Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • km 6/10 p. 3
  • Bitar Makarantar Hidima Ta Allah

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Bitar Makarantar Hidima Ta Allah
  • Hidimarmu Ta Mulki—2010
Hidimarmu Ta Mulki—2010
km 6/10 p. 3

Bitar Makarantar Hidima Ta Allah

Za a amsa waɗannan tambayoyi na gaba a Makarantar Hidima Ta Allah a makon 28 ga Yuni, 2010. Mai kula da makarantar zai gabatar da bita ta minti 20 bisa ga abin da aka nazarta daga makon 3 ga Mayu zuwa 28 ga Yuni, 2010.

1. Menene za mu iya koya daga makokin da Dauda ya yi bisa Abner? (2 Sam. 3:31-34) [w05 6/1 shafi na 29 sakin layi na 5; w06 8/1 shafi na 9 sakin layi na 9-10]

2. Menene za mu iya koya daga 2 Sama’ila 5:12? [w05 6/1 shafi na 29 sakin layi na 6]

3. Manufa mai kyau yana canja bukatun Allah ne? (2 Sam. 6:1-7) [w05 6/1 shafi na 29 sakin layi na 7]

4. Ta yaya ne abubuwan da Dauda ya yi wa Mephibosheth ke nuna ƙauna ta alheri, kuma yaya hakan ya kamata ya shafe mu? (2 Sam. 9:7) [w02 6/1 shafi na 16 sakin layi na 5]

5. Waɗanne darussa ne za mu iya koya daga dangantakar da ke tsakanin Ittai Bagitti da Sarki Dauda? (2 Sam. 15:19-22) [w09 5/15 shafuffuka na 27-28]

6. Daga Nassosi, me ya sa za mu iya ce zargin ƙarya ne Ziba ya yi wa Mephibosheth? (2 Sam. 16:1-4) [w02 3/1 shafi na 5 hasiya na sakin layi na 11]

7. Sa’ad da Dauda ya gaya wa Barzillai ya kasance cikin fadawansa, me ya sa Barzillai ya ce a zaɓi Chimham? (2 Sam. 19:33-37) [w07 6/1 shafi na 24 sakin layi na 13]

8. Menene za mu iya koya daga 2 Sama’ila 24:17? [w06 6/1 shafi na 31 sakin layi na 8]

9. Me ya sa Adonaija ya so ya ƙwace gadon sarauta duk da cewa Dauda na raye? (1 Sar. 1:5) [w05 7/1 shafi na 19 sakin layi na 5]

10. Me ya sa Jehobah ya amsa addu’ar da Sulemanu ya yi na samun hikima da fahimi? (1 Sar. 3:9) [w05 7/1 shafi na 20 sakin layi na 6]

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba