Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • km 8/10 p. 7
  • Ka Taɓa Amfani da Bangon Baya Kuwa?

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Ka Taɓa Amfani da Bangon Baya Kuwa?
  • Hidimarmu Ta Mulki—2010
  • Makamantan Littattafai
  • Hanyoyin Kyautata Yadda Muke Wa’azi—Yadda Za Mu Ba da Littafin nan Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa?
    Hidimarmu Ta Mulki—2015
  • Sabon Talifi don Soma Nazarorin Littafi Mai Tsarki
    Hidimarmu Ta Mulki—2010
  • “Yadda Za A Ba da Mujallu a . . .”
    Hidimarmu Ta Mulki—2013
  • Sabon Talifi don Soma Tattaunawa da Mutane
    Littafin Taro Don Rayuwa ta Kirista da Hidimarmu (2016)
Dubi Ƙari
Hidimarmu Ta Mulki—2010
km 8/10 p. 7

Ka Taɓa Amfani da Bangon Baya Kuwa?

Idan aka ba mutane mujalla, sukan soma kallon bangon gaban kafin su juya bayan. Talifin da ke bayan mujallun Hasumiyar Tsaro na wa’azi yana ɗauke da tambayoyi masu ta da marmari da bayanai tare da lambobin shafuffukan da za a iya ganin bayanan a ciki.

Muna iya yin amfani da wannan fannin wajen samun tambayoyi masu kyau da za mu iya soma tattaunawa da ita. Idan muna wa’azi a yankin a kai a kai, za mu iya bambanta gabatarwarmu ta yin amfani da tambayoyi dabam dabam a watan gabaki ɗaya. Idan mai gida ya taƙure da aiki, za mu iya gajartar da gabatarwarmu ta nuna ɗaya daga cikin tambayoyin da ke bangon bayan sai mu ce, “Idan za ka so ka san amsar, zan iya bar maka waɗannan mujallun, kuma za mu iya ƙara tattaunawa sa’ad da ka samu lokaci.” Wasu masu shela za su so su soma tattaunawa ta nuna wa mai gida talifin da ke bayan mujallar sai su gaya masa ya zaɓi tambaya da yake son su tattauna tare. Bayan hakan, za su iya nuna masa inda amsar take sai su karanta masa nassin da sun riga sun shirya. Wataƙila za ka iya yin tunani a kan wasu hanyoyi da za ka iya yin amfani da talifin da ke bayan mujallun Hasumiyar Tsaro don ta da marmarin mutane.

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba