Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w14 6/15 pp. 28-32
  • Ka Taimaka wa Wasu Su Ƙware Sosai

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Ka Taimaka wa Wasu Su Ƙware Sosai
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2014
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • JEHOBAH YANA MAI DA HANKALI GA HALAYENMU NA KIRKI
  • KA MAI DA HANKALI GA HALAYEN KIRKI NA MUTANE
  • KA TAIMAKA MUSU SU ƘWARE SOSAI
  • KA TAIMAKI WASU SU ƘWARE A NAN GABA
  • Ka Faɗi Maganar Allah Da Gaba Gaɗi
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2004
  • “Ku Yi Ta Gina Juna”
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2022
  • Matasa Ku Ci Gaba da Samun Ci Gaba Bayan Kun Yi Baftisma
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2022
  • ꞌYanꞌuwa Maza Matasa, Ku Yi Koyi da Markus da Timoti
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2025
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2014
w14 6/15 pp. 28-32

Ka Taimaka wa Wasu Su Ƙware Sosai

“Da idona a kanka zan ba ka shawara.”—ZAB. 32:8.

MECE CE AMSARKA?

  • Waɗanne misalai ne suka nuna cewa Jehobah yana mai da hankali ga baiwa da bayinsa suke da shi?

  • Me ya sa ya dace mu lura da halaye masu kyau da ’yan’uwanmu suke da su?

  • Ta yaya za a taimaka wa matasa ko kuma waɗanda ba su daɗe da yin baftisma ba su sami ci gaba?

1, 2. Ta yaya Jehobah yake ɗaukan bayinsa a nan duniya?

SA’AD DA iyaye suke kallon yadda yaransu suke wasa, a yawancin lokaci, suna mamakin irin baiwar da yaran suke da ita. Kai kuma fa, ka taɓa lura da hakan kuwa? Wani yaro zai ƙware wajen buga ƙwallo, wani kuma ya ƙware a yin zane-zane ko kuma ƙere-ƙere. Ko da wane irin baiwa ce yaro yake da ita, iyaye suna jin daɗin taimaka masa ya ƙware a yin amfani da shi.

2 Hakazalika, Jehobah yana lura da yaransa da suke nan duniya. Yana ganin bayinsa kamar “dukiyar al’umman duniya.” (Hag. 2:7, Littafi Mai Tsarki) Suna kama da dukiya domin bangaskiyarsu da kuma amincinsu. Wataƙila ka lura cewa wasu cikin ’yan’uwanmu a yau suna da baiwa dabam-dabam. Wasu ’yan’uwa sun ƙware a yin jawabi a gaban jama’a wasu kuma sun ƙware a tsara abubuwa. Wasu ’yan’uwa mata suna saurin koyan yaren wasu kuma su yi wa’azi da shi, wasu kuma sun ƙware wajen kula da marasa lafiya da kuma waɗanda suke bukatar ƙarfafa. (Rom. 16:1, 12) Babu shakka, muna farin cikin kasancewa tare da irin waɗannan ’yan’uwa maza da mata a ikilisiya ɗaya.

3. Waɗanne tambayoyi ne za mu tattauna a wannan talifin?

3 Amma wasu ’yan’uwa da matasa ko kuma waɗanda ba su daɗe da yin baftisma ba za su iya gani cewa ba su da wani amfani a ikilisiya. Ta yaya za mu taimaka musu su ƙware? Ta yaya za mu mai da hankali ga baiwar da suke da shi kuma mu ɗauke su kamar yadda Jehobah yake ɗaukansu?

JEHOBAH YANA MAI DA HANKALI GA HALAYENMU NA KIRKI

4, 5. Ta yaya labarin da ke littafin Alƙalawa 6:11-16 ya nuna cewa Jehobah yana kula da baiwar da bayinsa suke da shi?

4 Labarai da yawa a Littafi Mai Tsarki sun nuna cewa Jehobah yana ga halaye masu kyau na bayinsa da kuma irin baiwar da suke shi. Alal misali, a lokacin da aka zaɓi Gideon don ya ceci mutanen Allah daga hannun Midiyanawa, babu shakka ya yi mamaki sosai da gaisuwar da mala’ikan ya yi masa cewa: “Ubangiji yana tare da kai, ya jarumi.” Wataƙila a lokacin Gideon bai ɗauki kansa wani “jarumi” ba. Amma Jehobah ya ga cewa Gideon mai ƙwazo ne kuma zai iya amfani da shi wajen ceton Isra’ilawa.—Karanta Alƙalawa 6:11-16.

5 Jehobah ya tabbata da Gideon don ya lura da ƙwazonsa. Alal misali, Jehobah ya lura da yadda Gideon yake sussukar alkama. Ƙari ga haka, ya yi wannan aikin da dukan ƙarfinsa. Akwai wani abin da mala’ikan ya lura da shi kuma. A dā, manoma sukan yi sussuka a fili don iska ta riƙa kwashe ƙaiƙayin. Amma Gideon yana da wayo sosai shi ya sa ya yi sussukan a ɓoye don kada Midiyanawa su zo su kwashe amfanin gonarsa. Babu shakka, shi ya sa Jehobah bai ɗauke shi a matsayin manomi mai wayo kawai ba amma mai basira sosai. Hakika, Jehobah ya ga baiwar da Gideon yake da shi kuma ya koyar da shi.

6, 7. (a) Ta yaya yadda Jehobah ya ɗauki annabi Amos ya bambanta da na wasu Isra’ilawa? (b) Me ya nuna cewa annabi Amos haziƙi ne?

6 Hakazalika, Jehobah ya ga wani abu mai kyau a wurin Amos ko da yake wasu za su ga cewa shi shiru-shiru ne kuma ba haziƙi ba ne. Annabin ya kwatanta kansa a matsayin makiyayi da mai noman ’ya’yan ɓaure, wato abinci talakawa ke nan a lokacin. A lokacin da Jehobah ya aiki annabi Amos ya yi wa al’umma goma na Isra’ila da suke bauta wa gumaka kashedi, wasu Isra’ilawa sun ga cewa zaɓen da Allah ya yi bai dace ba.—Karanta Amos 7: 14, 15.

7 Ko da yake annabin ya fito daga ƙauye ne sosai, ya san al’adun sarakunan zamaninsa kuma hakan ya nuna cewa shi haziƙi ne. Wataƙila ya san yanayin ƙasar Isra’ila da wasu ƙasashen da ke kewaye da su da yake yana yawan harka da ’yan kasuwa da suke tafiye-tafiye. (Amos 1:6, 9, 11, 13; 2:8; 6:4-6) Wasu masanan Littafi Mai Tsarki a yau sun ce Amos ƙwararren marubuci ne. Ya yi amfani da kwatanci da kuma fasahar magana. Bai ji tsoron yi wa munafukin firistin nan Amaziah kashedi ba. Hakika, Jehobah ya zaɓi mutumin da ya dace don ya isar da saƙon. Ya ga baiwa da annabin yake da ita da wasu ba su gani ba.—Amos 7:12, 13, 16, 17.

8. (a) Wane tabbaci Jehobah ya ba Dawuda? (b) Me ya sa kalaman littafin Zabura 32:8 yake ƙarfafa waɗanda suke gani ba su ƙware ba?

8 Hakika, Jehobah yana lura da baiwa da kowane bawansa yake da ita. Ya tabbatar wa Dauda cewa zai riƙa masa ja-gora da “idonsa a kansa.” (Karanta Zabura 32:8.) Hakika, wannan abin ƙarfafa ne a gare mu. Ko da ba mu ƙware sosai ba, Jehobah zai iya ba mu ƙarfin da zai taimaka mana mu iya cim ma maƙasudanmu fiye da yadda muke tsammani. Kamar yadda malami yake yi wa ɗalibinsa ja-gora a duk abubuwan da yake yi, haka ma Jehobah yake mana ja-gora don mu iya cim ma maƙasudanmu. Kuma zai yi amfani da ’yan’uwanmu masu bi don su taimaka mana. A waɗanne hanyoyi ke nan?

KA MAI DA HANKALI GA HALAYEN KIRKI NA MUTANE

9. Ta yaya za mu bi umurnin Bulus na lura da halaye masu kyau da ’yan’uwanmu suke da shi?

9 Bulus ya aririce dukan Kiristoci su riƙa “lura” da halaye masu kyau da ’yan’uwanmu suke da su. (Karanta Filibiyawa 2:3, 4.) Ma’anar wannan shawara da Bulus ya yi shi ne mu riƙa mai da hankali ga baiwa da wasu suke da shi kuma mu yaba musu. Yaya muke ji idan wani ya lura da wani abu mai kyau da muka yi kuma ya yaba mana? Hakan yana sa mu ci gaba da ƙwazo. Hakazalika, idan muka lura da halaye masu kyau da ’yan’uwanmu suke da su kuma muka yaba musu, hakan zai sa su ci gaba da ƙoƙari da kuma ƙarfafa dangantakarsu da Jehobah.

10. Su waye ne kuma suke bukatar taimakonmu?

10 Su waye ne kuma za su so mu taimake su? Hakika, dukanmu muna bukatar mutane su ba mu hankalinsu a wasu lokatai. Har ila, ’yan’uwa matasa ko kuma waɗanda ba su daɗe da yin baftisma ba, za su so su riƙa saka hannu a hidimomin da ake yi a ikilisiya. Hakan zai sa su ji cewa su ma suna da amfani a ƙungiyar Jehobah. Da yake Littafi Mai Tsarki ya aririci ’yan’uwa su ƙware, idan ba mu ba su hankalinmu ba, za su ji kamar ba su da amfani kuma hakan zai hana su samun ci gaba.—1 Tim. 3:1.

11. (a) Ta yaya wani dattijo ya taimaka wa wani matashi ya daina jin kunya? (b) Wane darasi ka koya daga labarin Julien?

11 Wani dattijo mai suna Ludovic ma ya amfana daga irin wannan taimakon. Ya ce: “Idan na taimaka wa ’yan’uwa, hakan yana sa su sami ci gaba da sauri.” Sa’ad da Ludovic yake yin kalami game da wani ɗan’uwa mai jin kunya mai suna Julien, ya ce: “Na lura cewa Julien bai da gaba gaɗi a yin wasu ayyuka a cikin ikilisiya, saboda haka, ba ya kintsuwa kuma yana yin wasu abubuwa babu tsari. Amma na ga cewa yana da kirki kuma yana son ya taimaka wa ’yan’uwa a cikin ikilisiya. Saboda haka, na mai da hankali ga halayensa masu kyau don in ƙarfafa shi.” Daga baya, ɗan’uwa Julien ya soma hidima a matsayin bawa mai hidima, kuma yanzu haka shi majagaba ne.

KA TAIMAKA MUSU SU ƘWARE SOSAI

12. Wane hali ne ya kamata mu kasance da shi idan muna son mu taimaka wa wani ya ƙware? Ka ba da misali.

12 Hakika, idan muna son mu taimaka wa wasu, dole ne mu riƙa lura da abubuwan da suke yi. Kamar yadda labarin Julien ya nuna, bai kamata mu mai da hankali da kurakuran mutumin ba, amma mu mai da hankali ga halayensa da ayyukansa masu kyau. Abin da Yesu ya yi wa manzo Bitrus ke nan. Ko da yake a wasu lokatai Bitrus ya yi garaje, amma duk da haka, Yesu ya ba shi suna Kefas, wanda yake nufin dutse. Ta hakan, ya annabta cewa zai zama kamar dutse, wato zai kasance da bangaskiya sosai kamar yadda dutse yake da ƙwari.—Yoh. 1:42.

13, 14. (a) Ta yaya Barnaba ya nuna sanin yakamata a yadda ya bi da matashi Markus? (b) Ta yaya wani ɗan’uwa ya amfana daga irin taimakon da aka ba wa Markus? (Ka duba hoton da ke shafi na 28.)

13 Bari mu bincika labarin Barnaba da kuma Markus. (A. M. 12:25) A lokaci na farko da Bulus da Barnaba suka tafi yin wa’azi a ƙasar waje, wataƙila Markus ne “mai yi musu hidima,” wato mai tanadar musu da abubuwan da suke bukata. Amma sa’ad da suka isa lardin Pamphylia, Markus ya bar abokan tafiyarsa ya koma gida ba zato ba tsammani. (A. M. 13:5, 13) Ko da yake Barnaba ya san abin da Markus ya yi, ya mai da hankali ga halinsa mai kyau kuma daga baya, ya taimaka masa ya ƙware. (A. M. 15:37-39) Hakan ya taimaka wa wannan matashin ya zama bawan Jehobah da ya ƙware. Daga baya, Markus ya taimaka wa Bulus sa’ad da yake kurkuku a Roma. Ƙari ga haka, Bulus ya yabi Barnaba a wasiƙarsa a lokacin da yake aika gaisuwa ga ’yan’uwa da ke ikilisiyar Kolosi. (Kol. 4:10) Babu shakka, Barnaba ya ji daɗi sosai a lokacin da Bulus ya ce a turo masa Markus don ya taimake shi.—2 Tim. 4:11.

14 Wani ɗan’uwa da aka naɗa shi dattijo ba daɗewa ba, mai suna Alexandre ma ya amfana daga taimakon da wani ɗan’uwa ya yi masa. Ya ce: “A lokacin da nake matashi, yin addu’a a cikin jama’a matsala ce babba a gare ni. Wani dattijo ya nuna mini yadda zan iya yin shiri kuma in saki jiki. Maimakon ya daina ba ni damar yin addu’a, sai ya ci gaba da kirana a kai a kai don in yi addu’a sa’ad da ake taron ikilisiya da kuma na fita wa’azi. Daga baya, na kasance da gaba gaɗi sa’ad da nake yin addu’a.”

15. Ta yaya Bulus ya yaba wa ’yan’uwansa masu bi?

15 Sa’ad da muka lura da wani hali mai kyau da ’yan’uwanmu suke da shi, me muke yi? Muna yaba musu kuwa? A littafin Romawa sura 16, Bulus ya yaba wa ’yan’uwa fiye da 20 da yake ƙauna don wasu halayensu masu kyau. (Rom. 16:3-7, 13) Alal misali, Bulus ya yaba wa Andarunikus da Yuniyus don sun riga shi zama Kiristoci da kuma yawan jimirinsu. Ƙari ga haka, Bulus ya ambata sunan mahaifiyar Rufus, wataƙila don irin kulawa da ta yi masa.

16. Wane sakamako za a iya samu idan aka yaba wa matasa?

16 Idan muka yaba wa mutane, za su amfana sosai. Ka yi la’akari da wani ɗan’uwa matashi ɗan Faransa mai suna Rico. Mahaifinsa ba Mashaidin Jehobah ba ne don haka ya tsananta masa sosai a lokacin da yake so ya yi baftisma har hakan ya sa ɗan’uwan sanyin gwiwa. Saboda haka, Rico ya ɗauka cewa sai ya kai shekara sha takwas kafin ya soma bauta wa Jehobah da kyau. Ƙari ga haka, yana baƙin ciki don yaran makarantarsu suna masa ba’a. Dattijon da aka ce ya yi nazari da shi mai suna Frédéric, ya ce: “Na yaba wa Rico kuma na gaya masa cewa yana fuskantar hamayya ne don yana gaya wa mutane abin da yake koya daga Littafi Mai Tsarki kuma hakan ya nuna cewa shi mai gaba gaɗi ne.” Wannan furucin yabo ya taimaka wa Rico ya ƙarfafa bangaskiyarsa kuma ya kusaci mahaifinsa. A hankali, Rico ya yi baftisma a lokacin da yake shekara 12.

17. (a) Ta yaya za mu taimaka wa ’yan’uwa su samu ci gaba? (b) Ta yaya wani mai wa’azi a ƙasar waje ya taimaka wa matasa, kuma da wane sakamako?

17 A duk lokacin da muka yaba wa ’yan’uwa don wani abu mai kyau da suka yi, muna ƙarfafa su su bauta wa Jehobah da kyau. Wata ’yar’uwa da ta daɗe tana hidima a Bethel mai suna Sylvie,a ta ce mata ma za su iya yaba wa ’yan’uwa maza. A yawancin lokaci, mata sukan lura da wasu abubuwan da maza ba su gani ba. Hakika, ƙarfafawarsu za ta iya sa wanda ’yan’uwa maza suke yi ya daɗa armashi. Kuma tana ganin hakkinta ne ta yi hakan. (Mis. 3:27) Wani ɗan’uwa mai wa’azi a ƙasar waje mai suna Jérôme da yake hidima a ƙasar da ake kira French Guiana, ya taimaka wa ’yan’uwa da yawa su soma irin hidima da yake yi. Ya ce: “Na lura cewa idan na yaba wa ’yan’uwa matasa a kan wani abu mai kyau da suka yi a hidima ko kuma wani kalami mai kyau da suka yi, hakan yana sa su kasance da gaba gaɗi a yin wasu abubuwa kuma su ƙware.”

18. Me ya sa yin aiki tare da matasa yake da amfani?

18 Za mu iya ƙarfafa ’yan’uwa su ƙware ta wajen yin aiki tare da su. Dattijo zai iya gaya wa wani matashi da ya iya yin amfani da kwamfuta ya gurza musu bayanai daga dandalin jw.org da za su iya ƙarfafa tsofaffi da ba su da kwamfuta. Ko idan kana da wani gyara da za ka yi a Majami’ar Mulki za ka iya kiran wani matashi don ku yi aikin tare. Yin aiki tare da matasa zai ba ka damar lura da baiwar da suke da shi don ka yaba musu kuma ka ji ra’ayinsu.—Mis. 15:23.

KA TAIMAKI WASU SU ƘWARE A NAN GABA

19, 20. Me ya sa ya kamata mu taimaka wa ’yan’uwa su sami ci gaba?

19 A lokacin da Jehobah ya naɗa Joshua ya ja-goranci Isra’ilawa, ya umurci Musa ya “ƙarfafa” shi. (Karanta Kubawar Shari’a 3:28.) A yau mutane da yawa suna shigowa cikin ƙungiyar Jehobah. Ana bukatar ’yan’uwa maza su yi wasu ayyuka a cikin ikilisiya. Saboda haka, ya kamata ’yan’uwa a ikilisiya su taimaka wa waɗanda ba su daɗe da yin baftisma ba su ƙware. Ta hakan, da yawa za su soma hidima ta cikakken lokaci, kuma ’yan’uwa maza da yawa za su “iya su koya ma waɗansu” Kalmar Allah da kyau.—2 Tim. 2:2.

20 Ko da muna babbar ikilisiya ko kuma rukunin da bai kai ikilisiya ba, zai dace mu riƙa taimakawa juna don nan gaba. Abin da zai taimaka mana shi ne yin koyi da Jehobah da kullum yake lura da halaye masu kyau da bayinsa suke da su.

a An canja wasu sunaye.

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba