Yadda Za Mu Iya Ratsa Zukatan Danginmu da Ba Shaidu Ba
YESU KRISTI ya ce: “Tafi gida wurin ’yan’uwanka, ka faɗa musu irin . . . abubuwan da Ubangiji ya yi maka, da kuma yadda ya ji tausayinka.” A kusa da wani gari da ake kira Gadara da ke kudu maso gabashin Kogin Galili ne Yesu ya furta waɗannan kalmomin ga wani mutum da ke so ya zama mabiyinsa. Yesu ya nuna cewa ya fahimci wani abu game da ’yan Adam, wato suna marmarin gaya wa danginsu abubuwan da za su amfane su.—Mar. 5:19, Littafi Mai Tsarki.
Mutane da yawa suna nuna irin wannan halin a yau. Ana yin hakan a wasu al’adun fiye da wasu. Saboda haka, sa’ad da mutum ya soma bauta wa Jehobah, Allah na gaskiya, zai so ya gaya wa ’yan’uwansa game da sabon imaninsa. Amma ta yaya zai yi hakan? Ta yaya zai iya rinjayar ’yan’uwansa da imaninsu ba ɗaya ba ne? Littafi Mai Tsarki ya ba mu tabbatacciyar shawara.
“MUN SAMI ALMASIHUN”
A ƙarni na farko, Andarawus yana ɗaya daga cikin waɗanda suka fara gane cewa Yesu ne Almasihu. Shin wane ne ya fara gaya wa abin da ya gani? “Shi [Andarawus] ya fara samun ɗan’uwansa Siman, ya ce masa, Mun sami Almasihu (wato Kristi ke nan).” Sai ya kawo shi wurin Yesu, kuma hakan ya ba wa Bitrus damar zama mabiyin Yesu.—Yoh. 1:35-42.
Kusan shekaru shida bayan wannan, sa’ad da Bitrus yake Yafa, sai aka gaya masa ya tafi arewacin Kaisariya zuwa gidan Karniliyus, wani shugaban sojoji. Su wane ne Bitrus ya tarar a gidan? “Karniliyus kuwa yana nan yana jiransu, [Bitrus da abokan tafiyarsa], ya rigaya ya tattara danginsa da aminansa.” Da haka, Karniliyus ya ba wa ’yan’uwansa dama su saurari Bitrus yayin da yake magana kuma su yanke shawara bisa ga abubuwan da suka ji.—A. M. 10:22-33.
Wane darasi ne za mu koya daga yadda Andarawus da Karniliyus suka bi da ’yan’uwansu?
Andarawus da Karniliyus sun ɗauki al’amarin da muhimmanci. Andarawus ya kawo Bitrus ga Yesu, kuma Karniliyus ya shirya domin ’yan’uwansa su saurari abubuwan da Bitrus zai faɗa. Amma, Andarawus da Karniliyus ba su matsa wa ’yan’uwansu su zama mabiyan Yesu ba. Wane darasi ne za mu iya koya? Ya kamata mu bi misalinsu. Za mu iya tattauna wasu abubuwa da muka sani da danginmu. Ta hakan, za mu ba su damar koyan gaskiya da kuma sanin ’yan’uwanmu masu bi. Duk da haka, ya kamata mu daraja ra’ayinsu kuma mu guji matsa musu. Bari mu yi la’akari da misalin Jürgen da Petra, wasu ma’aurata da ke zama a ƙasar Jamus, hakan zai sa mu san yadda za mu iya taimaka wa danginmu su san gaskiya.
Petra ta yi nazarin Littafi Mai Tsarki da Shaidun Jehobah kuma daga baya ta yi baftisma. Mijinta Jürgen, hafsan soja ne. Da farko, bai ji daɗi cewa matarsa ta zama Mashaidiya ba. Amma da shigewar lokaci, ya fahimci cewa Shaidun suna koyar da gaskiyar da ke cikin Littafi Mai Tsarki. Kuma daga baya, shi ma ya yi baftisma kuma yanzu shi dattijo ne a ikilisiyarsu. Wace shawara ce ya bayar game da yadda za mu iya ratsa zukatan danginmu da ba Shaidu ba?
Jürgen ya ce: “Kada mu matsa musu kuma mu riƙa musu ruwan bayani game da batun addini. Hakan zai sa su daɗa ƙi da saƙonmu. Maimakon haka, mu riƙa tattaunawa da su cikin basira kuma mu yi hakan a duk lokacin da ya dace. Zai dace mu gabatar da su ga ’yan’uwa da tsaransu ne a cikin ikilisiyarmu, waɗanda suke da sha’awa iri ɗaya da su. Yin haka zai iya taimaka musu.”
Manzo Bitrus da dangin Karniliyus sun amince da saƙon Littafi Mai Tsarki nan da nan. Akasin haka, wasu mutane a ƙarni na farko da aka yi musu wa’azi ba su zama Kiristoci nan da nan ba.
’YAN’UWAN YESU KUMA FA?
A lokacin da Yesu yake hidima a duniya, wasu cikin ’yan’uwansa sun yi imani da shi. Alal misali, wataƙila manzo Yaƙub da Yohanna ’ya’yan kawun Yesu ne, kuma mahaifiyarsu Salome innar Yesu ce. Wataƙila tana ɗaya daga cikin “waɗansu da yawa, waɗanda suke yi musu [Yesu da manzanninsa] hidima daga cikin dukiyarsu.”—Luk 8:1-3.
Duk da haka, wasu ’yan’uwan Yesu ba su ba da gaskiya gare shi nan da nan ba. Alal misali, a wani lokaci fiye da shekara ɗaya bayan baftismar Yesu, mutane da yawa sun taru a wani gida domin su saurare shi. Amma sa’ad da “’yan’uwansa suka ji haka, sai suka fita su kamo shi, saboda sun ce, ‘Ai, ya ruɗe.’” Bayan haka, ’yan’uwansa sun sake tattauna game da shirinsa na yin tafiya, amma bai ba su amsa kai tsaye ba. Me ya sa? Domin “dā ma ’yan’uwansa ba su gaskata da shi ba.”—Mar. 3:21; Yoh. 7:5, LMT.
Wane darasi ne za mu iya koya daga yadda Yesu ya bi da ’yan’uwansa? Yesu bai ji haushi ba sa’ad da wasu cikinsu suka ce ya ruɗe. Ko bayan mutuwarsa da tashinsa daga mutuwa, ya sake ƙarfafa su ta wurin bayyana ga ɗan’uwansa Yaƙub. Mai yiwuwa, hakan ya tabbatar wa Yaƙub da sauran ’yan’uwansa cewa Yesu ne Almasihu. Haka ne ya sa suka kasance tare da manzannin da sauran ’yan’uwa a cikin wani gidan bene a Urushalima sa’ad da ruhu mai tsarki ya sauko musu. Ba da daɗewa ba, Yaƙub da Yahuda da wasu kuma cikin ’yan’uwan Yesu sun more gatan yin hidima.—A. M. 1:12-14; 2:1-4; 1 Kor. 15:7.
WASU SUNA BUKATAR LOKACI SOSAI
Kamar yadda yake a ƙarni na farko, wasu danginmu ma a yau suna iya ɗaukan lokaci sosai kafin su soma bauta wa Jehobah. Alal misali, Roswitha ’yar Katolika ce sa’ad da mijinta ya yi baftisma a matsayin Mashaidin Jehobah a shekara ta 1978. Da farko, Roswitha ta yi adawa da mijinta, da yake tana ganin abubuwan da ta yi imani da su gaskiya ne. Amma bayan shekaru da dama, ta daina hakan domin ta gane cewa Shaidun suna koyar da gaskiya. A shekara ta 2003, ita ma aka yi mata baftisma. Mene ne ya taimaka mata ta yi canji? Maimakon mijinta ya yi fushi domin adawar da take yi da shi, bai matsa mata ta canja ra’ayinta ba. Wace shawara ce ta bayar? Ta ce, “Mai haƙuri yakan dafa dutse har ma ya sha romonsa.”
Monika ta yi baftisma a shekara ta 1974, kuma shekaru goma bayan haka, ’ya’yanta biyu maza su ma sun yi baftisma. Ko da yake mijinta Hans bai tsananta mata don imaninta ba, amma bai yi baftisma ba har sai a shekara ta 2006. Wace shawara ce iyalin ta bayar bayan ta waiwayi baya? “Ka manne wa Jehobah, kuma kada ka bar wani abu ya hana ka riƙe imaninka.” Babu shakka, yadda suka ci gaba da tabbatar wa Hans cewa suna ƙaunarsa ya taimaka sosai kuma ba su fid da rai a kansa ba.
KU SA SU JI DAƊIN KOYARWAR GASKIYA
Yesu ya kwatanta koyarwar gaskiya da ruwa da ke ba da rai na har abada. (Yoh. 4:13, 14) Muna so danginmu su sami wartsakewa ta wajen shan wannan ruwa mai tsabta, wato koyarwar gaskiya. Hakika, bai kamata mu ba su wannan ruwan da yawa kuma a take ba, don hakan zai shaƙe su. Yadda muka bayyana musu imaninmu zai nuna ko wannan ruwan zai wartsake su ko kuma ya shaƙe su. Littafi Mai Tsarki ya ce “zuciyar mai adalci ta kan yi tunanin abin da za ta amsa” kuma “zuciyar mai hikima tana koya wa bakinsa, tana kuwa ƙara wa leɓunansa sani.” Ta yaya za mu iya bin wannan shawarar?—Mis. 15:28; 16:23.
Yana yiwuwa cewa mace za ta so ta bayyana wa mijinta imaninta. Idan ta yi “tunanin amsar da za ta bayar,” za ta yi magana da kyau kuma ba da garaje ba. Kada ta nuna cewa ita mai adalci ce fiye da shi ko ta fi shi fifiko. Furucinta mai kyau zai iya kwantar da hankalin mijinta kuma ya kawo salama a cikin gida. Wane lokaci ne mijinta zai fi sauraronta? Waɗanne abubuwa ne yake jin daɗin karantawa ko kuma yin taɗi game da su? Yana sha’awar kimiyya, siyasa ko kuma wasanni? Ta yaya za ta sa ya yi marmarin sanin koyarwar Littafi Mai Tsarki ba tare da rena shi ko ra’ayinsa ba? Yin irin wannan tunanin zai taimaka mata ta yi magana da basira kuma ta ɗauki matakin da ya dace.
Ba bayyana wa danginmu abin da muka gaskata a hankali ne kawai zai taimaka musu ba. Ya kamata mu riƙa nuna halaye masu kyau.
HALI MAI KYAU
Jürgen, wanda aka ambata ɗazu ya bayyana cewa: “Ka ci gaba da bin mizanan Littafi Mai Tsarki a rayuwarka ta yau da kullum. Wannan hanya ce mai kyau ta sa danginmu da ba masu bi ba su lura da halayenmu masu kyau, ko da yake ba za su yarda cewa suna hakan ba. Ga abin da Hans wanda ya yi baftisma shekaru 30 bayan matarsa, ya faɗa da ya nuna cewa shi ma ya yarda da hakan: “Yana da kyau mu kasance da halin Kirista, domin hakan zai sa danginmu su ga tabbaci cewa muna bin gaskiya.” Ya kamata danginmu su ga cewa imaninmu ya sa salon rayuwarmu ya bambanta a hanya mai kyau.
Manzo Bitrus ya ba da shawara mai kyau ga mata waɗanda mazajensu ba masu bi ba ne. Ya ce: “Ku yi zaman biyayya ga mazaje naku, domin ko da akwai waɗansu da ba su yin biyayya da magana, su rinjayu ban da magana; saboda halayen matansu; suna lura da halayenku masu tsabta tare da tsoro. Kada adonku ya zama ado na waje, wato su kitson gashi, da sa ado na zinariya ko yafa tufafi masu ƙawa, amma ya zama ɓoyayyen mutum na zuciya, cikin tufafi waɗanda ba su lalacewa na ruhu mai ladabi mai lafiya, abin da ke mai tamani mai girma a gaban Allah.”—1 Bit. 3:1-4.
Manzo Bitrus ya ce yana yiwuwa mace ta rinjayi mijinta ta wajen halayenta masu kyau. Wata ’yar’uwa mai suna Christa ta bi wannan ƙa’idar don ta rinjayi maigidanta da halinta mai kyau tun da ta yi baftisma a shekara ta 1972. Ko da yake mijinta ya taɓa yin nazari da Shaidu, amma bai amince da gaskiya ba. Ya halarci taron Kirista kuma ya yi cuɗanya da ’yan’uwa da ke ikilisiyar. ’Yan’uwan kuma sun ba shi damar yin zaɓi. Ta yaya Christa ta yi ƙoƙarin ratsa zuciyarsa?
Ta ce: “Na ƙuduri niyyar yin abin da Jehobah yake so, kuma na yi ƙoƙari in rinjaye mijina ba tare da ‘magana’ ba, amma ta halayena masu kyau. A duk lokacin da ya bukaci in yi wani abu da bai taka dokar Allah ba, ina iyakacin ƙoƙarina in yi biyayya da shi. Ina daraja ra’ayinsa, sa’an nan in bar kome a hannun Jehobah.”
Misalin Christa ya nuna muhimmancin kasancewa a shirye mu yi canji bisa ga yanayin da muke ciki. Ta ci gaba da yin abubuwan da za su ƙarfafa dangantakarta da Jehobah, kamar su halartan taro a kai a kai da kuma yin wa’azi. Har ila ta fahimci cewa hakkinta ne ta kula da mijinta kuma ta ƙaunace shi. Kasancewa da sauƙin hali da kuma fahimi yana da muhimmanci ga duk wanda yake sha’ani da dangin da ba Mashaidi ba ne. Littafi Mai Tsarki ya bayyana cewa “akwai lokaci kuma domin kowane abu.” Hakan yana nufin mutum ya nemi lokaci don kasance tare da iyalinsa, musamman ma aboki ko abokiyar aurensa da ba Mashaidiya ba ce. Kasancewa tare zai taimaka mana mu riƙa sadawa da kyau. Tarihi ya nuna cewa idan iyalai suna tattaunawa da juna sosai, hakan zai taimaka don kada su riƙa jin kaɗaici ko kuma kishi.—M. Wa. 3:1.
KADA KA FID DA RAI
Holger, wanda mahaifinsa ya yi baftisma shekaru 20 bayan sauran mambobin iyalin sun yi hakan ya ce: “Yana da muhimmanci mu nuna wa danginmu da ba ya bauta wa Jehobah cewa muna ƙaunarsa kuma muna masa addu’a. Christa ta daɗa da cewa, ‘ba za ta taɓa fid da rai ba, tana da bege cewa mijinta zai zo ga sanin Jehobah kuma ya soma bauta masa.’ Ya kamata mu ci gaba da nuna halaye masu kyau ga danginmu da ba sa bauta wa Jehobah, kuma mu riƙa sa rai cewa za su canja.
Maƙasudinmu shi ne mu kiyaye dangantakarmu da su, mu ba su damar sanin gaskiya kuma mu ratsa zukatansu da saƙon Littafi Mai Tsarki. Zai dace mu kasance da “ladabi da tsoro [ban-girma]” a dukan tafarkinmu.—1 Bit. 3:15.