Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w25 Afrilu pp. 26-31
  • ꞌYanꞌuwa Maza Matasa, Ku Yi Koyi da Markus da Timoti

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • ꞌYanꞌuwa Maza Matasa, Ku Yi Koyi da Markus da Timoti
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2025
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • KU BI MISALIN MARKUS TA YIN HIDIMA
  • KU BI MISALIN TIMOTI TA WAJEN ƘAUNAR MUTANE
  • SHAWARAR BULUS ZAI TAIMAKA MAKA
  • ZA KA SAMI ALBARKU DA YAWA IDAN KA YI WA MUTANE HIDIMA
  • ꞌYanꞌuwa Maza​—⁠Kuna Kokari don Ku Zama Bayi Masu Hidima?
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2024
  • “Dana Cikin Ubangiji, Kaunatacce, Mai-Aminci.”
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Wa’azi)—2016
  • Ku Tsai da Shawarwari da Za Su Nuna Kun Dogara Ga Jehobah
    Littafin Taro Don Rayuwa ta Kirista da Hidimarmu—2023
  • Ka Tuna Cewa Jehobah “Allah Mai Rai” Ne
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2024
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2025
w25 Afrilu pp. 26-31

TALIFIN NAZARI NA 18

WAƘA TA 65 Mu Riƙa Samun Ci Gaba!

ꞌYanꞌuwa Maza Matasa, Ku Yi Koyi da Markus da Timoti

“Ka nemi Markus ka zo tare da shi, saboda yana da amfani sosai gare ni cikin hidimata.”—2 TIM. 4:11.

ABIN DA ZA MU KOYA

Za mu ga yadda misalin Markus da Timoti zai taimaka wa ꞌyanꞌuwa maza matasa su kasance da halayen da ake bukata na yin hidima.

1-2. Waɗanne abubuwa ne da za su iya hana Markus da Timoti faɗaɗa hidimarsu?

ꞌYANꞌUWA maza matasa, za ku so ku faɗaɗa hidimarku ga Jehobah kuma ku ƙara taimaka wa ꞌyanꞌuwa a ikilisiya? Babu shakka za ku so ku yi hakan. Muna farin cikin ganin matasa maza da yawa da suke da niyyar yin hidima da kuma taimaka wa ꞌyanꞌuwa! (Zab. 110:3) Amma yin hakan a wasu lokuta bai da sauƙi. Duk da haka, kada ka yi jinkirin faɗaɗa hidimarka don kawai ba ka san yadda abubuwa za su kasance ba. Ka taɓa ƙin wani aiki don kana ganin ba za ka iya yi ba? Idan haka ne, ba kai ne mutum na farko da ya taɓa yin hakan ba.

2 Markus da Timoti ma sun taɓa ji kamar ba za su iya yin wani aiki da aka ba su ba. Ko da yake ba su san yadda abubuwa za su kasance da su ba, kuma wataƙila sun ga kamar ba za su iya yin aikin ba, ba su bar hakan ya hana su yin hidimar ba. Mai yiwuwa, Markus yana jin daɗin zama da mahaifiyarsa a gidansu lokacin da manzo Bulus ya gayyace shi ya zo ya bi shi da Barnaba zuwa waꞌazi. (A. M. 12:​12, 13, 25) Duk da haka, Markus ya bar gida don ya faɗaɗa hidimarsa ga Jehobah. Da farko ya je Antakiya. Daga baya ya bi Bulus da Barnaba zuwa wurare masu nisa. (A. M. 13:​1-5) Mai yiwuwa, Timoti ma yana zama da iyayensa ne lokacin da Bulus ya ce masa ya zo su je waꞌazi. A lokacin Timoti matashi ne, mai yiwuwa zai ji kamar bai cancanci ya yi waꞌazi tare da Bulus ba. (Ka duba 1 Korintiyawa 16:​10, 11 da 1 Timoti 4:12.) Duk da haka, ya yarda ya bi Bulus kuma ya sami albarku masu yawa don wannan shawarar da ya yanke.—A. M. 16:​3-5.

3. (a) Ta yaya muka san cewa Bulus ya ji daɗin aiki tare da Markus da Timoti? (2 Timoti 4:​6, 9, 11) (Ka kuma duba hotunan.) (b) Waɗanne tambayoyi ne za mu tattauna a wannan talifin?

3 Markus da Timoti sun koyi yadda za su yi ayyuka dabam-dabam a ikilisiya tun suna matasa. Bulus ya ji daɗin su ba kaɗan ba, shi ya sa lokacin da ya kusa ya mutu ya ce su zo su zauna tare da shi. (Karanta 2 Timoti 4:​6, 9, 11.) Waɗanne halaye ne Markus da Timoti suke da su da ya sa Bulus ya ƙaunace su kuma ya yarda da su? Ta yaya matasa maza za su yi koyi da su? Kuma ta yaya za su amfana daga shawarwari masu kyau da Bulus ya bayar?

Hotuna: Na 1. Markus yana shirya wa Bulus da Barnaba abinci da ruwan sha. Na 2. Timoti yana karanta wa wasu dattawa wasiƙa, kuma dukansu suna saurara.

Markus da Timoti sun taimaka wa Bulus sosai wajen yin hidima saꞌad da suke matasa kuma hakan ya sa Bulus ya ƙaunace su (Ka duba sakin layi na 3)b


KU BI MISALIN MARKUS TA YIN HIDIMA

4-5. Ta yaya Markus ya nuna cewa yana da niyyar yin hidima?

4 Wani littafin bincike ya ce, yin hidima yana nufin yin iya ƙoƙari wajen taimaka wa mutane, da kuma ci gaba da taimaka musu ko da yin hakan zai yi wuya. Abin da Markus ya yi ke nan. Lokacin da Bulus yake so ya je waꞌazi a ƙasar waje a ƙaro na biyu, bai yarda Markus ya bi su ba kuma mai yiwuwa hakan ya dami Markus. (A. M. 15:​37, 38) Amma hakan ya sa Markus ya daina yi wa ꞌyanꞌuwansa hidima ne? Aꞌa.

5 Markus ya bi Barnaba zuwa waꞌazi a wani wuri dabam. Wajen shekaru 11 bayan haka, lokacin da Bulus yake kurkuku a Roma, Markus yana cikin waɗanda suka taimaka masa. (Fil. 23, 24) Bulus ya ji daɗin taimakon da Markus ya yi masa har ya ce Markus ya “zama abin taꞌaziyya a gare” shi.—Kol. 4:​10, 11.

6. Ta yaya Markus ya amfana daga tarayyar da ya yi da ꞌyanꞌuwa da suka manyanta? (Ka duba ƙarin bayani.)

6 Markus ya amfana sosai domin ya yi tarayya da ꞌyanꞌuwa da sun manyanta. Bayan ya ɗan zauna da Bulus a Roma, sai ya je ya sami manzo Bitrus a Babila. Su biyun sun shaƙu sosai har Bitrus ya kira shi “ɗana Markus.” (1 Bit. 5:13) Mai yiwuwa da suke aiki tare, Bitrus ya gaya wa abokinsa Markus abubuwa da yawa game da rayuwar Yesu da kuma hidimarsa, kuma Markus ya rubuta labaran nan a littafin Markus.a

7. Ta yaya wani ɗanꞌuwa matashi mai suna Seung-Woo ya bi misalin Markus? (Ka kuma duba hoton.)

7 Markus ya ci gaba da bauta wa Jehobah kuma ya ƙulla abota da ꞌyanꞌuwan da suka manyanta. Ta yaya za ka bi misalin Markus? Wataƙila kana so ka zama bawa mai hidima ko dattijo, amma har ila hakan bai yiwu ba. Idan haka ne, kada ka gaji. A maimakon haka, ka nemi wasu hanyoyi da za ka yi wa Jehobah da ꞌyanꞌuwa hidima. Abin da Ɗanꞌuwa Seung-Woo wanda shi dattijo ne yanzu ya yi ke nan. A lokacin da yake matashi, yana gwada kansa da wasu matasa. Wasunsu sun sami damar yin hidima a ikilisiya kafin shi. Hakan ya sa Seung-Woo bai ji daɗi ba sam, kuma ya gaya wa dattawan yadda yake ji. Wani dattijo ya gaya masa cewa ya yi iya ƙoƙarinsa wajen yi wa ꞌyanꞌuwa hidima ko da mutane ba su lura da hakan ba. Seung-Woo ya bi shawarar kuma ya soma taimaka wa tsofaffi da waɗanda suke bukata a kai su taro. Game da abubuwan da suka faru a lokacin, Seung-Woo ya ce: “Na zo na fahimci ainihin abin da yi wa mutane hidima yake nufi. Na yi farin ciki sosai don na taimaka wa mutane.”

Wani ɗanꞌuwa matashi ya kawo wani ɗanꞌuwa da ya tsufa taro a mota.

Ta yaya matasa maza za su amfana idan suna yawan cuɗanya da ꞌyanꞌuwa maza da suka manyanta? (Ka duba sakin layi na 7)


KU BI MISALIN TIMOTI TA WAJEN ƘAUNAR MUTANE

8. Me ya sa Bulus ya zaɓi Timoti ya zama abokin tafiyarsa? (Filibiyawa 2:​19-22)

8 Bulus ya bukaci ꞌyanꞌuwa maza masu ƙarfin zuciya su bi shi zuwa biranen da aka tsananta masa. Ya soma da zaɓan wani ɗanꞌuwa da ya manyanta mai suna Sila. (A. M. 15:​22, 40) Daga baya ya zaɓi Timoti ma ya bi shi. Me ya sa Bulus ya zaɓi Timoti? Dalili na farko shi ne ꞌyanꞌuwa da suke wurin da Timoti yake sun faɗi abubuwa masu kyau game da shi. (A. M. 16:​1, 2) Ƙari ga haka, Timoti yana ƙaunar mutane sosai.—Karanta Filibiyawa 2:​19-22.

9. Ta yaya Timoti ya nuna cewa yana ƙaunar ꞌyanꞌuwa maza da mata?

9 Daga lokacin da Timoti ya soma hidima tare da Bulus, ya nuna cewa ya damu da mutane fiye da kansa. Hakan ya sa Bulus bai yi shakkar barin sa a Biriya ba domin ya ƙarfafa sabbin ꞌyanꞌuwa maza da mata da ke wurin. (A. M. 17:​13, 14) Babu shakka, Timoti ya koyi abubuwa da dama daga Sila da ke wurin a lokacin. Daga baya Bulus ya tura Timoti zuwa Tasalonika don ya ƙarfafa Kiristoci da ke wurin. (1 Tas. 3:2) A cikin shekaru 15 da ya yi yana hidima, Timoti ya ƙaunaci ꞌyanꞌuwa maza da mata. Kuma ya zama mai tausayi sosai har yakan “yi kuka tare da masu kuka.” (Rom. 12:15; 2 Tim. 1:4) Ta yaya matasa maza za su bi misalin Timoti?

10. Ta yaya wani ɗanꞌuwa mai suna Woo Jae ya koyi yadda zai ƙara ƙaunar mutane?

10 Wani ɗanꞌuwa mai suna Woo Jae ya koyi yadda zai ƙara ƙaunar ꞌyanꞌuwa. Lokacin da shi matashi ne, ba ya iya tattauna da ꞌyanꞌuwa maza da mata da suka tsufa. Don haka gaisuwa ne kawai yake haɗa su da shi a taro. Wani dattijo ya gaya masa cewa zai iya soma tattaunawa da ꞌyanꞌuwa ta wajen gaya musu abubuwan da yake so game da su. Kuma dattijon ya gaya masa cewa ya yi tunani game da abubuwan da mutumin yake so. Woo Jae ya bi shawarar da ɗanꞌuwan ya ba shi. A yau, Woo Jae dattijo ne. Kuma ya ce: “Yanzu yana min sauƙi in soma tattaunawa da mutane dabam-dabam. Ina iya fahimtar irin matsalolin da mutane suke fama da su. Hakan na sa ni farin ciki domin zan iya taimaka musu.”

11. Ta yaya ꞌyanꞌuwa matasa maza za su nuna cewa suna ƙaunar ꞌyanꞌuwa da ke ikilisiyarsu? (Ka kuma duba hoton.)

11 ꞌYanꞌuwa maza matasa, ku ma za ku iya koyan yadda za ku ƙara ƙaunar mutane. Idan kuka halarci taro, ku riƙa tattaunawa da dukan mutane, har da tsofaffi da yara. Ku tambaye su yadda suke, kuma ku saurare su. Yin hakan zai sa ku san yadda za ku taimaka musu. Mai yiwuwa ku ga cewa wasu maꞌaurata da suka tsufa suna bukatar taimako wajen yin amfani da manhajar JW Library®. Ko kuma cewa ba su yi shirin yin waꞌazi tare da wani ba. Za ku iya taimaka musu su san yadda za su yi amfani da naꞌurarsu da kyau ko kuma ku shirya fita waꞌazi da su. Idan kuna neman hanyoyin taimaka wa mutane, za ku zama misali mai kyau a ikilisiya.

Wani matashi da wani ɗanꞌuwa da ya tsufa suna waꞌazi gida-gida tare. Ɗanꞌuwan yana magana da wani mutum, matashin kuma yana nuna wa mutumin bidiyo a naꞌura.

Matasa maza za su iya taimaka wa ꞌyanꞌuwa a ikilisiya a hanyoyi dabam-dabam (Ka duba sakin layi na 11)


SHAWARAR BULUS ZAI TAIMAKA MAKA

12. Ta yaya matasa maza za su amfana daga shawarwari da Bulus ya ba wa Timoti?

12 Bulus ya ba wa Timoti shawarwari da za su taimaka masa ya bauta wa Jehobah da dukan zuciyarsa, kuma ya yi farin ciki a rayuwa. (1 Tim. 1:18; 2 Tim. 4:5) Idan kai matashi ne, shawarar da ya ba wa Timoti zai iya taimaka maka. Ta yaya? Ka karanta wasiƙu biyu da Bulus ya rubuta wa Timoti kamar kai ne aka rubuta wa, don ka ga shawarwarin da za su taimaka maka a rayuwa. Bari mu tattauna wasu daga cikinsu.

13. Me zai taimaka maka ka ci gaba da kusantar Jehobah?

13 Ka “horar da kanka cikin hali irin na Allah.” (1 Tim. 4:7b) Mene ne kasancewa da hali irin na Allah yake nufi? Hakan yana nufin mutum ya riƙe amincinsa ga Jehobah kuma ya riƙa yin abubuwan da za su sa Shi farin ciki. Tun da yake ba a haifan mu da wannan halin, muna bukatar mu yi iya ƙoƙarinmu don mu kasance da shi. Ta yaya za mu iya yin hakan? Ana yawan amfani da kalmar Helenanci da aka fassara zuwa “horar da kanka” wajen kwatanta irin horarwa da ƙwararrun ꞌyan wasa suke yi yayin da suke shirin yin wata gasa. ꞌYan wasan suna bukatar su guji duk wani abin da zai hana su cim ma burinsu. Mu ma muna bukatar mu mai da hankali sosai don mu zama da halayen da za su sa mu kusaci Jehobah.

14. Idan muna karanta Littafi Mai Tsarki, me ya kamata ya zama burinmu? Ka ba da misali.

14 Zai dace ka riƙa karanta Littafi Mai Tsarki kowace rana. Kuma yayin da kake hakan, ka tuna cewa burinka shi ne ka kusaci Jehobah. Alal misali, idan ka karanta labarin Yesu da wani saurayi mai arziki, me yake koya maka game da Jehobah? (Mar. 10:​17-22) Saurayin ya gaskata cewa Yesu ne Almasihu amma ya ƙi ya zama mabiyinsa. Duk da haka, Yesu ya ƙaunace shi. Kuma ya yi masa magana cikin alheri. Babu shakka, Yesu ya so mutumin ya ji daɗin bauta wa Jehobah. Kuma yadda Yesu ya bi da mutumin ya nuna irin ƙaunar da Jehobah ma yake masa. (Yoh. 14:9) Yayin da kake tunani a kan wannan labarin da kuma rayuwarka, ka tambayi kanka, ‘Me nake bukatar in yi don in ƙara kusantar Jehobah kuma in taimaka ma ꞌyanꞌuwa sosai?’

15. Me ya sa yake da muhimmanci ɗanꞌuwa matashi ya zama abin koyi ga sauran mutane? Ka ba da misali. (1 Timoti 4:​12, 13)

15 “Ka zama abin koyi ga sauran masu bi.” (Karanta 1 Timoti 4:​12, 13.) Bulus ya gaya wa Timoti ya koyi yadda zai yi karatu da koyarwa da kyau, amma ba shi ke nan ba. Bulus ya kuma gaya masa cewa ya zama mai ƙauna, da bangaskiya, da kuma tsabtar rai. Me ya sa? Domin halin mutum ya fi abin da yake faɗa muhimmanci. Alal misali, a ce an ba ka jawabi game da ƙara ƙwazo a waꞌazi. Zai yi maka sauƙi ka ba da jawabin idan kana yin iya ƙoƙarinka wajen yin waꞌazi. Kuma ꞌyanꞌuwa za su so su bi abin da ka ce idan kai da kanka ma kana yi.—1 Tim. 3:13.

16. (a) A waɗanne hanyoyi biyar ne ꞌyanꞌuwa matasa za su iya zama abin koyi? (b) Ta yaya ɗanꞌuwa matashi zai iya zama abin koyi “cikin magana”?

16 A 1 Timoti 4:​12, Bulus ya ambata hanyoyi biyar da ɗanꞌuwa matashi zai iya zama abin koyi ga sauran masu bi. Zai yi kyau ka ɗau lokaci don ka yi nazari a kan kowannensu. Alal misali, a ce kana so ka zama abin koyi “cikin magana.” Ka yi tunani a kan abubuwan da za ka iya faɗa don ka ƙarfafa mutane. Idan kana kan zama da iyayenka a gida, ka riƙa gode musu don abubuwan da suke maka. Bayan taro, ka gaya ma wani ɗanꞌuwa ko ꞌyarꞌuwa wani abu na musamman da ka ji daɗin sa a aikin da ta yi. Kuma ka iya ƙoƙarinka don ka ba da kalami a taro daga zuciyarka. Idan ka yi iya ƙoƙarinka don ka zama abin koyi cikin magana, mutane za su ga cewa kana samun ci gaba a bautarka ga Jehobah.—1 Tim. 4:15.

17. Me zai taimaka ma ɗanꞌuwa matashi ya ƙafa maƙasudai kuma ya cim ma maƙasudan? (2 Timoti 2:22)

17 “Ka guje wa mugayen shaꞌawace-shaꞌawace na matasa, ka sa kai ga neman adalci.” (Karanta 2 Timoti 2:22.) Bulus ya gaya wa Timoti ya guje ma duk wani abin da zai hana shi cim ma maƙasudansa, da abin da zai ɓata dangantakarsa da Jehobah. Kai ma za ka iya gani cewa wasu abubuwan da kake yi ba sa ba ka lokaci ka sa himma a bautarka ga Jehobah, duk da cewa ba abubuwa marasa kyau ba ne. Alal misali, ka yi tunani a kan yawan lokacin da kake amfani da shi wajen yin wasa, da yin amfani da intane da kuma buga wasannin bidiyo. Shin, za ka iya rage lokacin da kake yin abubuwan nan don ka iya yin ayyukan ibada? Za ka iya taimaka wajen kula da Majamiꞌar Mulkinku ko kuma ka fita yin waꞌazi da amalanke. Idan ka yi waɗannan abubuwan, za ka sami abokai da za su ƙarfafa ka ka ƙafa maƙasudai a bautarka ga Jehobah kuma za su taimaka maka ka cim ma maƙasudan.

ZA KA SAMI ALBARKU DA YAWA IDAN KA YI WA MUTANE HIDIMA

18. Waɗanne albarku ne Markus da Timoti suka samu?

18 Markus da Timoti sun yi canje-canje da yawa a rayuwarsu don su iya yi wa mutane hidima, hakan ya sa sun sami albarku da yawa kuma sun yi farin ciki sosai. (A. M. 20:35) Markus ya je wurare dabam-dabam a faɗin duniya don ya taimaka wa ꞌyanꞌuwa. Kuma ya rubuta labari mai daɗi game da rayuwar Yesu da hidimarsa. Timoti ya taimaka wa Bulus ya ƙafa ikilisiyoyi da kuma ƙarfafa ꞌyanꞌuwa. Babu shakka, Jehobah ya ga kome da Markus da Timoti suka yi don su bauta masa kuma hakan ya sa shi farin ciki sosai.

19. Me ya sa ya kamata matasa maza su bi shawarar da Bulus ya ba wa Timoti, kuma wane amfani ne za su samu idan suka yi hakan?

19 Wasiƙun da Bulus ya rubuta wa Timoti sun nuna cewa yana ƙaunar sa sosai. Amma Jehobah ne ya hure Bulus ya rubuta wasiƙun, don haka, abubuwan da ke ciki sun nuna cewa Jehobah yana ƙaunar matasa maza. Yana son matasa su yi farin ciki yayin da suke bauta masa. Don haka, ka bi shawarwarin da Bulus ya bayar, kuma ka yi niyyar yi ma ꞌyanꞌuwa hidima. Idan ka yi haka, za ka yi rayuwa mai inganci a yanzu kuma za ka “kafu cikin rai wanda shi ne ainihin rai” a nan gaba.—1 Tim. 6:​18, 19.

MECE CE AMSARKA?

  • Mene ne ka koya daga labarin Markus?

  • Ta yaya za ka yi koyi da Timoti wajen nuna cewa kana ƙaunar mutane?

  • Waɗanne shawarwari ne Bulus ya bayar da zai iya taimaka ma ɗanꞌuwa matashi ya faɗaɗa hidimarsa ga Jehobah?

WAƘA TA 80 ‘Mu Ɗanɗana, Mu Gani, Jehobah Nagari Ne’

a Bitrus mutum ne mai saurin bayyana yadda yake ji kuma hakan ya sa ya yi masa sauƙi ya gaya wa Markus irin tausayin da Yesu yake da shi, da abubuwan da ya faɗa da waɗanda ya yi. Shi ya sa a labarin da Markus ya rubuta game da Yesu, ya rubuta abubuwan da Yesu ya yi wa mutane domin ya tausaya musu.—Mar. 3:5; 7:34; 8:12.

b BAYANI A KAN HOTO: Markus yana taimaka wa Bulus da Barnaba lokacin da suka je waꞌazi a ƙasar waje. Timoti ya ziyarci wata ikilisiya don ya ƙarfafa ꞌyanꞌuwan.

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba