Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • km 4/10 p. 4
  • Bitar Makarantar Hidima Ta Allah

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Bitar Makarantar Hidima Ta Allah
  • Hidimarmu Ta Mulki—2010
Hidimarmu Ta Mulki—2010
km 4/10 p. 4

Bitar Makarantar Hidima Ta Allah

Za a amsa tambayoyi na gaba a Makarantar Hidima Ta Allah a makon 26 ga Afrilu, 2010. Mai kula da makaranta ne zai gabatar da bitar ta minti 20 bisa ga abin da aka yi nazarinsa daga makon 1 ga Maris zuwa 26 ga Afrilu, 2010.

1. Menene Naomi take nufi sa’ad da ta ce “Ubangiji ya nuna mini rashin yarda, Mai-iko duka kuma ya ƙuntata ni”? (Ruth 1:21) [w05-HA 4/1 shafi na 4 sakin layi na 1]

2. Waɗanne halaye ne suka sa Ruth ta zama “macen kirki.” (Ruth 3:11) [w05-HA 4/1 shafi na 5 sakin layi na 6]

3. Wane misali mai kyau ne Elkana ya kafa na ƙarfafa mutane da kalamai? (1 Sam. 1:8) [w05-HA 4/1 shafi na 7 sakin layi na 2]

4. Me ya sa roƙon da Isra’ila ta yi na samun sarki bai dace ba? (1 Sam. 8:5) [w05-HA 10/1 shafi na 11, sakin layi na 17]

5. Ta yaya Sama’ila da ya ‘tsufa ya yi furfura’ ya nuna misali mai kyau wajen yin addu’a game da wasu, kuma menene hakan ya nuna? (1 Sam. 12:2, 23) [w07-HA 6/1 shafi na 29 sakin layi na 14-15]

6. Me ya sa Saul ya yi wa Keniyawa alheri na musamman? (1 Sam. 15:6) [w05-HA 4/1 shafi na 8 sakin layi na 15]

7. Me ya sa Saul ya tambayi Dauda cewa “Ɗan wanene kai, ya sarmayi?” (1 Sam. 17:58) [w05-HA 4/1 shafi na 9 sakin layi na 3]

8. Menene za mu iya koya daga yadda Dauda ya bi da matsala mai tsanani da ya taso a Gath? (1 Sam. 21:12, 13) [w05-HA 4/1 shafi na 9 sakin layi na 7]

9. Ta yaya ƙauna da tawali’un Jonathan ya bayyanu sa’ad da ya kasance da muhimmanci ya taimaka da kuma ƙarfafa abokinsa Dauda? (1 Sam. 23:17) [lv-HA shafi na 28 sakin layi na 10, hasiya.]

10. Wane darasi ne muka koya daga saduwar da Saul ya yi da mayyar En-dor? (1 Sam. 28:8-19) [w05-HA 4/1 shafi na 9 sakin layi na 10]

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba