Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • km 5/12 pp. 2-3
  • Kana Shirye Saboda Bala’i Kuwa?

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Kana Shirye Saboda Bala’i Kuwa?
  • Hidimarmu Ta Mulki—2012
  • Makamantan Littattafai
  • ‘Ka Zo Ka Bi Ni’
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2009
  • Kana Cika Hidimarka ga Allah Kuwa?
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2019
  • “Na Yi Muku Kwatanci”
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2002
  • Me Ya Sa Za Ka Bi “Kristi”?
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2009
Dubi Ƙari
Hidimarmu Ta Mulki—2012
km 5/12 pp. 2-3

Kana Shirye Saboda Bala’i Kuwa?

1 A kowace shekara, girgizar ƙasa da ambaliyar teku da guguwa da ruwan sama mai ɗauke da iska mai ƙarfi da kuma ambaliyar ruwa suna shafan miliyoyin mutane a duniya har da ’yan’uwanmu. Za mu kasance masu hikima idan muna shirye tun da yake haɗari da kuma bala’i sukan faru ba zato kuma suna iya shafan kowannenmu.—Mis. 21:5.

2 Tun da Wuri: A wasu lokatai hukumomi suna iya gaya mana cewa bala’i zai auku. Yana da muhimmanci mu mai da hankali ga waɗannan gargaɗin. (Mis. 22:3) A irin wannan yanayin dattawa suna iya tuntuɓar dukan ’yan’uwan da ke ikilisiya don su taimaka musu su yi shirye-shiryen da ya kamata. Bayan bala’in ta auku, dattawa za su ƙoƙarta su tuntuɓi dukan ’yan’uwan da ke ikilisiyar don su ga ko suna lafiya kuma su ga irin taimakon da za su ba da. Ana iya ɓata lokaci wajen cim ma hakan, idan dattawa ba su da cikakken adireshin ’yan’uwa. Shi ya sa yake da muhimmanci ’yan’uwa su ba sakataren ikilisiyarsu da kuma dattijon da ke kula da rukuninsu na wa’azi adireshinsu da kuma lambar wayarsu.

3 Idan ikilisiyar tana yankin da bala’i ke yawan aukuwa, dattawa suna iya gaya wa masu shela su ba da suna da kuma lambar wayar wani danginsu ko abokinsu da ba ya zama a yankin, wanda za a iya tuntuɓa nan da nan idan wani abu ya faru. Hakan zai sa dattawa su san inda aka kai masu shela. Dattawa suna iya tsara matakin da ikilisiyar za ta ɗauka sa’ad da bala’i ya auku, kuma wannan tsarin zai ƙunshi kayayyakin taimakon gaggawa da ya kamata kowa a cikin ikilisiyar ya kasance da su, yadda za su ƙaura da kuma yadda za a taimaka wa waɗanda suke bukatar taimako sosai. Yana da muhimmanci a ba da haɗin kai wajen bin waɗannan shirye-shiryen da aka yi cikin ƙauna.—Ibran. 13:17.

4 Bayan Bala’i Ya Auku: Mene ne ya kamata ka yi sa’ad da bala’i ya auku a yankinku? Ka tabbatar da cewa ka biya bukatun iyalinka. Idan za ka iya, ka taimaka ma wasu da bala’in ya shafa. Ka yi ƙoƙarta ka kira dattijon da ke kula da rukuninku na wa’azi ko kuma wani dattijon nan da nan idan hakan zai yiwu. Ka yi hakan ko da ba ka bukatar taimako, kuma kana nan lafiya. Idan kana bukatar taimako, ka san cewa ’yan’uwanka suna iya ƙoƙarinsu su taimaka maka. (1 Kor. 13:4, 7) Ka tuna cewa Jehobah yana sane da yanayinka; kuma ka dogara da shi don ya taimake ka. (Zab. 37:39; 62:8) Ka mai da hankali ga zarafin taimaka wa mutane su ƙarfafa dangantakarsu da Jehobah kuma ka taimaka musu a zahiri. (2 Kor. 1:3, 4) Ka sake soma bin tsarinka na bauta wa Jehobah nan da nan, idan hakan zai yiwu.—Mat. 6:33.

5 Tun da yake labarin aukuwar bala’i yana ƙara jefa duniya cikin ruɗani, bari mu mai da hankali ga sabuwar duniya. Ba da daɗewa ba, bala’i zai zama labari. (R. Yoh. 21:4) Amma a yanzu, za mu iya ɗaukan matakai masu kyau don mu kasance a shirye saboda lokacin wahala yayin da muke ci gaba da yi wa mutane wa’azi da ƙwazo.

[Tambayoyi na Nazari]

1. Me ya sa hikima ce mu kasance a shirye saboda bala’i?

2. Me ya sa yake da muhimmanci mu ba dattawa adireshinmu da lambar wayarmu?

3. Ta yaya za mu iya ba wa dattawa haɗin kai idan muna zaune a inda bala’i ke yawan faruwa?

4. Mene ne ya kamata mu yi sa’ad da bala’i ya auku a yankinmu?

5. Ta yaya labarin aukuwar bala’i yake shafanmu a matsayin Kiristoci?

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba