Tsarin Ayyuka na Makon 3 ga Mayu
MAKON 3 GA MAYU
Waƙa ta 4
□ Nazarin Littafi Mai Tsarki na Ikilisiya:
bh babi na 3 sakin layi na 17-24 da akwati
□ Makarantar Hidima ta Allah:
Karatun Littafi Mai Tsarki: 2 Sama’ila 1 zuwa 3
Na 1: 2 Sama’ila 2:12-23
Na 2: Yesu Ya Yi Amfani da Sunan Allah Kuwa a Hidimarsa?
Na 3: Matattu Za Su Iya Yi Mana Lahani Kuwa? (td 34B)
□ Taron Hidima:
Waƙa ta 31
Minti 5: Sanarwa.
Minti 10: Idan Mai Gida Ya Ce, ‘Ba Ka Amince da Yesu Ba.’ Tattaunawa da masu sauraro. Me ya sa mutane a yankinmu suke faɗin hakan? Waɗanne tambayoyi ne za a iya yin amfani da su don sanin abin da ke zuciyarsu? Wane sashen koyarwar Yesu ne wataƙila za su so? Waɗanne bayanai a babi na 4 na littafin nan Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa? ne za a iya yin amfani da su don ba da amsa? Ka ƙarfafa masu shela su karanta wa mai gida abin da ke shafi na 2 na sabon fitowar Hasumiyar Tsaro, game da manufar mujallar.
Minti 10: Bukatun ikilisiya.
Minti 10: Ka More Albarkar Yin Wa’azi a Matsayin Rukuni. Tattaunawa da masu sauraro daga littafin nan Organized to Do Jehovah’s Will, shafi na 108, sakin layi na 1 zuwa 3. Ka gayyaci mai kula da hidima ya faɗi tsarin ayyuka na fita hidima da kuma inda za a yi taron hidimar fage. Ka gayyaci masu sauraro su yi kalami game da yadda suka amfana daga tallafa wa wannan shirin da kuma yin aiki tare da wasu masu shela da suke rukunin hidimar fagensu.
Waƙa ta 100