Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • km 11/10 pp. 5-6
  • Za Ku Iya Tattaunawa da Abokin Aure da Ba Mai Bi Ba Ne?

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Za Ku Iya Tattaunawa da Abokin Aure da Ba Mai Bi Ba Ne?
  • Hidimarmu Ta Mulki—2010
  • Makamantan Littattafai
  • Za a Iya Yin Farin Ciki a Iyalin da ba Kowa Ba Ne Yake Bauta wa Jehobah
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2012
  • Gaskiya Ba ta Kawo ‘Salama, Amma Takobi’
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2017
  • Ku Auri “Mai Bin Ubangiji” Kadai, Umurnin Yana da Amfani Har Ila?
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2015
Hidimarmu Ta Mulki—2010
km 11/10 pp. 5-6

Za Ku Iya Tattaunawa da Abokin Aure da Ba Mai Bi Ba Ne?

1. Me ya sa ba Kiristoci da suke cikin iyalin da wasu ba masu bi ba ne kaɗai suke son su taimaka wa abokan aurensu da ba masu bi ba ne su karɓi gaskiya?

1 Shin akwai wasu masu shela a ikilisiyarku da aboki ko abokiyar aurensu ba masu bi ba ne? Idan haka ne, babu shakka waɗannan masu shela suna son abokin aurensu ya bauta wa Allah tare da su. Amma ba su kaɗai ba ne suke da irin wannan marmarin. Ikilisiyar gabaki ɗaya tana da irin muradin Allah cewa “dukan mutane su tsira, kuma su kawo ga sanin gaskiya.” (1 Tim. 2:4) Ta yaya za mu iya taimaka wa aboki ko abokiyar aure da ba masu bi ba ne na masu shela da suke cikin ikilisiyarmu?

2. Ta yaya kasancewa da basira zai taimaka mana mu taimaki aboki ko abokiyar aure da ba mai bi ba ne?

2 Da farko, ya kamata mu yi ƙoƙari mu yi la’akari da ra’ayin wanda ba mai bi ba ne. Abokan aure da yawa da ba masu bi ba ne suna ƙaunar iyalinsu kuma suna ƙoƙari su kasance aboki ko abokiyar aure ko kuma iyaye mai kyau. Wataƙila sun amince da wani addini dabam da namu. Mai yiwuwa ba su san Shaidun Jehobah sosai ba sai dai abin da abokansu da ba sa son mu suka faɗa musu. Wasu suna yin fushi saboda lokacin da aboki ko abokiyar aurensu yake amfani da shi don bauta maimakon ya kasance tare da iyalin a gida. Basira zai taimaka mana mu bi da aboki ko abokiyar aure da ba mai bi ba ne cikin ƙauna da daraja kuma mu guji cika jin tsoro sa’ad da muke tare da shi ko ita.—Mis. 16:20-23.

3. Wace hanya ce mafi kyau na taɓa zuciyar wanda ba mai bi ba ne?

3 Nuna Kulawa: Hanya na farko mafi kyau na taɓa zuciyar aboki ko abokiyar aure da ba mai bi ba ne, shi ne ƙila ta halayenmu, ba ta tattaunawar Littafi Mai Tsarki ba. (1 Bit. 3:1, 2) Abu mai muhimmanci a wannan batun shi ne nuna kulawa. ’Yan’uwa mata a cikin ikilisiya za su iya nuna wa abokiyar aure da ba mai bi ba ce kulawa, ’yan’uwa maza ma za su iya yi wa abokin aure da ba mai bi ba ne hakan. Ta yaya?

4. Ta yaya za mu iya nuna kulawa?

4 Idan ba ka tattauna da aboki ko abokiyar auren ba tukuna, za ka iya yin hakan bayan ka riga ka tattauna yanayin da abokin auren da mai bi ne. Idan wanda ba mai bi ba ne bai amince da saƙon ba, kada ka yi sanyin gwiwa. Kasancewa da fara’a da kuma nuna kulawa zai iya motsa shi ya samu ra’ayi mai kyau game da Shaidun Jehobah. (Rom. 12:20) Wasu Kiristoci da suka manyanta sun gayyaci wanda ba mi bi ba ne da kuma iyalinsa zuwa gidansu don su ci abinci tare, da muradin sanin juna sosai da kuma sanyaya kowacce ƙiyayya da suke da shi. Sun tattauna abin da mutumin yake so, maimakon tilasta masa ya saurari tattaunawar Littafi Mai Tsarki. Daga baya, sa’ad da wanda ba mai bi ba ne ya ƙara sake jiki, ana iya tattauna abubuwa na Nassi. Ko kuma yana iya amince ya halarci taronmu don ya ga abin da matarsa take koya, musamman tun da ya riga ya san wasu daga cikin ikilisiyar. Ko da ba shi da marmarin bincika gaskiya, za a iya yaba masa don goyon bayan da yake wa abokiyar aurensa.

5. Ta yaya dattawa za su iya tattaunawa da wanda ba mai bi ba ne?

5 Ya kamata dattawa musamman su yi ƙoƙari su ziyarci waɗanda ba masu bi ba ne kuma su nemi zarafin ba da shaida. Wanda ba mai bi ba ne da ba ya son tattaunawar Littafi Mai Tsarki zai iya saurara wa ƙarfafa na ruhaniya sa’ad da yake jinya ko kuma yake da ciwo mai tsanani. Idan iyali da miji ko mata ba mai bi ba ne suka samu matsala, kamar rashin wani daga iyalin, dattawan za su iya gayyatar wanda ba mai bi ba ne ya kasance tare da su sa’ad da suke ƙarfafa iyalin.

6. Waɗanne dalilai ne za su motsa mu mu tattauna da aboki ko abokiyar aure da ba mai bi ba ne?

6 Ka yi tunanin farin ciki da Kirista da ke cikin ikilisiya zai samu idan aboki ko abokiyar aurensa ya nuna yana son saƙon kuma ya karɓi gaskiya! Irin wannan yanayi na farin ciki zai sa Jehobah, mala’iku da sauran mutanen ikilisiyar farin ciki matuƙa. (Luk 15:7, 10) Amma dai, idan da farko wanda ba mai bi ba ne bai saurari saƙon ba, za mu iya farin ciki cewa ƙoƙarce-ƙoƙarcenmu yana faranta wa Jehobah rai, wanda “ba shi nufin kowa da halaka ba, amma duka su kai ga tuba.”—2 Bit. 3:9.

[Bayanin da ke shafi na 6]

Hanya na farko mafi kyau na taɓa zuciyar aboki ko abokiyar aure da ba mai bi ba ne, shi ne ƙila ta halayenmu, ba ta tattaunawar Littafi Mai Tsarki ba

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba