Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w14 12/15 pp. 17-20
  • Ya Kamata Ka Canja Ra’ayinka Ne?

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Ya Kamata Ka Canja Ra’ayinka Ne?
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2014
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • Lokacin da Canja Ra’ayinka Ba Zai Dace Ba
  • Lokacin da Canja Ra’ayinka Ba Laifi Ba Ne
  • Lokacin da Canja Ra’ayinka Ya Zama Wajibi
  • Shin, Allah Yana Canja Zuciyarsa?
    Amsoshin Tambayoyi Daga Littafi Mai Tsarki
  • Su Waye Ne ’Yan’uwanmu?
    Ka Koya Daga Wurin Babban Malami
  • Fushi Ya Jawo Kisan Kai
    Darussa daga Littafi Mai Tsarki
  • ‘Wane ne Na Jehobah?’
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2018
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2014
w14 12/15 pp. 17-20

Ya Kamata Ka Canja Ra’ayinka Ne?

WASU matasa sun tsai da shawarar zuwa kallon wani fim. Sun ji cewa tsaransu da yawa a makaranta sun ji daɗin kallon fim ɗin. Yayin da suka kai gidan siliman, suka ga hotunan manyan makamai da mata da suka yi shigar banza. Mene ne za su yi? Shin za su shiga su kalli fim ɗin?

Wannan misalin ya nuna cewa za mu iya samun kanmu a wani yanayin da zai sa mu tsai da shawarar da za ta shafi dangantakarmu da Jehobah, da sakamako mai kyau ko marar kyau. A wani lokaci, za ka yi niyyar yin wani abu amma daga baya sai ka canja ra’ayinka. Hakan yana nuna cewa kana jinkiri ne, ko kuma matakin ne bai dace ba?

Lokacin da Canja Ra’ayinka Ba Zai Dace Ba

Mun ba da kanmu ga Jehobah kuma mun yi baftisma don muna ƙaunarsa. Muna son mu kasance da aminci ga Allah. Amma, magabcinmu Shaiɗan Iblis ya kuɗiri niyya ya sa mu daina kasancewa da aminci. (R. Yoh. 12:17) Mun tsai da shawarar bauta wa Jehobah da kuma bin umurninsa. Zai zama abin baƙin ciki idan muka canja ra’ayinmu bayan mun ba da kanmu ga Jehobah! Hakan zai sa mu yi hasarar rai ta har abada.

Fiye da ƙarnuka 26 da suka shige, Sarki Nebukadnezzar na Babila ya kafa siffa ta zinariya kuma ya ba da umurni cewa dukan mutane su rusuna su bauta wa siffar. Wanda ya ƙi yin hakan, za a jefa shi cikin tanderun wuta. Wasu bayin Allah matasa uku, wato Shadrach da Meshach da Abednego sun ƙi bin umurnin. Saboda haka, aka jefa su cikin tanderu na wuta. Jehobah ya cece su, amma sun riga sun shirya su sa ransu cikin hadari maimakon su canja ra’ayinsu game da bautar Allah.—Dan. 3:1-27.

Annabi Daniyel ya nace da yin addu’a ko da yake an ce za a jefa shi cikin ramin zakoki. Duk da haka, ya ci gaba da yin addu’a ga Jehobah sau uku a rana. Daniyel bai canja ra’ayinsa na bauta wa Allah na gaskiya ba. Saboda haka, an ceci wannan annabin “daga ikon zakuna.”—Dan. 6:1-27.

Bayin Allah na zamani suna rayuwa bisa ga shawarar da suka tsai da na ba bauta masa. A wani makaranta a Afirka, wasu ɗalibai da Shaidun Jehobah ne sun ƙi su sara wa tutar ƙasarsu. Aka ce za a kore su daga makaranta idan ba su sara wa tutar kamar sauran ɗaliban makarantar ba. Ba da daɗewa ba, ministan ilimi ya ziyarci garin kuma ya yi magana da wasu cikin waɗannan ɗaliban da Shaidu ne. Sai matasan suka bayyana matsayinsu cikin ladabi da kuma gaba gaɗi. Tun daga lokacin, ba a sake ta da batun ba kuma makarantar ta daina matsa wa Shaidun Jehobah matasa su yi abin da zai ɓata dangantakarsu da Jehobah.

Ka yi la’akari da Joseph da matarsa ta yi fama da ciwon daji, kuma ta rasu ba zato ba tsammani. Dangin Joseph sun san ra’ayinsa game da al’adun jana’iza kuma ba su matsa masa ba. Amma dangin matarsa ba Shaidun Jehobah ba ne, kuma suna so su bi wasu al’adun jana’iza, har da waɗanda Allah ya haramta. Joseph ya ce: “Da yake na ƙi amincewa, suka yi ƙoƙarin rinjayar ’ya’yana; amma sun yi tsayin daka. Har ila, danginmu sun so a kwana ana makoki bisa al’ada. Na gaya musu cewa ba za a kwana ana makoki a gida na. Sun san cewa hakan bai jitu koyarwar addinina ko kuma ta matata ba, saboda haka, bayan mun tattauna sosai, sai suka yi makokin a wani wuri.”

Joseph ya ce: “Na yi addu’a ga Jehobah don kada iyalina su ƙetare dokarsa a wannan mawuyacin lokacin. Jehobah ya ji addu’ata kuma ya taimaka mana mu kasance da aminci duk da matsin da muka fuskanta.” Joseph da ’ya’yansa sun ƙi su canja ra’ayinsu game da abin da suka yi imani da shi.

Lokacin da Canja Ra’ayinka Ba Laifi Ba Ne

Ba da daɗewa ba bayan Idin Faska ta shekara 32 a zamaninmu, wata mace Bakan’aniya ta zo wurin Yesu a yankin Zidoniya. Ta yi ta roƙon sa ya ceci ’yarta daga aljani. Da farko, Yesu bai amsa mata ba. Ya ce wa almajiransa: “Ba a aiko ni wurin kowa ba sai wurin ɓatattun tumaki na gidan Isra’ila.” Sa’ad da ta nace, sai Yesu ya ce: “Bai da kyau a ɗauki abincin ’ya’ya a jefa wa karnuka.” Da yake matar tana da bangaskiya sosai, sai ta amsa cewa: “Gaskiya, Ubangiji; gama ko karnuka sukan ci cikin ɓarɓashin da ke faɗiwa daga tebur na iyayengijinsu.” Saboda haka, Yesu ya ji roƙonta kuma ya warkar da ’yarta.—Mat. 15:21-28.

Ta yin hakan, Yesu ya bi gurbin Jehobah na canja ra’ayi idan yanayin ya bukaci hakan. Alal misali, Allah ya so ya halaka Isra’ilawa sa’ad da suka yi gunkin ɗan maraƙi, amma ya canja ra’ayinsa sa’ad da Musa ya roƙe shi.—Fit. 32:7-14.

Manzo Bulus ya bi gurbin Jehobah da kuma Yesu. Da farko, Bulus ya ɗauka cewa bai dace su je wa’azi a ƙasar waje tare da Yohanna Markus ba don ya gudu ya bar Bulus da Barnaba a tafiyarsu ta farko. Amma daga baya, Bulus ya fahimci cewa Markus ya canja halinsa kuma zai kasance da amfani a gare shi. Saboda haka, Bulus ya ce wa Timotawus: “Ka ɗauko Markus, ka kawo shi tare da kai: gama yana da amfani gare ni wajen hidima.”—2 Tim. 4:11.

Mu kuma fa? Idan muka yi la’akari da misalin Ubanmu na sama mai jin ƙai da haƙuri da ƙauna, za mu ga cewa a wani lokaci, zai dace mu canja ra’ayinmu. Alal misali, za mu iya canja ra’ayinmu game da wasu. Mu ajizai ne, amma Jehobah da Yesu ba sa yin kuskure. Duk da haka, sun canja ra’ayinsu sa’ad da yanayi ya bukaci hakan, shin bai kamata mu yi koyi da su kuma mu canja ra’ayinmu ba, idan yanayi ya bukace mu mu yi hakan?

Sa’ad da kake la’akari game da makasudai a bautar Jehobah, canja ra’ayinka zai iya zama abin da ya dace. Wasu da ake nazarin Littafi Mai Tsarki da su kuma sun soma halartan taro za su iya jinkirin yin baftisma. Wasu ’yan’uwa kuma za iya yin jinkirin soma hidimar majagaba ko da yanayinsu zai ba su damar yin haka. Ƙari ga haka, wasu ’yan’uwa maza suna gudun yin hidima a cikin ikilisiya. (1 Tim. 3:1) Shin akwai ɗaya daga cikin waɗannan yanayoyin da ya shafe ka? Jehobah yana ƙaunarka kuma yana so ka more irin waɗannan gatan. Saboda haka, zai dace ka canja ra’ayinka kuma ka ji daɗin yi wa Allah da kuma mutane hidima.

Wata ’yar’uwa mai suna Ella da ke hidima a wani reshen Shaidun Jehobah a Afirka, ta ce: “Lokacin da na zo Bethel, ban tabbata cewa zan daɗe ba. Ina son in bauta wa Jehobah da dukan zuciyata, amma ba na son in rabu da iyalinmu. Na yi kewarsu sosai da farko! ’Yar’uwa da muke ɗaki ɗaya ta ƙarfafa ni sai na yanke shawarar kasancewa a Bethel. Yanzu na yi shekaru goma a Bethel, amma zan so in ci gaba da zama a Bethel don in riƙa yi wa ’yan’uwana hidima.”

Lokacin da Canja Ra’ayinka Ya Zama Wajibi

Ka tuna da abin da ya faru da Kayinu sa’ad da ya soma kishin ƙanensa kuma ya ɓata rai saboda haushi? Allah ya gaya wa wannan mutum mai fushi cewa zai sami tagomashi idan ya koma ga yin nagarta. Allah ya gargaɗi Kayinu cewa ya yi ƙoƙari ya guji “zunubi” da ke “kwance a bakin ƙofa.” Da Kayinu ya canja ra’ayinsa da kuma halinsa, amma ya ƙi bin gargaɗin da Allah ya ba shi. Abin baƙin ciki, Kayinu ya kashe ƙaninsa kuma saboda haka, ya zama wanda da ya soma kisa a duniya.—Far. 4:2-8.

Ka kuma yi la’akari da misalin Sarki Uzziah. Da farko, ya yi abin da ya faranta wa Jehobah rai kuma ya biɗi Allah. Amma daga baya, Uzziah ya ɓata rawarsa da tsalle ta wajen kasancewa da fahariya. Ya shiga cikin haikali don ya ƙona turare, alhali shi ba firist ba ne. Sa’ad da firistoci suka yi masa gargaɗi cewa kada ya yi taurin kai ta wajen ƙona turaren, shin ya canja ra’ayinsa ne? A’a. A maimakon haka, Uzziah ya “hasala” kuma ya ƙi bin shawararsu. A sakamakon haka, Jehobah ya addabe shi da kuturta.—2 Laba. 26:3-5, 16-20.

Hakika, akwai lokacin da canja ra’ayinmu ya zama wajibi. Ga misalin wani ɗan’uwa mai suna Joachim. Ya yi baftisma a shekara ta 1955, amma aka yi masa yakan zumunci a shekara ta 1978. Bayan sama da shekara 20, ya tuba kuma aka dawo da shi cikin ikilisiya. Kwanan nan, wani ɗan’uwa ya tambaye shi dalilin da ya sa ya daɗe kafin ya ɗauki matakin dawowa. Joachim ya ce: “Fushi da kuma fahariya ne suka sa ni. Na yi da-na-sani cewa na ɓata lokaci sosai. Bayan da aka yi min yakan zumunci, na san cewa Shaidun Jehobah ne suke bin addini na gaskiya.” Ya canja ra’ayinsa kuma ya tuba.

Za mu iya samun kanmu a wani yanayin da zai bukaci mu canja ra’ayinmu da kuma tafarkinmu. Bari mu kasance da ra’ayin yin haka don mu ci gaba da faranta wa Jehobah rai.—Zab. 34:8.

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba