Tsarin Ayyuka na Makon 10 ga Mayu
MAKON 10 GA MAYU
Waƙa ta 131
□ Nazarin Littafi Mai Tsarki na Ikilisiya:
bh shafi na 4 sakin layi na 1 zuwa 7
□ Makarantar Hidima ta Allah:
Karatun Littafi Mai Tsarki: 2 Sama’ila 4 zuwa 8
Na 1: 2 Sama’ila 6:1-13
Na 2: Zai Yiwu Mutane Su Yi Magana da ’Yan’uwansu Matattu Kuwa? (td 34C)
Na 3: Dalilin da Ya sa Haɗama Bautar Gumaka Ce (Afi. 5:5)
□ Taron Hidima:
Waƙa ta 25
Minti 5: Sanarwa.
Minti 10: Ku Ba da Taimako Mai Amfani ga Waɗanda Suke Yankinku. Tattaunawa da masu sauraro daga littafin nan Benefit From Theocratic Ministry School Education, shafi na 188, sakin layi na 4, zuwa ƙarshen shafi na 189. Ka ɗan gana da wani da ya samu ci gaba domin wani ya nuna ya damu da shi.
Minti 10: Majami’ar Mulki Mai Tsabta Tana Girmama Jehobah. Jawabi daga dattijo. Jehobah Allah ne mai tsarki, saboda haka ya kamata tsabta ta zahiri ta kasance abu mai muhimmanci ga mutanensa. (Fit. 30:17-21; 40:30-32) Ta wajen tsabtace wurin bautarmu da kuma yanayi mai kyau, za mu sa a ɗaukaka Jehobah. (1 Bit. 2:12) Ka gana da ɗan’uwan da ke kula da tsabtace da kuma gyare-gyare na ikilisiya. Ka faɗi labari na yankin ko wanda ke a rubuce da ya nuna yadda yanayi mai kyau na Majami’ar Mulki ya kai ga ba da shaida a unguwar. Ka ƙarfafa kowa ya saka hannu wajen sa Majami’ar Mulki ta kasance cikin yanayi mai kyau.
Minti 10: ‘Wannan Bishara Kuwa Za a Yi Wa’azinta!’ Tambaya ana ba da amsa.
Waƙa ta 118