Tsarin Ayyuka na Makon 7 ga Yuni
MAKON 7 GA YUNI
Waƙa ta 48
□ Nazarin Littafi Mai Tsarki na Ikilisiya:
bh rataye shafi na 201-204
□ Makarantar Hidima ta Allah:
Karatun Littafi Mai Tsarki: 2 Sama’ila 19 zuwa 21
Na 1: 2 Sama’ila 19:11-23
Na 2: An Halicci Duniya Don Ta Zama Aljanna (td 15A)
Na 3: Hanyoyin da Shaiɗan Yake Amfani da Su Ya Makantar da Mutane Daga Sanin Gaskiya (2 Kor. 4:4)
□ Taron Hidima:
Waƙa ta 60
Minti 5: Sanarwa.
Minti 10: Ku Yi Wa’azi a Hanyar da Za a Fahimce Ku. Tattaunawa da masu sauraro daga littafin nan Benefit From Theocratic Ministry School Education, shafuffuka na 226-229.
Minti 10: Tattaunawa da masu sauraro na “Wasiƙa Daga Hukumar Mulki” wacce ke ’yar cikin Hidimarmu Ta Mulki ta Afrilu ko Mayu 2010. Ka faɗi labari ɗaya ko biyu mai ƙarfafawa da aka samu a hidimar fage. Ka sa mai shela ya gwada labari mai ƙarfafawa da ya auku a yankinku ba da daɗewa ba. Ka gayyaci masu sauraro su yi kalamai a kan fitattun sashe na rahoton dukan duniya da ke ’yar cikin Hidimarmu Ta Mulki ta Fabrairu 2010. Ka kammala da ƙarfafa waɗanda suka iya karanta Turanci su karanta Yearbook ɗin shekara ta 2010 kuma su amfana daga labaran hidimar fage da ke ciki.
Minti 10: Hanyoyin Yin Wa’azin Bishara—Yin Aiki a Yankuna da Ake Harsuna da Yawa. Tattaunawa da masu sauraro daga littafin nan Organized To Do Jehovah’s Will, shafi na 107, sakin layi na 2-3. Ka ɗan gana da mai kula da hidima. Waɗanne ikilisiyoyi na wani yare ne suke aiki a yankin? Waɗanne shirye-shirye ne aka yi don ba da haɗin kai ga waɗannan ikilisiyoyin don a yi wa kowa wa’azi ba tare da mutane da yawa sun yi wa mutum ɗaya wa’azi ba?
Waƙa ta 75