AMSOSHIN TAMBAYOYIN MASU KARATU
Sa’ad da Yesu ya gaya wa Saddukiyawa cewa waɗanda aka tayar daga mutuwa ba za su yi “aure ba, ba a kuwa aurar da su” ba. (Luk 20:34-36) Shin yana magana ne game da waɗanda za a tayar a nan duniya?
Wannan tambaya ce mai muhimmanci musamman ma ga waɗanda matansu ko mazansu sun mutu. Waɗannan za su yi marmarin sake haɗuwa da matansu ko mazansu a sabuwar duniya. Wani da matarsa ta mutu ya ce: “Ni da matata ba mu tsai da shawarar raba aurenmu ba. Mun so mu ci gaba da bauta wa Jehobah cikin haɗin kai a matsayin mata da miji har abada. Har ila, wannan muradin bai fita a zuciyata ba.” Shin akwai dalilin yin bege cewa waɗanda za a ta da daga matattu za su sake aure kuwa? Amsar ita ce, ba mu da cikakken bayani a kan wannan batun.
A cikin shekaru da yawa yanzu, littattafanmu sun ce kalaman Yesu game da tashin matattu da kuma sake aure suna nuni ne ga tashin matattu da za a yi a duniya kuma waɗanda za a tayar a duniya ba za su sake aure kuma ba.a (Mat. 22:29, 30; Mar. 12:24, 25; Luk 20:34-36) Shin Yesu yana magana game da waɗanda za su je sama ne? Bari mu bincika abin da Yesu ya ce game da wannan maimakon ba da amsar kai tsaye.
Ka yi la’akari da yanayin. (Karanta Luka 20:27-33.) Saddukiyawa waɗanda ba su gaskata da tashin matattu ba sun yi wa Yesu tambaya game da tashin matattu da kuma auren gādo don su kama shi da laifi ne.b Yesu ya ce musu: “’Ya’yan duniyan nan suna aure, ana kuwa aurad da su: amma su waɗanda aka maishe su sun isa su kai wancan zamani da tashi kuma daga matattu, ba su aure ba, ba a kuwa aurad da su gama ba shi yiwuwa kuma su sake mutuwa: gama sun zama daidai da mala’iku; ’ya’yan Allah suke kuwa, da shi ke ’ya’yan tashin matattu ne.”—Luk 20:34-36.
Me ya sa littattafanmu suka ce wataƙila Yesu yana magana ne game da tashin matattu da za a yi a duniya? Akwai dalilai biyu da suka sa aka faɗi hakan. Na ɗaya, wataƙila Saddukiyawan suna magana ne game da tashin matattu da za a yi a duniya kuma Yesu ya ba su amsar da ta yi daidai da tambayarsu. Na biyu kuma, Yesu ya kammala amsarsa ta wurin yin magana game da amintattun bayin Allah kamar su Ibrahim da Ishaƙu da kuma Yaƙubu da za a tayar a nan duniya.—Luk 20:37, 38.
Amma, wataƙila Yesu yana magana ne game da tashin matattu zuwa sama. Me ya sa muka ce haka? Bari mu yi la’akari da wasu fitattun furuci guda biyu.
“Amma su waɗanda aka maishe su sun isa [cancanci] . . . tashi kuma daga matattu.” Amintattun shafaffu sun “cancanci zama a Mulkin Allah.” (2 Tas. 1:5, 11, Littafi Mai Tsarki) Hadayar Yesu ta sa sun cancanci samun rai, saboda haka, ba sa mutuwa kamar masu zunubi. (Rom. 5:1, 18; 8:1) Ana kiran waɗannan ‘masu albarka kuma masu tsarki,’ kuma sun cancanci a tayar da su zuwa sama. (R. Yoh. 20:5, 6) Akasin wannan, waɗanda za a tayar da su su yi rayuwa a duniya sun ƙunshi “marasa adalci.” (A. M. 24:15) Shin za a iya ce waɗannan sun “cancanci” tashi daga mutuwa?
“Ba shi yiwuwa kuma su sake mutuwa.” Yesu bai ce: “Ba za su mutu ba kuma.” Amma ya ce: ‘Ba shi yiwuwa kuma su sake mutuwa.’ Wasu fassarar Littafi Mai Tsarki sun ce “ba sa ƙarƙashin ikon mutuwa kuma” da “mutuwa ba ta da iko a kansu kuma ba.” Za a tayar da shafaffu da suka gama rayuwarsu a duniya cikin aminci zuwa sama kuma a ba su jiki marar mutuwa, wato ba za su sake mutuwa ba. (1 Kor. 15:53, 54) Mutuwa ba ta da iko kuma bisa waɗanda za su tafi sama.c
Mene ne za mu iya kammala bisa ga abin da muka tattauna? A lokacin da Yesu ya yi magana game da aure da kuma tashin matattu, wataƙila yana magana ne a kan waɗanda za su je sama. Idan haka ne, to, yana nufin cewa waɗanda za a tayar da su zuwa sama ba za su yi aure ba, ba kuwa za su mutu ba. Ƙari ga haka, za su kasance kamar mala’iku a wani fanni. Amma idan muka kammala hakan, tambayoyi da yawa za su iya tasowa.
Na farko, me ya sa Yesu ya yi magana game da tashin matattu zuwa sama sa’ad da yake ba da amsa ga Saddukiyawa da wataƙila suna tunanin tashin matattu a nan duniya? Ba a kowane lokaci ba ne Yesu yake ba magabtansa amsa bisa abin da ke zuciyarsu ba. Alal misali, sa’ad da Yahudawa suka so Yesu ya nuna musu wata alama, ya ce musu: “Ku rushe haikalin nan, a cikin kwana uku sai in tashe shi kuma.” Wataƙila Yesu ya san cewa suna nufin ainihin haikali ne, amma “maganar haikalin jikinsa yake yi.” (Yoh. 2:18-21) Wataƙila Yesu ya ga bai dace ya ba da amsa ga waɗannan Saddukiyawan ba da yake suna gwada shi ne. Ban da haka ma, ba su gaskata da tashin matattu da kuma wanzuwar mala’iku ba. (Mis. 23:9; Mat. 7:6; A. M. 23:8) Maimakon haka, wataƙila ya so ya bayyana wa almajiransa masu aminci wata gaskiya game da tashi daga matattu zuwa sama da yake wata rana su ma za su kasance cikin waɗanda za su je sama.
Na biyu, me ya sa Yesu ya kammala tattaunawarsa ta wajen yin magana game da Ibrahim da Ishaƙu da Yaƙubu waɗanda za a tayar da su a nan duniya? (Karanta Matta 22:31, 32.) Ka lura cewa kafin Yesu ya ambaci ubannin iyali, ya ce, “amma ga zancen tashin matattu.” Wataƙila Yesu ya yi amfani da wannan furucin don canja batu daga waɗanda za su je sama zuwa waɗanda za su tashi a nan duniya. Da yake Yesu ya san cewa Saddukiyawa sun gaskata da littattafan da Allah ya hure Musa ya rubuta, sai ya yi kaulin abin da Jehobah ya ce wa Musa sa’ad da ya sa kurmi ya ci wuta kuma ya yi hakan ne don ya tabbatar musu cewa lallai za a yi tashin matattu a nan duniya.—Fit. 3:1-6.
Na uku, idan kalaman Yesu game da tashin matattu da yin aure yana nuni ne ga waɗanda za su je sama, shin hakan yana nufin cewa waɗanda za a tayar a nan duniya za su iya yin aure ne? Kalmar Allah ba ta amsa wannan tambayar kai tsaye ba. Idan har Yesu yana magana ne game da tashin matattu zuwa sama, to, furucinsa bai ba da ƙarin haske a kan ko waɗanda za a tayar a duniya za su iya yin aure sa’ad da duniya ta zama aljanna ba.
Littafi Mai Tsarki ya ce mutuwa tana kashe aure. Saboda haka, idan wani da matarsa ta rasu, ko wata da mijinta ya rasu ta sake yin aure, bai kamata ta ji cewa ta yi laifi ba. Wannan shawara ce da mutum zai yanke da kansa, kuma bai kamata a yi musu sūka ba idan suka sake yin aure saboda kaɗaici.—Rom. 7:2, 3; 1 Kor. 7:39.
Babu shakka, an san muna da tambayoyi da yawa da za mu yi game da rayuwa a sabuwar duniya. Maimakon mu riƙa ɓata lokaci muna yin irin waɗannan tambayoyin, zai dace mu jira mu ga abin da zai faru a lokacin. Amma muna da tabbaci cewa: Mutane masu biyayya za su yi farin ciki, don Jehobah zai buɗe hannunsa ya biya bukatu da kuma muradin mutane a hanyar da ta dace.—Zab. 145:16.
a Ka duba Hasumiyar Tsaro ta 1 ga Yuni, 1987, shafuffuka na 30-31 na Turanci.
b A zamanin dā, ana auren gādo, wato mutum yana iya aurar matar ɗan’uwansa da ya mutu kuma a haifa masa ’ya’ya don kada a manta da sunansa ko zuriyarsa.—Far. 38:8; K. Sha 25:5, 6.
c Waɗanda aka tayar daga mutuwa a nan duniya za su yi rayuwa har abada kuma ba za a ba su rai marar mutuwa ba. Idan kana so ka san bambancin da ke tsakanin rai marar mutuwa da kuma rai na har abada, ka duba Hasumiyar Tsaro ta 15 ga Fabrairu, 2009, shafi na 25, sakin layi na 6.