoh. 14:23, 24; 15:10.

Biɗar Hanya Mafificiya Ta Ƙauna

12. Menene Bulus yake nufi da furcin nan “hanya mafificiya”?

12 Manzo Bulus ya yi koyi da Kristi. Domin ya bi sawun Kristi kud da kud, Bulus ya sami bakin ƙarfafa ’yan’uwansa su zama masu koyi da shi. (1 Kor. 11:1) Ko da yake ya aririci Kiristocin da ke Koranti su ci gaba da kasancewa da himma wajen biɗar wasu kyauta na ruhu da ke bayyane a ƙarni na farko, kamar su warkarwa da kuma yin magana da harsuna dabam-dabam, Bulus ya nuna cewa da akwai wani abu da ya fi kyau da za su biɗa. A Korantiyawa 12:31, ya ba da bayani: “In nuna muku wata hanya mafificiya.” Abubuwan da ke cikin ayoyi na gaba sun nuna cewa hakan ita ce hanya mafificiya ta ƙauna. A wane azanci ne take mafificiya? Bulus ya kwatanta abin da yake nufi. (Karanta 1 Korantiyawa 13:1-3.) Idan yana da wasu iyawa na musamman kuma ya cim ma abubuwa da yawa amma ba shi da ƙauna, me zai zama? Babu kome! Ruhun Allah ya motsa shi ya bayyana wannan gaskiya mai muhimmanci. Babu shakka, bayyana mana wannan ya motsa mu sosai!

13. (a) Menene jigon shekara ta 2010? (b) A wane azanci ne ƙauna ba ta ƙarewa daɗai?

13 Bayan haka, Bulus ya bayyana mana abin da ƙauna take nufi da abin da ba ta nufi. (Karanta 1 Korantiyawa 13:4-8.) Yanzu, ka bincika sosai ka ga yadda kake bin abubuwan da ƙauna take bukata. Ka mai da hankali musamman ga furci na ƙarshe a aya ta 7 da kuma jimla ta farko a aya ta 8: ‘Ƙauna tana daurewa abu duka. Ƙauna ba ta ƙarewa daɗai,’ wanda zai zama ayar jigonmu a shekara ta 2010. Ka lura cewa a aya ta 8, Bulus ya faɗi cewa za a kawar da kyauta na ruhu, har da yin annabci da magana a harsuna dabam-dabam, waɗanda aka yi amfani da su a sabuwar ikilisiyar Kirista da aka kafa a lokacin. Za a daina yin su. Amma ƙauna za ta ci gaba da kasancewa. Jehobah ne ƙauna, kuma zai kasance ne har abada. Saboda haka, ƙauna ba ta ƙarewa daɗai. Za ta ci gaba da kasancewa har abada a matsayin halin Ubanmu madawwami.—1 Yoh. 4:8.

Ƙauna Tana Daurewa da Abu Duka

14, 15. (a) Ta yaya ƙauna za ta taimaka mana mu jimre wa gwaji? (b) Me ya sa wani ɗan’uwa matashi ya ƙi ƙarya amincinsa?

14 Menene ke taimaka wa Kiristoci su jimre kowane irin gwaji, yanayi mai wuya da kuma matsalolin da suke fuskanta? Ƙauna ce da ba ta son kai. Irin wannan ƙaunar ta fi ba da dukiyarmu. Ta haɗa da kasancewa a shirye mu riƙe amincinmu da kuma rasa ranmu domin Kristi. (Luk 9:24, 25) Ka yi tunanin tafarki na aminci na Shaidu da suka sha wahala a sansanin fursuna, sansanin aikin wahala, da kurkuku a lokacin Yaƙin Duniya na biyu da kuma bayan yaƙin.

15 Wani matashi ɗan Jamus mai suna Wilhelm ya bayyana wannan gaskiyar. Maimakon ya ƙarya amincinsa, ya kasance da aminci sa’ad da ya fuskanci mutuwa a hannun sojojin Nazi. A cikin wasiƙa na ban kwana ga iyalinsa, ya rubuta: “Dole ne mu yi ƙaunar Allah fiye da kome, yadda Shugabanmu Yesu Kristi ya ba da umurni. Idan muka kasance da aminci a gare shi, zai saka mana.” Daga baya, a cikin wani talifi na Hasumiyar Tsaro, wani daga cikin iyalinsa ya rubuta: “A duk lokacin wahala da iyalinmu ta fuskanta mun, tabbatar da cewa ƙaunarmu ga Allah ita ce farko a kowane lokaci.” Irin wannan halin ne ’yan’uwa da yawa suke jimrewa a kurkuku a ƙasar Armenia, Eritriya, Koriya ta Kudu, da wasu ƙasashe. Waɗannan ’yan’uwan suna kasancewa da aminci a ƙaunarsu ga Jehobah.

16. Menene ’yan’uwanmu da ke Malawi suka jimre?

16 A wurare da yawa, jarraba iri-iri sun gwada bangaskiya da jimirin ’yan’uwanmu. Shaidun Jehobah a Malawi sun jimre da hani na gwamnati, hamayya mai tsanani, da wulakanci masu yawa da sauransu, har tsawon shekaru 26. An albarkace su domin jimrewarsu. Sa’ad da aka soma tsananta musu, da akwai wajen Shaidu 18,000 a wannan ƙasar. Shekara talatin bayan hakan, adadinsu ya ƙaru fiye da sau biyu zuwa 38,393. An ga irin wannan sakamakon a wasu ƙasashe.

17. Menene wasu a cikin iyali da wasu ba masu bi ba ne suke fuskanta, me ya sa suka iya jimre da wulakanci?

17 Ko da yake yana yi wa mutanen Allah wuya su fuskanci farmaki na kai tsaye daga masu hamayya. Ya fi kasancewa da wuya sa’ad da Kiristoci suka fuskanci hamayya daga iyalinsu. Matsi na iya zuwa daga waɗanda suke cikin gida ɗaya ko kuma dangogi na kusa. Ba Yesu ya annabta cewa hakan zai faru ba? Hakika, kuma mutane da yawa sun ga gaskiya kalamansa. (Mat. 10:35, 36) Matasa sun jimre hamayya daga iyayensu da ba masu bi ba. An kori wasu daga gida, amma Shaidu masu kirki sun karɓe su. Iyayen wasu sun ƙi su. Menene ya taimaka wa irin waɗannan su jimre wannan wulakancin? Ba ƙaunar da suke yi wa ’yan’uwa kawai ba ce, amma fiye da kome, tabbatacciyar ƙaunarsu ga Jehobah da kuma Ɗansa.—1 Bit. 1:22; 1 Yoh. 4:21.

18. Ta yaya ƙauna da take jimre wa abu duka take taimaka wa Kiristoci ma’aurata?

18 Da akwai yanayi da yawa a rayuwa da ake bukatan a nuna ƙaunar da ke jimre wa abu duka. A cikin gami na aure, ƙauna tana taimaka wa ma’aurata su daraja kalaman Yesu: “Abin da Allah ya gama fa, kada mutum shi raba.” (Mat. 19:6) Sa’ad da suke fuskantar “wahala a cikin jiki,” ya kamata Kiristoci ma’aurata su tuna wa kansu cewa Jehobah ne mafi muhimmanci a cikin aurensu. (1 Kor. 7:28) Kalmarsa ta ce ‘ƙauna tana jimrewa da abu duka,’ kuma mata da miji da suka yafa wannan halin za su sami ƙarfafawar manne wa juna kuma su riƙe aurensu.—Kol. 3:14.

19. Menene ya faru tsakanin mutanen Allah bayan bala’o’i?

19 Ƙauna tana taimaka mana mu jimre da abu duka a lokacin bala’i. Hakan gaskiya ne sa’ad da girgizar ƙasa ta faru a kudancin ƙasar Peru da kuma Muguwar Guguwar Katrina da ta halaka wasu wurare a kudu maso gabas a ƙasar Amirka. ’Yan’uwanmu da yawa sun yi hasarar gidajensu ko kuma dukiyarsu a waɗannan bala’o’in. Ƙauna ta motsa ikilisiyoyi da ke dukan duniya su yi tanadin kayan agaji, kuma waɗanda suka ba da kansu sun taimaka wajen sake gina gidaje da kuma gyara Majami’un Mulki. Irin waɗannan ayyuka sun nuna cewa ’yan’uwanmu suna ƙauna da kuma kula da juna a dukan lokaci da kuma a kowane yanayi.—Yoh. 13:34, 35; 1 Bit. 2:17.

Ƙauna ba ta Ƙarewa Daɗai

20, 21. (a) Me ya sa ƙauna take da tamani sosai? (b) Me ya sa ka ƙuduri aniya ka biɗi hanya mafificiya ta ƙauna?

20 Mun ga hikimar biɗar hanya mafificiya ta ƙauna tsakanin mutanen Jehobah a yau. Hakika, tana da kyau a dukan yanayi. Ka yi la’akari da yadda manzo Bulus ya nanata wannan gaskiyar. Da farko, ya faɗi cewa za a kawar da kyauta na ruhu da kuma cewa ikilisiyar Kirista za ta manyanta. Sai ya kammala cewa: “Yanzu dai bangaskiya, da bege, da ƙauna sun tabbata, su uku; amma mafi girmansu ƙauna ce!”—1 Kor. 13:13.

21 Daga baya, abubuwa da muke begensu za su zama gaskiya, kuma saboda haka, bukatar kasancewa da bege a gare su zai ƙare. Ba za mu ƙara kasancewa da bege ga alkawura da muke jira su cika bayan an sabonta dukan abubuwa ba. Ƙauna kuma fa? Ba za ta taɓa ƙarewa ba daɗai. Za ta kasance. Da yake muna begen rai madawwami, babu shakka za mu gani kuma mu fahimci ƙarin fannoni na ƙaunar Allah. Ta wajen yin nufin Allah a biɗar hanya mafificiya ta ƙauna da ba ta ƙarewa daɗai, za ka iya kasancewa har abada.—1 Yoh. 2:17.

Ta Yaya Za Ka Amsa?

• Me ya sa za mu mai da hankali da ƙauna ta ƙarya?

• Ƙauna za ta iya taimaka mana mu jimre menene?

• A wane azanci ne ƙauna ba ta ƙarewa daɗai?

[Bayanin da ke shafi na 27]

Jigon shekara ta 2010 zai zama: ‘Ƙauna tana daurewa da abu duka. Ƙauna ba ta ƙarewa daɗai.’—1 Kor. 13:7, 8

[Hotunan da ke shafi na 25]

Ƙaunar Allah tana motsa mu mu ba da shaida

[Hotunan da ke shafi na 26]

Ƙauna da ba ta ƙarewa ta taimaka wa ’yan’uwanmu maza da mata a Malawi su jimre gwaje-gwaje

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba