Sanarwa
◼ Littafin da za a ba da a watan Satumba: Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa? Ku yi ƙoƙarin soma nazarin Littafi Mai Tsarki a haɗuwa na farko. Oktoba: Mujallun Hasumiyar Tsaro da Awake! A inda masu gida suke son saƙon, ka ba da warƙar nan Za Ka so ka San Amsoshin Waɗannan Tambayoyin?, kuma ka ƙudurta soma nazarin Littafi Mai Tsarki da wani. Nuwamba: Littafi Mai Tsarki—Wane Saƙo Ne Ke Cikinsa? Za a ba da cikakken bayani game da yadda za a yi kamfen da wannan mujallar a dukan duniya a nan gaba. Ku ba da sabuwar mujallar tare da waɗannan mujallun: Ruhohin Matattu—Zasu Taimake Ka ne ko Kuwa Zasu Yi Maka Barna? Sun Wanzu Kuwa Da Gaske?, Hanyar Rai Madawwami—Ka Same ta Kuwa?, Za Ka Iya Zama Abokin Allah! Disamba: Littafin nan The Greatest Man Who Ever Lived. Idan akwai yara a gidan, ku ba da littafin nan Ka Koya Daga Wurin Babban Malami.
◼ Za a ba da jawabi na musamman na Tuna Mutuwar Yesu na shekara ta 2011 a makon 25 ga Afrilu, 2011. Za a sanar da jigon jawabin a nan gaba. Ikilisiyoyi da suke da ziyarar mai kula da da’ira ko taro na musamman ko na da’ira a makon za su ba da jawabin a mako na gaba. Kada kowacce ikilisiya ta ba da jawabin kafin ranar 25 ga Afrilu.