Bitar Makarantar Hidima Ta Allah
Za a amsa waɗannan tambayoyi na gaba a Makarantar Hidima Ta Allah a makon 25 ga Afrilu, 2011. Mai kula da makaranta zai yi bita ta minti 20 daga abubuwan da aka tattauna a makonnin 7 ga Maris zuwa 25 ga Afrilu, 2011.
1. Ta yaya ne “mutanen ƙasa iri iri suka zama Yahudawa”? (Esther 8:17) [w06 3/1 shafi na 31 sakin layi na 4]
2. Me ya sa aka ƙyale Shaiɗan ya bayyana a gaban Jehobah? (Ayu. 1:6; 2:1) [w06 4/1 shafi na 8 sakin layi na 6]
3. Wane yanayi ne matar Ayuba take ciki sa’ad da ta gaya wa mijinta ya la’anci Allah ya mutu? (Ayu. 1:9) [w06 4/1 shafi na 8 sakin layi na 9]
4. Me ya sa sanin cewa Jehobah “yana da hikima a zuciya, mai-iko ne da ƙarfi” ya sa mu kasance da tabbaci? (Ayu. 9:4) [w07 6/1 shafi na 15 sakin layi na 16]
5. A wace hanya ce furcin da Eliphaz ya yi cewa mutum yana haɗiye “mugunta kamar ruwa” ya nuna tunani na Shaiɗan? (Ayu. 15:16) [w10 2/15 shafi na 20 sakin layi na 1-2]
6. Ta yaya ne fushi zai iya shafarmu? (Ayu. 19:2) [w06 9/1 shafi na 15 sakin layi na 8]
7. Mene ne ya taimaka wa Ayuba ya riƙe amincinsa? (Ayu. 27:5) [w09 4/15 shafi na 6 sakin layi na 17]
8. Wane irin hali ne Ayuba ya nuna ga Jehobah? (Ayu. 28:28) [w09 4/15 shafi na 6 sakin layi na 16]
9. Mene ne Elihu ya yi kafin ya ba da gargaɗi, kuma yaya za mu yi koyi da shi? (Ayu. 35:2) [w06 4/1 shafi na 10 sakin layi na 9]
10. Yaya ya kamata yin bimbini game da ayyukan Jehobah masu ban mamaki ya shafe mu? (Ayu. 37:14) [w06 4/1 shafi na 10 sakin layi na 10]