Tsarin Ayyuka na Makon 20 ga Disamba
MAKON 20 GA DISAMBA
Waƙa ta 79
□ Nazarin Littafi Mai Tsarki na Ikilisiya:
bh babi na 13 sakin layi na 1 zuwa 6
□ Makarantar Hidima ta Allah:
Karatun Littafi Mai Tsarki: 2 Labarbaru 20 zuwa 24
Na 1: 2 Labarbaru 20:1-12
Na 2: Menene Koyan Harshe Mai Tsarki da Yin sa Ya Ƙunsa? (Zeph. 3:9)
Na 3: Albarkar da Mulkin Allah Za Ta Kawo (td 33A)
□ Taron Hidima:
Waƙa ta 12
Minti 5: Sanarwa.
Minti 15: Ka Taɓa Amfani da Su Kuwa? Tattaunawa. Ta wajen ba da jawabi, ka ɗan taƙaita bayanai da suke cikin waɗannan talifofin Hidimarmu Ta Mulki: “Ka Taɓa Gwada Yin Nazari a Haɗuwa ta Farko?” da “Yadda Za Ka Koya wa Sababbi Yin Wa’azi” (km 5/10) da kuma “Za Ka Iya Yin Wa’azi Sa’ad da Ka Samu Zarafi!” (km 8/10). Ka gayyaci masu sauraro su yi kalami a kan yadda suka yi amfani da shawarwari da ke cikin waɗannan talifofin da kuma yadda suka amfana.
Minti 15: “Sabon Talifi don Soma Nazarorin Littafi Mai Tsarki.” Tambayoyi ana ba da amsoshi. Ka kammala ta wajen sa a yi gwaji ɗaya ko biyu da ya nuna yadda za a yi amfani da talifin nan “Learn From God’s Word—Why Learn From God?” [“Ka Koya Daga Kalmar Allah—Me Ya Sa Za Ka Koya Daga Wurin Allah?”] a Hasumiyar Tsaro ta 1 ga Janairu 2011 na Turanci don soma nazarin Littafi Mai Tsarki.
Waƙa ta 17