DAGA TARIHINMU
“Eureka Drama” Ya Sa Mutane da Yawa Sun San Gaskiya
A TURANCI, kalmar nan “Eureka” tana nufin “Na samu!” Sa’ad da mutane ke neman zinariya a jihar Kalifoniya a ƙasar Amirka, a ƙarni na 19, mahaƙi yakan yi wannan furucin sa’ad da ya samo zinariya. Amma, Charles Taze Russell da wasu Ɗaliban Littafi Mai Tsarki kamar sa sun sami abin da ya fi zinariya tamani, wato gaskiyar Littafi Mai Tsarki. Kuma sun yi marmarin sanar da wannan gaskiya ga wasu.
A ranin shekara ta 1914, miliyoyin mutane a manyan birane sun kalli fim ɗin “Photo-Drama of Creation” mai tsawon awa takwas da Ɗaliban Littafi Mai Tsarki suka fitar. Fim ɗin yana da kala mai kyau da bayani mai ƙayatarwa da kuma sauti mai daɗi. Wannan fim da aka ɗauko daga Littafi Mai Tsarki ya nuna tarihin ’yan Adam daga farkon halitta zuwa ƙarshen Sarautar Kristi na Shekara Dubu.—R. Yoh. 20:4.a
Waɗanda suke zama a ƙananan garuruwa da ƙauyuka fa? A watan Agusta na 1914, Ɗaliban Littafi Mai Tsarki sun fitar da “Eureka Drama,” wani taƙaitaccen shirin “Photo-Drama of Creation” marar fim don dukan masu son gaskiya su amfana, har da waɗanda ke zama a ƙauyuka da karkara. An tsara wannan taƙaitaccen shirin cikin kashi uku kuma a harsuna da dama: Shirin “Eureka X” yana ɗauke da dukan tattaunawar da kuma kiɗan. Shirin “Eureka Y” yana ɗauke da dukan sauti da kuma hotuna masu kyau. Shirin “Eureka Family Drama” da aka tsara don amfani a cikin gida yana ɗauke da wasu bayanai da kuma waƙoƙi. Ƙari ga haka, ana iya samun garmaho da kuma kayayyakin na’urar nuna fim masu sauƙi daga wurin Ɗaliban Littafi Mai Tsarki.
Ɗaliban Littafi Mai Tsarki za su iya zuwa ƙauyuka da wannan shirin kuma su yi amfani da shi ba tare da bango mai faɗi don nunawa ba. Ta hakan sun kai saƙon Littafi Mai Tsarki zuwa sababbin yankuna. Za a iya kunna shirin “Eureka X,” wanda sauti ne kawai da dare ko da rana. Ƙari ga haka, za a iya kunna na’urar nuna shirin “Eureka Y” ko ba wutar lantarki, ta wajen yin amfani da fitila mai ci da kabad wato, carbide. Wani rahoto da aka bayar a Hasumiyar Tsaro ta harshen Finnish, ya ce: “Za mu iya nuna waɗannan hotunan kusan a ko’ina.” Kuma hakan gaskiya ne!
Ɗaliban Littafi Mai Tsarki ba su yi amfani da manyan wuraren nuna wasa ba, maimakon haka, sun nuna hikima ta wajen yin amfani da ajujuwan makaranta da gidajen kotu da kuma tashoshin jirgin ƙasa, har ma da falon manyan gidaje. An nuna shirin a waje ta wajen yin amfani da farin ƙyalle da aka rataye a gefen rumbu. Wani ɗan’uwa mai suna Anthony Hambuch ya ce: “Manoma sukan jera gungume a cikin gonakinsu don mutane su zauna kuma su kalli shirin.”’Yan’uwa da ke nuna waɗannan shirye-shiryen sun yi amfani da karusa don ɗaukan na’urorinsu da jakunkunarsu da kayayyakin kafa tanti da kuma na yin dahuwa.
A wasu lokuta, mutane ƙalila ne suka kalli shirin, a wasu lokuta kuma, ɗarurruwan mutane ne suka kalli shirin. A ƙasar Amirka, mutane 400 sun taɓa halartan wani shirin da aka nuna a wani gari mai mazauna 150. A wani wuri kuma, wasu sun yi tafiya da ƙafa na tsawon mil biyar, wato kilomita 8 don su kalli shirin. Sautin da maƙwabtan ’Yar’uwa Charlotte Ahlberg a ƙasar Sweden suka ji sa’ad da suka taru a cikin ƙaramin gidanta ya ratsa zuciyarsu sosai. Wajen mutane 1,500 ne suka halarci wani shirin da aka nuna a wani garin da ake haƙar ma’adinai a ƙasar Ostareliya. Hasumiyar Tsaro ta ba da rahoto cewa “hotuna da sautin garmahon sun burge farfesoshi da ɗalibai da ke makarantu da kuma kwalejoji.” Shirin “Eureka Drama” ya yi tashe har ma a wuraren da ake da gidajen silima.
KOYA WA MUTANE GASKIYA
Shirin “Eureka Drama” ya taimaka wajen kafa rukuni don koya wa mutanen da suka so saƙon Littafi Mai Tsarki, kuma wannan rukunin Ɗaliban Littafi Mai Tsarki sukan aika masu yin jawabi don su kafa sababbin rukunonin nazari a wurare dabam-dabam. Ba a san ainihin adadin mutanen da suka kalli shirin “Eureka Drama” ba. An yi amfani da wasu cikin waɗannan shirye-shiryen a kai a kai. Duk da haka, a shekara ta 1915, shirye-shirye guda 14 cikin 86 ne kawai aka ba da rahotonsu a kai a kai. Ko da yake muna baƙin ciki domin ba mu sami cikakken adadin ba, rahoton ƙarshen shekara ya nuna cewa mutane fiye da miliyan ɗaya ne suka kalli wannan shirin. Wajen mutane 30,000 sun ce a ba su littattafan da ke bayyana Littafi Mai Tsarki.
Wataƙila shirin “Eureka Drama” bai kasance wani abu da za a iya tunawa da shi a tarihi ba, amma a bayyane yake cewa miliyoyin mutane ne suka kalli wannan shiri na musamman, daga Ostareliya zuwa Ajantina, daga Afirka ta Kudu zuwa British Isles da Indiya, da kuma Caribbean. Mutane da yawa daga cikinsu sun sami gaskiyar Littafi Mai Tsarki, kuma wannan gaskiyar ta fi zinariya tamani, kuma su ma za su iya cewa “Eureka!”
a Ka duba talifin nan “Daga Tarihinmu, Ya Yi Shekara 100 Yana Ƙarfafa Imaninmu” a Hasumiyar Tsaro ta 15 ga Fabrairu, 2014, shafuffuka na 30-32.