Ayyuka na Makon 2 ga Mayu
MAKON 2 GA MAYU
Waƙa ta 99 da Addu’a
□ Nazarin Littafi Mai Tsarki na Ikilisiya:
bh babi na 18 sakin layi na 14-19 (minti 25)
□ Makarantar Hidima ta Allah:
Karatun Littafi Mai Tsarki: Ayuba 38-42 (minti 10)
Na 1: Ayuba 40:1-24 (minti 4 ko ƙasa da hakan)
Na 2: Amfani da Ake Samu Daga Kasancewa da Tawali’u da Kuma Haƙuri (minti 5)
Na 3: Baftisma Baya Wanke Zunubai—td 9B (minti 5)
□ Taron Hidima:
Waƙa ta 82
Minti 10: Sanarwa. Ka yi amfani da shawarar da ke shafin nan don gwada yadda za a iya soma nazari a Asabar ta farko a watan Mayu. Ka ƙarfafa kowa ya saka hannu.
Minti 15: Bukatun ikilisiya. Jawabi da aka ɗauko daga awutlayi na Taron Gunduma na shekara ta 2011.
Minti 10: Ku Yi Shirin Ba da Mujallu a Watan Mayu. Tattaunawa. Ka yi amfani da minti ɗaya ko biyu don yin bitar abin da ke cikin mujallun. Sai ka zaɓi talifofi biyu ko uku, kuma ka gayyaci masu sauraro su faɗi tambayoyi da nassosi da za su iya yin amfani da su a gabatarwar. Ka sa a gwada yadda za a ba da kowacce mujallar.
Waƙa ta 91 da Addu’a