‘Wannan Bishara Kuwa Za a Yi Wa’azinta’!
1. Yaya muka san cewa babu abin da zai iya hana aikin wa’azi?
1 Babu abin da zai iya hana Jehobah ya cika nufinsa. (Isha. 14:24) Ko da yake Alƙali Gidiyon da mazajensa ɗari uku sun fuskanci sojojin Midiyanawa guda dubu ɗari da talatin da biyar da ake ganin ba za su iya yin nasara a kan su ba, amma Jehobah ya gaya masa: ‘Za ka ceci Isra’ila daga hannun Midian: ba ni na aike ka ba?’ (Alƙa. 6:14) Wane aiki ne yake da goyon bayan Jehobah a yau? Yesu ya ce: “Wannan bishara kuwa ta mulki za a yi wa’azinta cikin iyakar duniya.” (Mat. 24:14) Babu wanda ya isa ya hana wannan aikin daga cikawa!
2. Me ya sa za mu sa rai cewa Jehobah zai taimaka mana ɗai-ɗai a hidima?
2 Jehobah Yana Taimaka Mana Ɗai-Ɗai: Duk da cewa muna da gaba gaɗin cewa Jehobah zai sa Shaidunsa su yi nasara a matsayin rukuni, ya dace mu sa rai kuwa cewa zai taimaka mana ɗai-ɗai? A lokacin wahala, manzo Bulus ya shaida taimakon Jehobah ta hanyar Ɗansa, Yesu. (2 Tim. 4:17) Mu kasance da gaba gaɗi cewa Jehobah zai albarkaci ƙoƙarce-ƙoƙarcenmu ɗai-ɗai don cim ma nufinsa.—1 Yoh. 5:14.
3. A waɗanne irin yanayi ne Jehobah yake taimaka mana?
3 Shin alhinin rayuwa na yau da kullum yana hana ka samun isashen lokaci na yin wa’azi kuwa? “Yana bada ƙarfi ga masu-kasala.” (Isha. 40:29-31) Kana fuskantar tsanani ko hamayya ne? “Ka zuba nawayarka bisa Ubangiji, shi kuma za ya taimake ka.” (Zab. 55:22) Kana kasa nuna gaba gaɗi a wasu lokatai kuwa? ‘Sai ka tafi, ni kuwa ina tare da bakinka.’ (Fit. 4:11, 12) Kana da ciwon da ya sa ba ka iya fita hidima sosai? Jehobah yana daraja ƙoƙarce-ƙoƙarcen da ka yi da zuciya ɗaya kuma zai iya yin amfani da su, ko yaya ƙanƙantarsa.—1 Kor. 3:6, 9.
4. Ta yaya kasancewa da gaba gaɗi ga Jehobah zai shafe mu?
4 Hannun Jehobah “a miƙe ya ke, wa za ya juyar da shi?” (Isha. 14:27) Da gaba gaɗi cewa Jehobah zai albarkaci hidimarmu, bari mu ci gaba da yin wa’azi da “gaba gaɗi cikin Ubangiji.”—A. M. 14:3.