Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w14 6/15 pp. 8-11
  • Ta Yaya Za Ka Taimaki ’Yan’uwa da Aurensu Ya Mutu?

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Ta Yaya Za Ka Taimaki ’Yan’uwa da Aurensu Ya Mutu?
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2014
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • BAƘIN CIKI BAYAN MUTUWAR AURE
  • ƘOƘARIN DAWOWA HANKALINKA
  • IDAN KA KAƊAITA KUMA KA SOMA JIN CEWA AN YASAR DA KAI
  • Iyayena Suna Shirin Kashe Aure
    Tambayoyin Matasa
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2014
w14 6/15 pp. 8-11

Ta Yaya Za Ka Taimaki ’Yan’uwa da Aurensu Ya Mutu?

Wataƙila ka san wasu mutane da yawa da aurensu ya mutu. Dalilin hakan shi ne don kashe aure ya zama ruwan dare a duniya yau. Alal misali, wani bincike a ƙasar Poland ya nuna cewa yawancin ’yan shekara talatin da suka yi aure za su iya kashe aurensu bayan shekara uku zuwa shida, kuma ba su kaɗai ne ke kashe aure ba.

Wani rahoto na Institute for Family Policy (Hukumar Tafiyar da Al’amuran Iyali) a ƙasar Sifen ta ce, rabin waɗanda suke yin aure [a Turai] za su kashe aurensu. Haka ma yake a wasu ƙasashe masu tasowa.

BAƘIN CIKI BAYAN MUTUWAR AURE

Mene ne wannan mugun sakamako da ake samu a wurare da yawa ya ƙunsa? Wata da ta ƙware wajen ba da shawara game da aure a Gabashin Turai ta ce: “Kashe aure shi ne yake bayyana a fili abin da ya riga ya faru, wato taɓarɓarewar aure da kuma rabuwa. Kuma irin wannan yanayin yana sa baƙin ciki sosai. Abubuwan da suke bin bayan kashe aure sau da yawa su ne, fushi da nadama da taƙaici da fid da zuciya da kuma kunya.” A wasu lokatai, hakan yakan jawo tunanin kisan kai. Ta ƙara da cewa: “Sa’ad da kotu ya sanar cewa an kashe aure, salon rayuwa za ta canja. Da yake wanda aurensa ya mutu yana jin taƙaici da kaɗaici, zai iya yin irin wannan tunanin: ‘To, yanzu da aurena ya mutu, mene ne matsayina? Mene ne manufar rayuwata?’”

Wata mata mai suna Ewa ta furta yadda ta ji shekarun baya. Ta ce: “Sa’ad da aurenmu ya mutu, na ji kunya sosai don maƙwabtana da abokan aikina za su soma kirana ‘bazawara.’ Na yi fushi sosai. Na kasance uwa da uba da yake an ƙyale ni da yara biyu.”a Wani ɗan’uwa mai suna Adam da ya yi hidima a matsayin dattijo na shekaru sha biyu, ya ce: “Mutuncina ya zube kuma a wasu lokatai nakan ji haushi kuma har na soma guje wa mutane.”

ƘOƘARIN DAWOWA HANKALINKA

Saboda yawan tunani game da yadda rayuwarsu za ta kasance, wasu sun yi fama da tunani mara kyau, wato shekaru da yawa bayan aurensu ya mutu. Za su iya gani cewa mutane ba su damu da su ba. Ƙari ga haka, wani marubuci ya ce, yanzu za su “canja ɗabi’unsu kuma su soma magance matsalolinsu da kansu.”

Wani mutum mai suna Stanisław ya ce: “A lokacin da aurenmu ya mutu, matata ta dā ta hana ni ganin ’ya’yanmu mata biyu. Hakan ya sa na ji kamar babu wanda ya damu da ni kuma cewa Jehobah ma bai damu da ni ba. Ba na jin daɗin rayuwa kuma. Daga baya na gane cewa tunanin nan da na yi bai dace ba sam.” Wata mata mai suna Wanda da aurenta ya mutu ta damu da yadda rayuwarta zai kasance kuma ta ce: “Na ji cewa wataƙila bayan wani lokaci, mutane har da ’yan’uwa ma ba za su damu da ni da kuma yarana ba. Amma, ’yan’uwa ba su ƙyale mu ba, kullum suna taimakona wajen yin renon yaran don su zama bayin Jehobah.”

Waɗannan kalaman sun nuna cewa bayan kashe aure wasu suna yin tunanin da ba dace ba. Za su iya raina kansu ta wajen ganin cewa ba su da wani mutuncin da zai sa a kula da su. Ban da haka ma, za su iya sukar waɗanda suke tare da su. A sakamakon haka, za su soma tunani cewa ikilisiyarsu ba ta damu da su da kuma yadda suke ji ba. Duk da haka, labaran Stanisław da Wanda sun nuna cewa waɗanda aurensu ya mutu daga baya za su iya sanin cewa ’yan’uwa suna ƙaunarsu sosai. Hakika, ’yan’uwa Kiristoci suna kula da irin waɗannan mutanen ko da ba a iya ganin hakan da farko.

IDAN KA KAƊAITA KUMA KA SOMA JIN CEWA AN YASAR DA KAI

Zai dace mu riƙa tunawa cewa, duk da ƙoƙarin da muke yi don mu taimaka, waɗanda aurensu ya mutu za su riƙa jin kaɗaici a wasu lokatai. Zawarawa musamman za su ji cewa ba a ƙaunarsu sosai. Wata mata mai suna Alicja ta ce: “Aurenmu ya mutu shekara takwas yanzu. Duk da haka, a wasu lokatai nakan ji kamar ba ni da mutunci. Idan na yi irin wannan tunanin, sai in guji mutane kuma in riƙa kuka ina tausaya wa kaina.”

Ko da yake irin wannan yanayin ba sabon abu ba ne ga wanda aurensa ya mutu, Littafi Mai Tsarki ya ba da shawara cewa bai dace mu ware kanmu daga mutane ba. Ƙin bin wannan shawarar zai zama muna yin watsi da dukan “sahihiyar hikima.” (Mis. 18:1) Ya kamata wanda yake jin kaɗaici ya gane cewa hikima ce ya guji neman shawara daga wani da jinsinsu ba ɗaya ba. Ta hakan, ba za su samu kansu a cikin yanayi na kasancewa da sha’awa da wanda ba abokin aurensu ba.

Damuwa game da yadda rayuwarsu za ta kasance da kaɗaici da jin cewa an yasar da su za su iya sa ’yan’uwanmu da aurensu ya mutu baƙin ciki sosai. Ya kamata mu yi koyi da Jehobah ta wajen tallafa wa waɗannan ’yan’uwa da yake mun fahimci cewa irin wannan tunanin ya zama ruwan dare kuma yana kasancewa da wuya a shawo kansa. (Zab. 55:22; 1 Bit. 5:6, 7) Muna da tabbaci cewa za su yi farin ciki idan muka taimake su. Hakika, za su sami abokai na ƙwarai da yawa da za su taimaka musu a ikilisiya!—Mis. 17:17; 18:24.

a An canja wasu sunaye.

Yadda Za Ka Kasance da Ra’ayi Mai Kyau Idan Aurenka Ya Mutu

Bayin Jehobah suna ɗaukan aure da muhimmanci. Me ya sa? Domin muna bin shawarar Littafi Mai Tsarki. Alal misali, a littafin Malakai 2:16, Allah ya ce: “Ina jin ƙyamar kisan aure.” Hujja da Littafi Mai Tsarki ya bayar na kashe aure ita ce zina kawai. Saboda haka, ba zai dace mu nemi kashe aurenmu don wani dalili dabam kuma mu yi shiri mu auri wani ko wata ba.—Far. 2:22-24; K. Sha 5:21; Mat. 19:4-6, 9.

Idan aure ya mutu, wato idan ɗaya daga cikin ma’auratan ya ci amana, ’yan’uwa da ke ikilisiya za su iya taimaka mana. Suna koyi da Jehobah ta wajen yin iya ƙoƙarinsu don su taimaka wa adalai “masu-karyayyar zuciya.”—Zab. 34:15, 18; Isha. 41:10.

YADDA ZA KA IYA TAIMAKA?

Shin za ka iya ba da taimako da ake bukata ruwa a jallo? Mene ne za ka iya yi don ka taimaka wa wanda yake fuskantar irin yanayin da aka ambata ɗazun? Ka yi la’akari da abin da Littafi Mai Tsarki ya ce da kuma yadda amintattun Kiristoci suka ba da taimako.

Ka saurara da kyau. (Mis. 16:20, 23)

Ya kamata mu fahimta cewa bayan mutuwar aure, wanda abin ya shafa ba zai so ya bayyana dukan abin ya jawo kisan auren ba. Zai iya kasancewa a cikin halin taƙaici kuma ya furta wani abin da bai dace ba kuma daga baya ya yi da-na-sani. (Mis. 12:25; Rom. 12:15) Michał wanda ya taimaka wa Adam da aka ambata ɗazun, ya ce mutum zai iya kasancewa mai tausayi ba tare da ya san dukan abin da ya faru ba: “Na yi ƙoƙarin taimaka wa Adam ya gane cewa sa’ad da yake baƙin ciki, zai iya gaya min wani abin da bai so ba.” Saboda da haka, Michał ya bayyana masa cewa ba ya bukatar ya san dukan abin da ya faru. Duk da haka, ya saurara da kyau. Za mu iya nuna alheri kafin ko kuma bayan taron Kirista idan muka yi tambaya kamar: “Yaya ake ji da haƙuri? Na san kana baƙin ciki. Allah ya sawwaƙe.”

Ka nuna cewa ka damu. (Filib. 2:4)

Mirosław ya ce: “Ni da matata mun shirya don mu taimaka wa wata ’yar’uwa bazawara. Alal misali, mun gyara mata makullin wani ƙofar gidanta. Ƙari ga haka, mun kai ta ganin likita.” Waɗannan abubuwan kamar ba su da muhimmanci; amma sun taimaka mata sosai. ’Yar’uwa da ma’auratan nan suka taimaka ta dawo cikin hankalinta da shigewar lokaci. Daga baya, ta soma hidimar majagaba kuma ’yarta mai shekara 11 ta yi baftisma.

Ka tabbatar wa wanda aurensa ya mutu cewa Jehobah ba ya farin ciki don yanayinsa.

Idan yana gani ba shi da muhimmanci a idon kowa, za ka iya tabbatar masa cewa Jehobah yana ƙaunar kowane bawansa. Babu shakka, mun “fi gwarare masu-yawa daraja.” Muna da muhimmanci da kuma daraja a gaban Allah. (Mat. 10:29-31) “Ubangiji yana auna zukata” kuma ya san yanayin waɗanda aurensu ya mutu. Ba zai ƙyale bayinsa masu aminci ba. (Mis. 17:3; Zab. 145:18; Ibran. 13:5) Yayin da kake kula da shi, ka nuna masa cewa Allah yana son sa saboda yadda yake ƙaunar gaskiya da kuma ƙoƙarce-ƙoƙarcensa na bauta masa da aminci.—Filib. 2:29.

Ka ƙarfafa wanda aurensa ya mutu ya riƙa halartan taron ikilisiya a kai a kai.

Halartan taron yakan yi wa wasu wuya sa’ad da suke fama da baƙin ciki. Amma muna samun ƙarfafa da kuma “ingantawa” idan muka halarci taro. (1 Kor. 14:26, Littafi Mai Tsarki; Zab. 122:1) Saboda da haka, matakin da dattawa suka ɗaukawa don su taimaka yana da amfani sosai. ’Yar’uwa mai suna Wanda da aka ambata ɗazu, ta ce, “Ba mu manta da yadda suka kula da mu ba.”

Ka taimaka wa wanda aurensa ya mutu ya ƙarfafa dangantakarsa da Allah ta wajen yin addu’a da nazarin Littafi Mai Tsarki da kuma bimbini. (Yaƙ. 4:8)

Ko da yake Jehobah shi ne mai iko duka kuma yana sama, ya damu da ‘wanda shi ke talaka mai-karyayyen ruhu, wanda yake rawan jiki da maganarsa.’—Isha. 66:2.

Ka ba da lokacinka don ku fita wa’azi tare ko kuma ku shirya taro tare.

Hakan zai taimakawa wanda aurensa ya mutu ya kasance da gaba gaɗi yayin da yake sake samun hankalinsa. Wata mai suna Marta ta taimaka wa wata ’yar’uwa mai himma da take baƙin ciki bayan aurenta ya mutu, kuma ta ce: “Muna fita wa’azi tare a kai a kai. Muna kafa maƙasudi kuma idan muka cim ma maƙasudinmu, muna farin ciki. A wani lokaci, mukan shirya abubuwan da za a tattauna a taro tare, kuma mu dafa wani abinci mai daɗi mu ci tare.”

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba