Shin Kana Koyon Dukan Abin da Za Ka Iya Koya Daga Wurin Jehobah?
1. Yaya Jehobah ya ɗauki ilimi?
1 Jehobah ‘Mafi Girma Mai Koya Mana,’ yana son mu samu ilimi. (Isha. 30:20) Halitta ta fari da ya koyar shi ne Ɗansa na fari. (Yoh. 8:28) Jehobah bai daina koyarwa ba bayan da Adamu ya yi tawaye, amma ya koyar da ’yan Adam ajizai cikin ƙauna.—Isha. 48:17, 18; 2 Tim. 3:14, 15.
2. Wane aikin koyarwa ne ake yi yanzu?
2 A yau, Jehobah yana ja-gora a aikin ilimantarwa mafi girma da ake yi. Kamar yadda Ishaya ya annabta, miliyoyin mutane daga dukan duniya suna hawan “dutse na gidan Ubangiji.” (Isha. 2:2) Me ya sa suke hawan dutsen? Don Jehobah ya koya musu hanyoyinsa! (Isha. 2:3) A shekarar hidima ta 2010, Shaidun Jehobah sun yi amfani da sa’o’i fiye da biliyan ɗaya da rabi don yin wa’azi da kuma koya wa mutane gaskiya ta Littafi Mai Tsarki. Ƙari ga hakan, ana yin koyarwa ta ruhaniya ga fiye da ikilisiyoyi 105,000 a dukan duniya, kuma bawa mai aminci mai hikima yana buga littattafan Kirista masu ilimantarwa a harsuna fiye da 500.
3. Ta yaya ka amfana daga koyarwar da Jehobah yake mana?
3 Ka Amfana Sosai: Mun amfana sosai daga koyarwa na Allah! Mun koyi cewa Allah yana da suna kuma yana kula da mu. (Zab. 83:18; 1 Bit. 5:6, 7) Mun san amsa ga wasu tambayoyi masu muhimmanci a rayuwa, kamar su, Me ya sa mutane suke wahala da kuma mutuwa? Ta yaya zan iya yin farin ciki na gaske? Mene ne ma’anar rai? Jehobah ya kuma ba mu shawarwari na ɗabi’a da suka taimaka mana mu sa ‘hanyarmu ta yi albarka.’—Josh. 1:8.
4. Mene ne wasu ilimantarwa da bayin Jehobah za su iya morewa, kuma me ya sa ya kamata mu koya dukan abin da za mu iya koya daga wurin Jehobah?
4 Ƙari ga hakan, Jehobah ya tanadar da koyarwa na musamman da ke taimaka wa bayinsa masu yawa su faɗaɗa hidimarsu. Shafuffuka na 4 zuwa 6 sun lissafa zarafin da wasu suke da shi. Ko da yanayinmu bai ƙyale mu mu samu waɗannan koyarwar ba, zai dace mu yi amfani da koyarwar da Jehobah yake mana. Shin muna ƙarfafa matasa da malamansu suke yawan sa su biɗi makarantar jami’a, su kafa wa kansa maƙasudi na ruhaniya, wato, koyarwa ta Allah, wanda shi ne ilimi mafi muhimmanci? Koyon dukan abin da ya kamata daga wurin Jehobah zai taimaka mana mu more rayuwa mai kawo farin ciki yanzu da kuma rai na har abada a nan gaba.—Zab. 119:105; Yoh. 17:3.
Wasu Zarafin Ilimantarwa da Ƙungiyar Jehobah Take Tanadarwa
Azuzuwan Koyon Karatu
• Manufa: Don a koya wa mutane yadda ake karatu da kuma rubutu domin su iya karanta Littafi Mai Tsarki da kansu kuma su koya wa wasu gaskiya.
• Tsawon Lokaci: Dangane da bukatar.
• Wuri: Ikilisiyar yankin.
• Wanda Zai Iya Halarta: Dukan masu shela da kuma waɗanda suke son saƙonmu.
• Yadda Za a Shiga: Dattawan ikilisiya ne suke shirya azuzuwan dangane da bukatar yankin kuma suna ƙarfafa dukan waɗanda za su amfana su halarta.
Makarantar Hidima ta Allah
• Manufa: Don koyar da masu shela “su zama masu iya koyar da mutane . . . domin su taimaka wa juna . . . kuma don hakan ya taimaka musu su furta begen da suke da shi.”—Benefit From Theocratic Ministry School Education, shafi na 5.
• Tsawon Lokaci: Ba a sauke karatu.
• Wuri: Ikilisiyar yankin.
• Wanda Zai Iya Halarta: Dukan masu shela. Da kuma waɗanda suke halartar tarurruka a kai a kai, da suka amince da koyarwar Littafi Mai Tsarki kuma rayuwarsu ta jitu da ƙa’idodin Kirista.
• Yadda Za a Shiga: Ka tattauna da dattijon da ke kula da Makarantar Hidima ta Allah.
Azuzuwa na Harsunan Ƙasashen Waje
• Manufa: Don koyar da masu shela yadda za su yi wa’azi a wani harshen.
• Tsawon Lokaci: Wata huɗu ko biyar. Ana yawan yin azuzuwan ranar Asabar da safe sa’o’i ɗaya ko biyu.
• Wuri: Galibi, Majami’ar Mulki da ke kusa.
• Wanda Zai Iya Halarta: Masu shela da suke nuna misali mai kyau a cikin ikilisiya kuma suna da niyyar yin wa’azi a harshen ƙasar waje.
• Yadda Za a Shiga: Ofishin reshe ne ke shirya azuzuwan dangane da bukatar ƙasar.
Gine-gine na Majami’ar Mulki
• Manufa: Don gina da kuma gyara Majami’un Mulki. Wannan ba makaranta ba ce, amma ana koya wa waɗanda suke wannan aikin yadda ake ayyuka dabam-dabam na gini don su taimaka wajen gine-gine.
• Tsawon Lokaci: Dangane da yanayin wanda ya ba da kansa.
• Wuri: Duk inda aka tura Rukunin da ke Gina Majami’un Mulki. Ana iya gayyatar wasu daga cikinsu su taimaka a aikin agaji a wuri mai nisa da bala’i ta faru.
• Ƙwarewa: Wajibi ne ɗan’uwa ko ’yar’uwa ta yi baftisma kuma ta kasance da misali mai kyau a cikin ikilisiya. Ko sun san aikin gini ko a’a.
• Yadda Za a Shiga: Ka cika takardar nan Application for Kingdom Hall Construction Volunteer Program (A-25) da dattawa za su ba ka.
Makarantar Hidima ta Majagaba
• Manufa: Don taimaka wa majagaba su ‘cika hidimarsu sosai.’—2 Tim. 4:5.
• Tsawon Lokaci: Mako biyu.
• Wuri: Inda ofishin reshe suka zaɓa, sau da yawa a Majami’ar Mulkin da ke kusa da inda majagaban suke.
• Ƙwarewa: Waɗanda suka yi hidimar majagaba na kullum aƙalla na tsawon shekara guda.
• Yadda Za a Shiga: Za a zaɓa majagaban da suka cancanta ba tare da saka takarda ba kuma mai kula da da’ira zai sanar da su.
Makarantar Sababbin Masu Hidima a Bethel
• Manufa: Ana yin wannan makarantar a ofishin reshe, don ta taimaki sababbi su yi nasara a hidimarsu a Bethel.
• Tsawon Lokaci: Sa’a ɗaya duk mako na tsawon mako goma sha shida.
• Wuri: A Bethel.
• Ƙwarewa: Dole ne mutum ya kasance yana ɗaya daga wanda yake cikin iyalin Bethel ko kuma waɗanda suka ba da kansu na dogon lokaci (shekara ɗaya ko fiye da hakan).
• Yadda Za a Shiga: Za a sa sunan waɗanda suke Bethel da suka cancanta a makarantar nan da nan.
Makarantar Hidima ta Mulki
• Manufa: Don koyar da dattawa da bayi masu hidima su kula da aikinsu na masu kula da kuma hakkinsu a ƙungiyar. (A. M. 20:28) Hukumar Mulki ce za ta tsai da lokacin da za a yi wannan makarantar bayan wasu shekaru.
• Tsawon Lokaci: Cikin ’yan shekarun nan, na dattawa kwana ɗaya da rabi ne kuma na bayi masu hidima kwana ɗaya ne.
• Wuri: Galibi, a Majami’ar Mulki ko Majami’ar Taro da ke kusa.
• Ƙwarewa: Wajibi ne mutum ya zama dattijo ko bawa mai hidima.
• Yadda Za a Shiga: Mai kula da da’ira zai sanar da dattawa da kuma bayi masu hidima da suka cancanta.
Makaranta Don Dattawan Ikilisiyaa
• Manufa: Don taimaka wa dattawa su kula da hakkokinsu a cikin ikilisiya.
• Tsawon Lokaci: Kwana biyar.
• Wuri: Ofishin reshe ne ke zaɓa, galibi a Majami’ar Mulki ko Majami’ar Taro.
• Ƙwarewa: Wajibi ne mutum ya zama dattijo.
• Yadda Za a Shiga: Ofishin reshe za su gayyaci dattawan da suka cancanta.
Makaranta Don Masu Kula Masu Ziyara da Matansub
• Manufa: Don a taimaki masu kula masu ziyara da masu kula da gunduma su ƙware sosai a hidimarsu ga ikilisiya kuma su sa ƙwazo a “aiki cikin kalma da koyarwa” kuma su yi kiwon waɗanda suke ƙarƙashin kulawarsu.—1 Tim. 5:17; 1 Bit. 5:2, 3.
• Tsawon Lokaci: Wata biyu.
• Wuri: Inda ofishin reshe ya zaɓa.
• Ƙwarewa: Wajibi ne ya zama mai kula da da’ira ko mai kula da gunduma.
• Yadda Za a Shiga: Ofishin reshe ne yake gayyatar masu kula masu ziyara da matansu da suka cancanta.
Makarantar Littafi Mai Tsarki don ’Yan’uwa Maza Marasa Aurec
• Manufa: Don a koyar da dattawa da bayi masu hidima da ba su yi aure ba don su kula da ƙarin hakki a cikin ikilisiya. Za a aika yawancin waɗanda suka sauke karatu su yi hidima a inda akwai bukata a ƙasarsu. Za a iya aika kalila cikinsu su yi hidima a wata ƙasa idan suka ba da kansu.
• Tsawon Lokaci: Wata biyu.
• Wuri: Ofishin reshe ne ke zaɓan inda za a yi makarantar; ana yi a Majami’ar Taro da Majami’ar Mulki ko kuma a ofishin reshe.
• Ƙwarewa: ’Yan’uwa maza marasa aure da ke tsakanin shekara 23 da 62 da suke da koshin lafiya kuma suna son su yi hidima ga ’yan’uwansu kuma su faɗaɗa abubuwan Mulkin a duk inda aka tura su. (Mar. 10:29, 30) Wajibi ne su yi hidima a matsayin dattijo ko bawa mai hidima aƙalla na tsawon shekara biyu ba tare da fashi ba.
• Yadda Za a Shiga: Idan ana wannan makarantar a ƙasarku, ana yin taron don waɗanda suke son su halarta a taron da’ira. Za a ba da ƙarin bayani game da wannan makarantar a wannan taron.
Makarantar Littafi Mai Tsarki don Kiristoci Ma’auratad
• Manufa: Don a yi wa ma’aurata koyarwa na musamman don Jehobah da ƙungiyarsa su yi amfani da su sosai. Za a tura yawancinsu da suka sauke karatu zuwa wuraren da ake da bukata a ƙasarsu. Ana iya tura kalilan zuwa hidima a wata ƙasa idan sun ba da kansu.
• Tsawon Lokaci: Wata biyu.
• Wuri: An yi kalilan azuzuwa na farko a Cibiyar Koyarwa ta Watchtower da ke Patterson, a birnin New York, Amirka. Bayan hakan, za a yi wannan makarantar a wuraren da ofishin reshe suka zaɓa a yi, galibi a Majami’ar Taro ko kuma Majami’ar Mulki.
• Ƙwarewa: Ma’aurata masu shekara 25 da 50 kuma suna da cikakkiyar lafiya da yanayinsu zai sa su iya yin hidima a duk inda ake da bukata kuma suna da halin “Ga ni; ka aike ni.” (Isha. 6:8) Bugu da ƙari, za su kasance ma’aurata na aƙalla shekara biyu kuma suna hidima na cikakken lokaci na aƙalla shekara biyu ba tare da fashi ba.
• Yadda Za a Shiga: Idan ana wannan makarantar a ƙasarku, ana yin taron waɗanda suke son su shiga a ranar taro na musamman. Ana ba da ƙarin bayani a wannan taron.
Makarantar Littafi Mai Tsarki ta Gileyad
• Manufa: Don a koyar da majagaba da masu hidima ta cikakken lokaci don yin hidima a wata ƙasa.
• Tsawon Lokaci: Wata biyar.
• Wuri: A Cibiyar Koyarwa ta Watchtower da ke Patterson, a birnin New York, Amirka.
• Ƙwarewa: Ma’aurata da suka yi baftisma shekara uku kuma masu shekara tsakanin 21 da 38 a lokacin da suka fara sa takardar shiga. Dole ne su zama ma’aurata aƙalla shekara biyu kuma suna hidima ta cikakken lokaci na aƙalla shekara biyu ba tare da fashi ba. Dole ne masu neman shiga su kasance da cikakkiyar lafiya. Majagaba da suke hidima a wata ƙasa suna iya sa takardar neman shiga (har da waɗanda suke da matsayin hidima a wata ƙasa) da masu kula masu ziyara da waɗanda suke Bethel da waɗanda suka sauke karatun Makarantar Koyar da Masu Hidima a dā da Makarantar Littafi Mai Tsarki don ’Yan’uwa Maza Marasa Aure da Makarantar Littafi Mai Tsarki don Kiristoci Ma’aurata idan sun cika bukatu da ake nema.
• Yadda Za a Shiga: A ofisoshin reshe da aka zaɓa, ana yin taro don waɗanda suke son halartar wannan makaranta a lokacin taron gunduma. Ana ba da ƙarin bayani a wannan taron. Idan ba a yin wannan taron a lokacin taron gunduma a ƙasarku kuma za ka so ka sa takarda, kana iya rubuta wa ofishin reshe da ke ƙasarku don ƙarin bayani.
Makaranta don Waɗanda suke Kwamitin Reshe da Matansu
• Manufa: Don a taimaka wa waɗanda suke Kwamitin Reshe su kula da aikinsu na kula da gidajen Bethel da kyau da kuma mai da hankali ga batutuwa na hidima da suka shafi ikilisiyoyi da kula da da’irori da gundumomi da ke yankunansu da yin fassara da buga littattafai da aika su zuwa ikilisiyoyi da kuma kula da sashe dabam-dabam.—Luk 12:48.
• Tsawon Lokaci: Wata biyu.
• Wuri: Cibiyar Koyarwa ta Watchtower da ke Patterson, a birnin New York, Amirka.
• Ƙwarewa: Dole ne mutum ya kasance cikin Kwamitin Reshe ko waɗanda suke Kwamiti na Ƙasar ko kuma an naɗa su su yi wannan hidimar.
• Yadda Za a Shiga: Hukumar Mulki ce take gayyatar ’yan’uwa maza da suka cancanta da matansu.
[Hasiya]
a A yanzu ba a yin wannan makarantar a dukan ƙasashe.
b A yanzu ba a yin wannan makarantar a dukan ƙasashe.
c A yanzu ba a yin wannan makarantar a dukan ƙasashe.
d A yanzu ba a yin wannan makarantar a dukan ƙasashe.