Tanadi don Kiristoci Masu Hidima
1. Wanne sabon shiri ne aka soma a shekara ta 1938, kuma don me?
1 Ƙungiyar Jehobah ta soma sabon shiri a shekara ta 1938. An gayyaci rukunin ikilisiyoyi da yawa don su halarci taron zango, wanda ake kiran taron da’ira yanzu. Don me? Informant ta Janairu 1939 (yanzu Hidimarmu Ta Mulki) ta ba da amsa: “Waɗannan tarurrukan sashen Tsarin Ƙungiyar Jehobah ne don cim ma hidimar Mulki. Koyarwar da aka yi tana da muhimmanci don ta taimaki kowa su yi aikinsu yadda ya kamata.” Idan mun yi la’akari da ƙarin masu shelar Mulki da aka samu na 58,000 a shekara ta 1938 zuwa fiye da 7,000,000 a shekara ta 2009, muna da tabbaci cewa tarurrukan da’ira suna cim ma manufarsu na taimaka wa masu hidima su “yi aikin da aka ba su”!
2. Wane bayani ne za a gabatar a taronmu na da’ira na shekara ta 2011?
2 Jigo na Shekara Mai Zuwa: Muna ɗokin halartar taron da’ira da zai soma daga watan Janairu 2011 da kuma ƙarfafa da za a samu daga taron. An ɗauko Jigon “Ku Ba na Duniya Ba Ne” daga littafin Yohanna 15:19. Waɗanne jawabai da za a ba da ne za su amfane masu hidimar Kirista? A ranar Asabar za mu saurari jawabin nan “Ta Yaya Hidima ta Cikakken Lokaci Take Kāre Mu?” Za mu kuma more magana daki-daki mai sashe uku “Kada Ku Gurɓata ta Wurin . . . ” “Bisan,” “Babbar Karuwa,” da kuma “Dillalan Duniya.” A ranar Lahadi za mu saurari wata magana daki-daki mai jigo “Ka Yi Ƙaunar Jehobah, Ba Duniya Ba.” Wasu jawaban sun haɗa da “Ku Ci Gaba a Matsayin ‘Saukakku, Baƙi Masu-Tafiya’” da kuma “Ku Yi Farin Ciki, Za Ku Iya Yin Nasara da Duniya.”
3. Waɗanne amfani ne za mu iya samu daga halartar taron da’ira?
3 Bayan wata ’yar’uwa da ta rage fitar hidimar fage a kai a kai ta halarci taron da’ira na kwanan nan, ta rubuta cewa tsarin ayyukan ya sa ta sake bincika yanayinta kuma ta kuɗiri aniyar “fita hidima kuma ta daina ba da hujjoji!” Babu shakka tsarin ayyuka na taron da’ira na shekara ta 2011 zai taimaki dukanmu mu yi ƙaunar Jehobah maimakon duniya. (1 Yoh. 2:15-17) Ka tabbata ka halarta kuma ka mai da hankali domin ka amfana daga wannan tanadi mai kyau da aka yi wa Kiristoci masu hidima!