Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w14 7/15 pp. 23-27
  • “Ku Ne Shaiduna”

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • “Ku Ne Shaiduna”
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2014
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • SHAIDUN ALLAH A ZAMANIN DĀ
  • “GA SHI, ZAN YI WANI SABON AL’AMARI”
  • MA’ANAR SUNAN ALLAH
  • YADDA ZA MU NUNA GODIYA
  • Ka Daraja Suna Mai Girma Na Jehobah
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2013
  • Jehobah Ya Ɗaukaka Sunansa
    Mulkin Allah Yana Sarauta!
  • Allah Yana da Suna
    Ka Koya Daga Wurin Babban Malami
  • Sunan Jehobah Yana da Muhimmanci a Gare Mu
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2025
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2014
w14 7/15 pp. 23-27

“Ku Ne Shaiduna”

“Ku ne shaiduna, in ji Ubangiji.”—ISHA. 43:10.

MECE CE AMSARKA?

  • Me ya sa za a iya ce da Isra’ilawa Shaidun Jehobah?

  • Mene ne ma’anar sunan Allah?

  • Ta yaya za mu nuna cewa mun daraja yadda ake kiranmu da suna mai tsarki na Allah?

1, 2. (a) Mene ne zama Mashaidi yake nufi? (b) Me ya sa Jehobah bai dangana da kafofin yaɗa labarai na duniyar nan ba?

MENE NE zama mashaidi yake nufi? Wani ƙamus ya ce mashaidi shi ne “mutumin da ya ga wani abu da ya auku kuma ya ba da rahoton.” Akwai wata jarida a Afirka ta Kudu da ake kira The Witness, wato Shaida. An soma buga wannan jaridar fiye da shekaru 160 da suka shige. Wannan sunan ya dace domin manufar jarida ita ce ta bayyana abubuwan da suka auku dalla-dalla. Mutumin da ya soma wallafa wannan jaridar ya yi alkawari cewa “labaran gaskiya ne kawai za a riƙa wallafawa a jaridar.”

2 Abin baƙin ciki, kafofin yaɗa labarai da yawa a yau ba sa yawan faɗin gaskiya. Hakika, ba su faɗi gaskiya game da Allah ba da kuma abubuwan da ya yi. Amma Jehobah, wanda shi ne Maɗaukakin Sarki bai dangana da kafofin yaɗa labarai na duniya ba. Allah ya furta kalmomi na gaba ta baƙin annabi Ezekiyel. Ya ce: “Al’umma kuwa za su sani ni ne Ubangiji.” (Ezek. 39:7, Littafi Mai Tsarki) Jehobah yana da Shaidu kusan miliyan takwas da suke gaya wa mutane a faɗin duniya game da shi. Waɗannan Shaidun suna sanar da mutane abubuwan da Jehobah ya yi a dā da waɗanda yake yi yanzu da kuma waɗanda zai yi a nan gaba. Littafin Ishaya 43:10 ta ce: “Ku ne shaiduna, in ji Ubangiji, barana kuma wanda na zaɓa.” Idan muka sa yin wa’azi ya zama abu mafi muhimmanci a rayuwarmu, za mu nuna cewa lallai, mu Shaidun Jehobah ne.

3, 4. (a) A wace shekara ce aka soma kiran Ɗaliban Littafi Mai Tsarki Shaidun Jehobah kuma yaya suka ji? (Ka duba hoton da ke shafi na 23.) (b) Waɗanne tambayoyi ne za mu tattauna yanzu?

3 Sunan Jehobah zai kasance har abada domin shi “Sarki na zamanu” ne. Kuma shi da kansa ya ce: “Wannan shi ne sunana har abada, shi ne kuma inda za a tuna da ni har tsararaki duka.” (1 Tim. 1:17; Fit. 3:15; ka gwada Mai-Wa’azi 2:16.) A shekara ta 1931, Ɗaliban Littafi Mai Tsarki sun soma yin amfani da sunan nan Shaidun Jehobah. Saboda haka, mutane sun aika wasiƙu don su nuna godiyarsu kuma aka wallafa da yawa daga ciki a wannan mujallar. Wata ikilisiya a ƙasar Kanada ta rubuta cewa wannan sabon sunan ya sa sun daɗa ƙuduri niyyar yin rayuwar da za ta sa a yabi sunan Jehobah.

4 Ta yaya za ka nuna cewa ka daraja yadda ake kiranka Mashaidin Jehobah? Kuma, shin za ka iya bayyana dalilin da ya sa Jehobah ya kira mu Shaidunsa kamar yadda littafin Ishaya ya nuna?

SHAIDUN ALLAH A ZAMANIN DĀ

5, 6. (a) Ta yaya iyaye Isra’ilawa suka ba da shaida game da Jehobah? (b) Wane abu ne kuma aka bukaci iyaye Isra’ilawa su yi, kuma me ya sa iyaye a yau suke bukatar su yi hakan?

5 Jehobah ya zaɓi Isra’ilawa don su zama shaidunsa. Kowane Ba’isra’ile yana da gatan ba da shaida game da shi. (Isha. 43:10) Alal misali, hanya ɗaya da iyaye suke ba da shaida ita ce ta wajen koya wa yaransu abubuwan da Allah ya yi a zamanin dā. Jehobah ya umurci iyaye su koya wa yaransu game da Idin Ƙetarewa. Ya ce musu: “Zai faru kuma, sa’anda ’ya’yanku za su ce maku, Mene ne dalilinku da wannan ibada? Za ku ce, Hadaya ce ta faskar Ubangiji, da ya ƙetare gidajen ’ya’yan Isra’ila cikin Masar, sa’anda ya bugi Masarawa, ya ceci gidajenmu kuma.” (Fit. 12:26, 27) Iyayen sun bayyana cewa Fir’auna bai yarda Isra’ilawa su je su yi ibada wa Jehobah a jeji ba. Fir’auna ya ce: “Wane ne Ubangiji, har da zan ji muryatasa in saki Isra’ila kuma?” (Fit. 5:2) Iyayen su gaya wa yaransu yadda Jehobah ya nuna wa Fir’auna da sauran mutane cewa shi ne Allah Maɗaukakin Sarki. Ya buga Masarawa da annoba goma kuma ya ceci Isra’ilawa daga rundunar Masarawa a Jar Teku. Isra’ilawa sun ga cewa Jehobah Allah na gaskiya ne kuma yana cika alkawuransa.

6 Isra’ilawa sun san cewa gata ne babba su zama shaidun Jehobah. Sun gaya wa yaransu da kuma bayin da suke aiki a gidajensu abubuwa masu ban al’ajabi da Jehobah ya yi. Isra’ilawa sun kuma san cewa suna bukatar su kasance da ɗabi’a mai kyau. Jehobah ya ce: “Sai ku zama masu-tsarki: gama ni Ubangiji Allahnku mai-tsarki ne.” Iyaye Isra’ilawa suna bukatar su koyar da yaransu su kasance masu tsarki, wato su bi ƙa’idodin Jehobah. (Lev. 19:2; K. Sha 6:6, 7) Wajibi ne iyaye a yau ma su yi hakan, kuma su koya wa yaransu su yi rayuwar da za ta sa a yabi suna mai girma na Allah!—Karanta Misalai 1:8; Afisawa 6:4.

7. (a) Sa’ad da Isra’ilawa suka yi biyayya ga Jehobah, ta yaya al’ummai da ke kewaye da su suka ji? (b) Wane gata ne dukan mutanen da suke amsa sunan Jehobah suke da shi?

7 Jehobah ya albarkaci Isra’ilawa sa’ad da suka yi masa biyayya. A sakamakon haka, al’ummai da ke kewaye da su sun ga cewa Jehobah yana kāre bayinsa. (K. Sha 28:10) Amma abin baƙin ciki, shekarun da Isra’ilawa suka yi rashin aminci ga Jehobah sun fi yawa. Sun bauta wa gumakan Ka’aniyawa kuma kamar waɗannan gumaka,sun yi zalunci kuma suka yi hadaya ta ƙonawa da ’ya’yansu. Ƙari ga haka, sun wulaƙanta talakawa. Mun koyi muhimmin darasi daga misalinsu. Muna bukatar mu yi koyi da Jehobah kuma mu kasance masu tsarki domin mu bayin Allah Mafi Tsarki ne.

“GA SHI, ZAN YI WANI SABON AL’AMARI”

8. Mene ne Jehobah ya ce Ishaya ya yi, kuma wane mataki ne Ishaya ya ɗauka?

8 Jehobah ya yi amfani da annabi Ishaya don ya ja kunnen Isra’ilawa cewa zai halaka Urushalima, kuma zai bari a kai bayinsa bauta a wata ƙasa. Jehobah ya kuma ce zai yi “wani sabon al’amari” kuma zai cece su daga bauta a wata hanya mai ban mamaki. (Isha. 43:19) Jehobah ya san cewa Isra’ilawa ba za su tuba ba, amma ya gaya wa Ishaya cewa ya ci gaba da yi musu gargaɗi. Littafin Ishaya sura ta ɗaya zuwa shida suna ɗauke da waɗannan gargaɗin. Ishaya ya so ya san shekarun da Isra’ilawa za su ci gaba da yin rashin biyayya. Sai Allah ya ce: “Har birane su zama kangaye, babu mazauni a ciki, gidaje kuma babu mutum a ciki, ƙasa ta yi daji sarai.”—Karanta Ishaya 6:8-11.

9. (a) A wane lokaci ne annabcin da Ishaya ya yi game da Urushalima ya cika? (b) Wane gargaɗi ne muke bukatar mu saurara a yau?

9 Ishaya ya ci gaba da jan kunnen Isra’ilawa game da wannan halakar da ke tafe har fiye da shekaru 46. Ya soma wannan annabcin a shekara ta ƙarshe da Sarki Uzziah ya yi sarauta, wato a shekara ta 778 kafin zamaninmu zuwa shekara ta 732 sa’ad da Sarki Hezekiya yake sarauta. Bayan haka, Jehobah ya ci gaba da yi wa bayinsa gargaɗi har shekara ta 607 kafin zamaninmu sa’ad da aka halaka Urushalima. An ja wa Isra’ilawa kunne shekaru da yawa kafin a halaka su. Hakazalika a yau, Jehobah yana yin amfani da bayinsa don ya ja wa mutane kunne game da abin da zai faru a nan gaba. Mujallar Hasumiyar Tsaro ta daɗe tana gaya wa mutane cewa nan ba da daɗewa ba, za a kawo ƙarshen mulkin Shaiɗan bisa duniya kuma Yesu Kristi zai soma sarautarsa na shekara dubu ɗaya.—R. Yoh. 20:1-3, 6.

10, 11. Ta yaya Isra’ilawa a Babila suka shaida cikar annabcin Ishaya?

10 Wasu Isra’ilawa sun tsira daga halakar Urushalima. Me ya sa? Domin sun yi biyayya ga umurnin da Jehobah ya bayar cewa su ba da kai ga Babiloniyawa kuma su yarda a kai su bauta. (Irm. 27:11, 12) Shekaru saba’in bayan haka, ƙalilan cikinsu sun shaida cikar wani annabcin da Ishaya ya yi, ya ce: “Allah Mai Tsarki na Isra’ila, Ubangiji wanda ya fanshe ku ya ce, ‘Domin in cece ku zan aiko sojoji gāba da Babila, Zan rushe ƙofofin birni.’”—Isha. 43:14, LMT.

11 Jehobah ya cika wannan annabcin a hanya mai ban al’ajabi. A wata yammar watan Oktoba na shekara ta 539 kafin zamaninmu, Sarkin Babila da dakarunsa suna biki don su girmama allolinsu. Har ma suna shan ruwan inabi da kwafuna masu tsarki da suka sace daga haikalin Jehobah. Amma a daren, Sarki Sairus da rundunarsa sun kai wa Babila hari kuma sun ci su da yaƙi. A shekara ta 538 ko 537, Sairus ya ce Yahudawa su koma Urushalima kuma su sake gina haikalin Allah. Jehobah ya kāre su sa’ad da suke komawa. Dukan waɗannan abubuwan sun faru saboda annabcin da Ishaya ya yi. Yadda Isra’ilawa suka kammala gina haikalin da ke Urushalima ya sa sun shaida cewa Jehobah Allah na gaskiya ne kuma ba ya fasa cika alkawarinsa. Jehobah ya kira Yahudawan da suka dawo daga Urushalima “mutanen da na yi domin kaina, su ne za su bayyana yabona.”—Isha. 43:21; 44:26-28.

12, 13. (a) Su wane ne suka haɗa kai da Isra’ilawa wajen gina haikalin? (b) Mene ne ake bukatar “waɗansu tumaki” su yi yayin da suke goyon bayan “Isra’ila na Allah,” kuma mene ne suke ɗokin gani?

12 Sa’ad da Isra’ilawa suka dawo don su gina haikalin, baƙi da yawa sun soma bauta wa Jehobah tare da su. Daga baya, baƙin da suka soma bauta wa Jehobah suka ƙaru. (Ezra 2:58, 64, 65; Esther 8:17) A yau, Kiristoci shafaffu al’ummar Allah ne, wato “Isra’ila na Allah” kuma “taro mai-girma” na “waɗansu tumaki” suna bauta wa Jehobah tare da su. (R. Yoh. 7:9, 10; Yoh. 10:16; Gal. 6:16) Ana kiran shafaffu da waɗansu tumaki Shaidun Jehobah kuma hakan babban gata ne.

13 A sabuwar duniya, taro mai girma za su sami zarafi mai kyau na gaya wa mutanen da suka tashi daga matattu abubuwan da suka shaida a matsayin Shaidun Jehobah a kwanaki na ƙarshe. Muna bukatar mu kasance da tsarki domin mu sami wannan zarafin a nan gaba. Muna yin kuskure kowace rana ko da yake muna ƙoƙari mu bi ƙa’idodin Jehobah. Saboda haka, muna bukatar mu riƙa roƙon Jehobah kullum domin ya gafarce mu. Idan muka kasance da tsarki, za mu nuna cewa muna godiya don yadda Jehobah ya ba mu gatan zama Shaidunsa.—Karanta 1 Yohanna 1:8, 9.

MA’ANAR SUNAN ALLAH

14. Mene ne ma’anar sunan nan Jehobah?

14 Domin mu fahimci dalilin da ya sa gata ne sosai a kira mu da sunan Jehobah, muna bukatar mu san ma’anar sunan. An ɗauko sunan daga aikatau na Ibrananci da ke nufi “yana zama.” Mun fahimci cewa sunan Allah yana nufin “Yana Sa Ya Kasance.” Jehobah ya zaɓi wannan sunan domin yana so mu fahimci ko wane ne shi. Shi ne mahaliccin dukan abu kuma babu abin da ya isa ya hana shi yin abin da yake so, ko Shaiɗan ma ya yi kaɗan.

15. Mene ne za mu iya koya game da sunan Jehobah daga abin da ya gaya wa Musa? (Ka duba akwatin nan “Suna Mai Cike da Ma’ana.”)

15 Jehobah ya bayyana wa Musa ma’anar sunansa da kyau. Sa’ad da Jehobah ya tura Musa ya ’yantar da bayinsa daga hannun Masarawa, ya ce masa: “Zan Zama Abin da Nake So In Zama.” Sai ya daɗa: “Zan Zama ya aiko ni wurinka.” (Fit. 3:14, New World Translation) Saboda haka, Jehobah zai zama duk abin da yake so don ya cika nufinsa. Jehobah ya yi iya ƙoƙarinsa don ya zama Mai-ceto da Mai-kāriya da Mai-kula da kuma Mai-tanadarwa ga Isra’ilawa.

YADDA ZA MU NUNA GODIYA

16, 17. (a) Ta yaya za mu nuna cewa mun daraja gatan da muke da shi na kiranmu da sunan Allah? (b) Mene ne za mu tattauna a talifi na gaba?

16 A yau, Jehobah bai canja ba. Sunansa yana tuna mana cewa zai zama kowane abu da yake so don ya kula da bayinsa. Alal misali, yana tanadar mana da dukan bukatunmu don mu rayu kuma mu kasance da imani sosai. Akwai wani abu kuma da sunan Jehobah ya koya mana. Me ke nan? Jehobah zai iya sa halittarsa ta zama duk abin da yake so don ya cika nufinsa. Alal misali, yana amfani da Shaidunsa don su cim ma aikinsa. Ya kamata hakan ya motsa mu mu yi rayuwar da za ta ɗaukaka shi. Wani mai suna Kåre daga ƙasar Norway ɗan shekara 84 da ya yi fiye da shekara 70 yana bauta wa Jehobah ya ce: “Bauta wa Jehobah, Maɗaukakin Sarki, da kuma kasancewa cikin mutanen da ake kiransu da sunansa, babban gata ne sosai. Gata ne sosai koya wa mutane gaskiyar da ke cikin Littafi Mai Tsarki da kuma yadda sanin wannan gaskiyar yake sa su farin ciki. Alal misali, ina matuƙar farin ciki sa’ad da na koya musu yadda hadayar Kristi yake amfanarmu kuma ya sa mu sami begen yin rayuwa cikin salama a duniya a nan gaba.”

17 A wasu wurare a duniya yau, yana da wuya a sami mutanen da suke so su koya game da Jehobah. Amma kamar Ɗan’uwa Kåre, muna farin ciki sa’ad da muka ga ko da mutum ɗaya ne da ya yarda mu koya masa sunan Allah. Amma a wace hanya ce za mu iya zama Shaidun Jehobah kuma mu sake zama shaidun Yesu? Za mu tattauna wannan tambayar a talifi na gaba.

Suna Mai Cike da Ma’ana

Abin da yake nufi

  • “Yana Sa Ya Kasance”

Abin da ya sa ya dace

  • Jehobah ya halicci dukan abu

  • Yana ci gaba da sa nufinsa da ƙudurinsa su cika

Abin da ya nuna

  • Zai zama duk abin da ya dace don ya cika alkawuransa

  • Yana sa halittarsa ta zama duk abin da yake so don ya cika nufinsa

  • Babu abin da ba zai iya yi ba ko kuma ya sa ya kasance don ya cika nufinsa ba

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba