Tsarin Ayyuka na Makon 11 ga Afrilu
MAKON 11 GA AFRILU
Waƙa ta 44 da Addu’a
□ Nazarin Littafi Mai Tsarki na Ikilisiya:
bh babi na 17 sakin layi na 16-20 da akwati (minti 25)
□ Makarantar Hidima ta Allah:
Karatun Littafi Mai Tsarki: Ayuba 21-27 (minti 10)
Na 1: Ayuba 25:1–26:14 (minti 4 ko ƙasa da hakan)
Na 2: Dalilin da Ya Sa Bai Kamata a Ɗauki Giciye a Matsayin Abin Ibada Ba (minti 5)
Na 3: Dalilin da Ya Sa Armageddon Alamar Ƙauna Ce Daga Allah—td 5B (minti 5)
□ Taron Hidima:
Waƙa ta 98
Minti 5: Sanarwa. Ka sanar wa ikilisiyar ci gaba da aka samu a yankin a kamfen da aka yi na gayyatar mutane zuwa Tuna Mutuwar Yesu.
Minti 10: Ka Shuka Irinka, Kuma Kada Ka Ja Hannunka. (M. Wa. 11:6) Tattaunawa da aka ɗauko daga Hasumiyar Tsaro ta 1 ga Maris, 2005, shafi na 31. Bayan an tattauna labarin, ka gayyaci masu sauraro su faɗi darussan da suka koya.
Minti 10: Yadda Za a Yi Wa’azi ta Hanyar Wasiƙa. Tattaunawa da aka ɗauko daga littafin nan Benefit From Theocratic Ministry School Education, shafuffuka na 71 zuwa 73.
Minti 10: “Za a Ba da Shaida Sosai.” Tambayoyi ana ba da amsoshi.
Waƙa ta 8 da Addu’a