‘Abinci a Lotonsa’
1. Ta yaya tsarin ayyuka na ranar taro na musamman na kwanan nan ya taimaka maka da kuma wasu?
1 “Ainihin abin da muke bukata kenan!” Muna yawan furta wannan kalamin bayan mun halarci taro na musamman. Wani mai kula da da’ira ya ba da rahoto cewa bayan ’yan’uwa a da’irarsa sun saurari taron kwanan nan, wasu cikinsu sun furta muradinsu na saka hannu sosai a hidima. Wani mai kula mai ziyara ya ce: “Ya taimaka mana mu fahimci daidai lokacin da muke ciki yayin da muke yin tunani a kan zaɓinmu a rayuwa.” Wani kuma ya ce, “Masu shela da yawa ma sun faɗi cewa taron ya faɗakar da su su tabbatar cewa sun mai da hankali ga abin da ya fi muhimmanci, wato, hidima.” Ta yaya ranar taro na musamman ya taimaka maka?
2. Mene ne za a tattauna a tsarin ayyuka na shekara ta 2011?
2 Tsarin ayyuka na shekara ta 2011 zai kasance daidai abin da muke bukata. Jigon shi ne “Ka Nemi Mafaka a Jehobah,” wanda aka ɗauko daga Zabura 118:8, 9, NW. Ga wasu jigon da za a tattauna: “Yadda Jehobah Ya Zama Mafaka a Lokatan Wahala,” “Ku Taimaka wa Wasu Su Samu Mafaka a Ƙarƙashin Fukafukan Jehobah,” “Ku Yi Koyi da Jehobah Wajen Tanadin Mafaka,” “Matasa, Ku Sa Jehobah Ya Zama Madogararku!” da “Aljannarmu ta Ruhaniya, Tanadin da Jehobah Ya Yi Don Mu Samu Mafaka.”
3. Me ya kamata mu yi don mu amfana sosai daga taron?
3 Yadda Za Ku Amfana: Da zarar an sanar da kwanan watan, ku yi shiri don ku halarci taron, kuma ku gayyaci ɗaliban Littafi Mai Tsarkinku don su halarta tare da ku. Domin mu ‘ba da amfani cikin haƙuri,’ wajibi ne mu tuna abin da muka ji. (Luk 8:15) Saboda haka ka saurari tsarin ayyukan sosai, kuma ka rubuta fitattun bayanai da kuma abin da kake son ka yi amfani da shi a rayuwarka da kuma a hidima. Bayan taron, ku tattauna tsarin ayyukan tare a matsayin iyali, kuma ku yi la’akari da hanyoyin da kai da kuma iyalinka za ku iya amfani da bayanan.
4. Me ya sa ya kamata mu yi ɗokin halartar ranar taro na musamman wanda za a yi kwanan nan?
4 Kamar abinci mai ɗanɗano da mai gina jiki, an shirya ranar taro na musamman na shekara ta 2011 cikin ƙauna da natsuwa. Bari Jehobah ya albarkace ƙoƙarce-ƙoƙarcenku don halarta da kuma amfana daga wannan ‘abinci a lotonsa’ da zai amfane masu hidimar Kirista sosai.—Mat. 24:45.