Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w14 6/15 p. 7
  • Amsoshin Tambayoyin Masu Karatu

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Amsoshin Tambayoyin Masu Karatu
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2014
  • Makamantan Littattafai
  • Begen Tashin Matattu Yana Da iko
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2000
  • Ta Yaya Za A Ta da Matattu?
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2020
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2014
w14 6/15 p. 7

AMSOSHIN TAMBAYOYIN MASU KARATU

Shin Ya dace Kiristoci su ƙona gawa a lokacin jana’iza?

Littafi Mai Tsarki bai haramta al’adar ƙona gawa ba.

Littafi Mai Tsarki yana ɗauke da wasu labarai game da ƙona gawawwaki da kuma ƙasusuwan mutanen da suka mutu. (Josh. 7:25; 2 Laba. 34:4, 5) Wataƙila hakan ya nuna cewa waɗannan mutane ba su cancanci jana’izar da ta dace ba. Amma ba dukan ƙona gawawwaki ba ne ke da wannan ma’anar ba.

Za mu iya gane hakan daga mutuwar Sarki Saul da ’ya’yansa uku. Dukan su huɗu sun mutu ne sa’ad da suke yaƙi da Filistiyawa. Ɗaya daga cikin ’ya’yan Saul aminin Dauda ne. Sa’ad da jaruman Isra’ilawa da ke zama da Jabesh-gilead suka ji abin da ya faru, sai suka ɗauki gawawwakin Saul da ’ya’yansa suka ƙona su. Bayan haka, suka binne ƙasusuwansu. Dauda ya yaba wa waɗannan Isra’ilawa don wannan matakin da suka ɗauka.—1 Sam. 31:2, 8-13; 2 Sam. 2:4-6.

Littafi Mai Tsarki ya ce za a yi tashin matattu, wato Allah zai sake rayar da mutumin da ya mutu. Mun gaskata cewa, Allah zai iya sake ta da mutum da ya mutu kuma ya ba shi sabon jiki ko da an ƙona gawarsa ko a’a. Yahudawa uku masu aminci da Sarki Nebuchadnezzar ya yi musu hukuncin mutuwa ba su ji tsoro cewa idan jikinsu ya ƙone sakamakon wannan hukuncin, Allah ba zai ta da su ba. (Dan. 3:16-18) Hakan yake da bayin Jehobah masu aminci da aka ƙone gawawwakinsu a sansanin Nazi. Bayin Allah masu aminci dabam-dabam sun halaka sa’ad da aka yi fashe-fashe kamar na bam da kuma a wasu hanyoyi dabam-dabam kuma saboda haka, ba a ga gawawwakinsu ba. Duk da haka, muna da tabbaci cewa za a ta da su.—R. Yoh. 20:13.

Jehobah ba ya bukata ya harhaɗa gangar jikin da mutum ya yi rayuwa da shi a dā kafin ya ta da shi. Mun san hakan ta yadda Allah yake ta da Kiristoci shafaffu zuwa sama. Kamar Yesu da aka “rayar da shi cikin ruhu,” ana ta da Kiristoci shafaffu da jiki na ruhu. Ba sa zuwa sama da wani sashe na jikinsu na dā.—1 Bit. 3:18; 1 Kor. 15:42-53; 1 Yoh. 3:2.

Mun gaskata cewa Allah zai ta da mutumin da ya mutu ko da an ƙona jikinsa ko a’a don mun yi imani cewa Allah zai cika alkawuransa. (A. M. 24:15) Ko da yake ba mu san dalla-dalla yadda Jehobah ya ta da waɗanda suka mutu a dā ba da kuma yadda zai yi hakan a nan gaba ba. Duk da haka, mun ba da gaskiya ga Jehobah. Ya tanadar da takamaiman ‘shaida’ ta wajen ta da Yesu.—A. M. 17:31; Luk 24:2, 3.

Ya kamata Kiristoci su yi la’akari da al’adu da ra’ayoyin mutane a yankinsu da kuma dokoki da suka shafi jana’iza. (2 Kor. 6:3, 4) Saboda haka, iyali ko mutumi ne da kansa zai tsai da shawara ko a ƙone gawa a lokacin jana’iza ko a’a.

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba