Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w14 2/15 pp. 3-7
  • Ka Yabi Kristi​—⁠Sarki Mai Ɗaukaka!

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Ka Yabi Kristi​—⁠Sarki Mai Ɗaukaka!
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2014
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • “ZUCIYATA TANA MALALA DA WANI NAGARIN AL’AMARI”
  • MAGANAR ALHERI SUNA FITOWA DAGA LEƁUNAN SARKI
  • AN ƊAUKAKA SARKIN FIYE DA ‘TSARARAKINSA’
  • SARKIN YA ‘RATAYE TAKOBINSA’
  • SARKIN YANA KĀRE GASKIYA
  • SARKIN YANA YIN ‘AL’AMURA MASU BAN RAZANA’
  • SARKIN YANA CIN NASARA
  • Shugabanmu Mai Ƙwazo A yau
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2010
  • Mulkin “da ba Za a Rushe Shi ba Daɗai”
    Ka Bauta wa Allah Maƙadaici na Gaskiya
  • Menene Mulkin Allah?
    Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa?
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2014
w14 2/15 pp. 3-7

Ka Yabi Kristi, Sarki Mai Ɗaukaka!

“Ka yi hawan ɗaukaka zuwa nasara.”—ZAB. 45:4.

MUHIMMAN DARUSSA

  • A waɗanne hanyoyi ne Allah ya shafe Yesu fiye da ‘tsararakinsa’?

  • Yaushe ne Kristi ya rataye takobinsa, ta yaya ya yi amfani da shi da farko kuma a yaushe ne zai sake amfani da shi?

  • Wace muhimmiyar gaskiya ce Sarki Yesu zai kāre?

1, 2. Me ya sa Zabura ta 45 take da muhimmanci a gare mu?

SARKI mai ɗaukaka ya yi sukuwa garin kāre gaskiya da kuma adalci kuma ya ci nasara bisa magabatansa. Bayan ya kammala cin nasarar, sai ya auri kyakkyawar mace. Za a riƙa tuna da kuma ɗaukaka wannan Sarkin har abada. Waɗannan ne wasu cikin abubuwan da aka kwatanta a littafin Zabura ta 45.

2 Zabura ta 45 tana ɗauke da labari mai daɗi kuma abubuwan da aka ambata a ciki suna da muhimmanci sosai a gare mu. Sun shafi rayuwarmu yanzu da kuma a nan gaba. Bari mu mai da hankali sosai yayin da muke bincika wannan zaburar.

“ZUCIYATA TANA MALALA DA WANI NAGARIN AL’AMARI”

3, 4. (a) Mene ne “wani nagarin al’amari” da marubucin zabura ya yi magana a kai, kuma ta yaya ya shafe mu? (b) Wane saƙo game da wani “sarki ne” muke wa’azinsa, kuma ta yaya harshenmu ya zama kamar alƙalami?

3 Karanta Zabura 45:1. “Wani nagarin al’amari” da ya sa zuciyar marubucin zabura ta yi “malala” ya shafi wani sarki ne. Asali a Ibrananci wannan kalmar “malala” tana nufin “tafasa,” wato yadda ruwa ke tafasa. Marubucin zabura ya yi farin ciki sosai sa’ad da ya ji wannan labarin, sai ya ji kamar zuciyarsa tana tafasa kuma harshensa ya yi kama da ‘alƙalami na gwanin marubuci.’

4 Ta yaya hakan ya shafe mu? Albishiri game da Mulkin Almasihu shi ne wani nagarin al’amari da ke ratsa zuciyarmu. Saƙon Mulkin ya zama “nagarin” abu a shekara ta 1914. Tun daga lokacin, wannan saƙon ba game da wani Mulki da za a kafa a nan gaba ba ne, amma game da gwamnati ce da ke sarauta yanzu a sama. Wannan ne “bishara kuwa ta Mulki” da muke yaɗawa a “cikin iyakar duniya domin shaida ga dukan al’ummai.” (Mat. 24:14) Shin saƙon Mulkin tana sa zuciyarmu ta yi “malala”? Muna yin wa’azin Mulkin da himma kuwa? Kamar marubucin zabura, waƙar da muke yi game da “sarki ne,” wato Sarki Yesu Kristi. Muna sanar wa mutane cewa Yesu ne Sarkin Mulkin Allah a sama. Saboda haka, muna gayyatar kowa, har da sarakunan wannan duniyar, su ba da kai ga Sarautar Yesu. (Zab. 2:1, 2, 4-12) Kuma harshenmu yana kama da ‘alƙalamin ƙwararen marubuci’ don muna amfani da Littafi Mai Tsarki wajen yin wa’azi.

Muna sanar da albishiri game da Sarkinmu, Yesu Kristi

MAGANAR ALHERI SUNA FITOWA DAGA LEƁUNAN SARKI

5. (a) Me ya sa Yesu ya yi kyaun gaske? (b) Ta yaya Yesu ya yi wa’azi da ke ratsa zuciya, kuma yaya za mu bi misalinsa?

5 Karanta Zabura 45:2. Nassosi ba su bayyana sifar Yesu dalla-dalla ba. Da yake kamili ne, babu shakka, shi ‘kyakkyawan’ mutum ne. Amma abin da ya sa yake da kyaun gaske shi ne amincinsa ga Jehobah. Ƙari ga haka, Yesu ya yi wa’azi game da Mulkin Allah kuma ya yi hakan da kalamai masu ratsa zuciya. (Luk 4:22; Yoh. 7:46) Shin muna yin iya ƙoƙarinmu wajen yin koyi da Yesu a wa’azin da muke yi kuwa?—Kol. 4:6.

6. Ta yaya Allah ya albarkaci Yesu har abada?

6 Jehobah ya albarkaci hidimar da Yesu ya yi a duniya kuma ya ba shi lada a sakamakon sadaukar da ransa da ya yi. Me ya sa Jehobah ya yi hakan? Domin Yesu ya ƙaunaci Allah kuma ya kasance da aminci a gare shi. Manzo Bulus ya ce: “Da aka iske shi [Yesu] cikin kamanin mutum, ya ƙasƙantar da kansa, ya zama yana biyayya har da mutuwa.” Bulus ya ci gaba da cewa: “Domin wannan Allah kuma ya ba shi mafificiyar ɗaukaka, ya ba shi suna wanda ke bisa kowane suna; domin cikin sunan Yesu kowace gwiwa ta rusuna, ta cikin sama da ta kan duniya da ta ƙarƙashin duniya, kowane harshe kuma shi shaida Yesu Kristi Ubangiji ne, zuwa darajar Allah Uba.” (Filib. 2:8-11) Jehobah ya albarkaci Yesu “har abada” ta wajen ta da shi daga mutuwa kuma ya ba shi rai marar mutuwa.—Rom. 6:9.

AN ƊAUKAKA SARKIN FIYE DA ‘TSARARAKINSA’

7. A waɗanne hanyoyi ne Allah ya shafe Yesu fiye da ‘tsararakinsa’?

7 Karanta Zabura 45:6, 7. Domin Yesu yana son nagarta kuma ya tsane duk abin da zai ɓata sunan Ubansa, shi ya sa Jehobah ya naɗa shi Sarkin Mulkinsa. An shafe Yesu da “mān farin ciki” fiye da ‘tsararakinsa,’ wato sarakunan da suka fito daga zuriyar Dauda. Ta yaya? Na ɗaya, Jehobah ne da kansa ya shafe Yesu. Na biyu kuma, Jehobah ya shafe shi a matsayin Sarki da kuma Babban Firist. (Zab. 2:2; Ibran. 5:5, 6) Ƙari ga haka, an shafe Yesu da ruhu mai tsarki kuma sarautarsa ba ta duniya ba ce amma ta sama ce.

8. Me ya sa muke da tabbaci cewa Yesu zai yi sarauta cikin adalci, kuma mene ne furucin nan ‘Allah ne kursiyinka’ yake nufi?

8 Jehobah ya naɗa Ɗansa a matsayin Sarki a sama a shekara ta 1914. ‘Sandan adalci kuma shi ne sanda mulkinsa,’ saboda haka, muna da tabbaci cewa zai yi sarauta cikin adalci. Yana da ikon zama Sarki, domin Allah ne kursiyinsa, wato Jehobah ne ya naɗa shi Sarki. Sarautar Yesu zai dawwama “har abada abadin.” Babu shakka, muna murnar bauta wa Jehobah a ƙarƙashin Sarkin da ya naɗa!

SARKIN YA ‘RATAYE TAKOBINSA’

9, 10. (a) Yaushe ne Kristi ya rataye takobinsa, kuma ta yaya ya yi amfani da shi? (b) Ta yaya Yesu zai yi amfani da takobinsa a nan gaba?

9 Karanta Zabura 45:3. Jehobah ya umurci Sarkin da ya naɗa ya ‘rataye takobinsa.’ Ta hakan, yana ba Yesu izinin yaƙan dukan waɗanda suke gāba da sarautar Allah kuma ya halaka su. (Zab. 110:2) An kwatanta Kristi a matsayin “mai-iko” don shi Sarki ne da kuma Mayaƙi da ba za a iya cin sa a yaƙi ba. Ya soma rataye takobinsa a shekara ta 1914 sa’ad da ya ci nasara a kan Shaiɗan da aljanunsa kuma ya jefo su duniya.—R. Yoh. 12:7-9.

10 Wannan shi ne nasara na farko da Sarkin ya yi. Wajibi ne ya ci gaba da “yin nasara.” (R. Yoh. 6:2) Jehobah ƙudura cewa za a halaka dukan sassa duniyar Shaiɗan, kuma a kawo ƙarshen tasirin Shaiɗan da aljanunsa. Babila babba, wato daular addinin ƙarya ce za a soma halakawa. Jehobah zai yi amfani da masu mulki na duniya wajen halakar da wannan muguwar ‘karuwa.’ (R. Yoh. 17:16, 17) Bayan haka, wannan Sarki da kuma Mayaƙi zai kawo ƙarshen dukan gwamnatocin duniyar Shaiɗan. Kristi, wanda aka kira da suna “mala’ikan rami marar-matuƙa,” zai kammala nasararsa ta wajen jefa Shaiɗan da aljanunsa cikin rami marar matuƙa. (R. Yoh. 9:1, 11; 20:1-3) Bari mu tattauna yadda Zabura ta 45 ta annabta waɗannan abubuwan masu ban al’ajabi.

SARKIN YANA KĀRE GASKIYA

11. Ta yaya Kristi yake yaƙi don kāre “gaskiya”?

11 Karanta Zabura 45:4. Wannan Sarkin ba zai yi yaƙi don ya ci ƙasashe ko kuma ya mayar da mutane bayinsa ba. Amma yana da dalilai masu kyau na yin yaƙi. Yana yin yaƙi don ya kāre “gaskiya da tawali’u da adalci.” Gaskiya mafi muhimmanci da za a kāre ita ce wadda ta shafi Jehobah a matsayin Allah maɗaukakin Sarki. Sa’ad da Shaiɗan ya yi tawaye, ya ce Jehobah bai da ikon yin sarauta bisa halittunsa. Tun daga lokacin, aljanu da kuma wasu ’yan Adam sun saka hannu a wannan tawayen. Yanzu ne lokacin da Sarkin da Jehobah ya naɗa zai yi yaƙi don ya tabbatar wa dukan halittu cewa Jehobah shi ne wanda yake da ikon sarauta.

12. A wace hanya ce Sarkin yake yaƙi don ya ɗaukaka “tawali’u”?

12 Ƙari ga haka, Sarkin zai yi yaƙi don ya ɗaukaka “tawali’u.” Yesu ya kafa misali mafi kyau na nuna tawali’u da kuma biyayya ga Ubansa. (Isha. 50:4, 5; Yoh. 5:19) Wajibi ne duka talakawan Sarkin su bi misalinsa na tawali’u kuma su yi bayayya ga Jehobah a matsayin maɗaukakin Sarki. Waɗanda suka yi hakan ne kawai za a yarda su yi rayuwa a sabuwar duniya na Allah.—Zak. 14:16, 17.

13. Ta yaya Yesu yake yaƙi don ɗaukaka “adalci”?

13 Kristi yana yaƙi har ila don ya ɗaukaka “adalci.” Sarkin yana ɗaukaka “adalci na Allah,” wato ƙa’idodin Jehobah game da nagarta da mugunta. (Rom. 3:21; K. Sha 32:4) Annabi Ishaya ya yi annabci game da Sarki Yesu Kristi cewa: “Wani sarki za ya yi mulki cikin adalci.” (Isha. 32:1) Sarautar Yesu zai kawo “sababbin sammai da sabuwar duniya, inda adalci yake zaune.” (2 Bit. 3:13) Hakan yana nufin cewa za a bukaci kowa a sabuwar duniyar ya yi rayuwar da ta jitu da ƙa’idodin Jehobah game da nagarta da mugunta.—Isha. 11:1-5.

SARKIN YANA YIN ‘AL’AMURA MASU BAN RAZANA’

14. Ta yaya hannun dama na Kristi zai cim ma ‘al’amura na ban razana”? (Ka duba hoton da ke shafi na 3.)

14 Marubucin zabura ya ce Sarkin yana sukuwa da takobi a rataye a gefensa. (Zab. 45:3) Sai ya ɗauki takobin da hannun damarsa ya soma amfani da shi. Marubucin zabura ya annabta game da Yesu cewa: “Hannunka na dama za ya . . . [cim ma] al’amura na ban razana.” (Zab. 45:4) Sa’ad da Yesu Kristi zai yi sukuwa don ya halaka zamanin Shaiɗan a yaƙin Armageddon, zai yi “al’amura na ban razana” ga maƙiyansa. Ba mu san yadda zai halaka zamanin Shaiɗan ba, amma dukan wani matakin da zai ɗauka zai razanar da mutanen da suka ƙi amincewa da Sarautarsa. (Karanta Zabura 2:11, 12.) Sa’ad da yake annabci game da kwanaki na ƙarshe, Yesu ya ce mutane za su “suma don tsoro, da kuma fargabar al’amuran da ke aukuwa ga duniya, don za a girgiza manyan abubuwan da ke sararin sama.” Sai ya ƙara da cewa: “Sa’an nan za su ga Ɗan mutum yana zuwa a cikin girgije tare da iko da babbar daraja.”—Luk 21:26, 27.

15, 16. Su waye ne za su kasance a cikin “rundunan” da za su bi Yesu zuwa yaƙi?

15 Littafin Ru’ya ta Yohanna ya bayyana yadda Sarkin zai zo da “iko da ɗaukaka.” Ya ce: “Sai na ga sama a buɗe; ga kuma wani farin doki, da mahayinsa, ana ce da shi Mai-aminci da Mai-gaskiya; cikin adalci kuwa yake yin shari’a da yaƙi kuma. Rundunan yaƙi kuwa waɗanda ke cikin sama suka bi shi bisa fararen dawakai, suna yafe da linen mai-laushi, fari fat, mai-tsabta kuwa. Daga cikin bakinsa kuma takobi mai-kaifi yana fitowa, domin shi bubbuga al’ummai da shi: za ya mallake su kuma da sanda ta ƙarfe: yana kuwa taka wurin matsewar ruwan anab na zafin hasalar Allah Mai-iko duka.”—R. Yoh. 19:11, 14, 15.

16 Su waye ne “rundunan” da ke sama da za su bi Yesu zuwa wannan yaƙin? A lokaci na farko da Yesu ya rataye takobinsa don ya kori Shaiɗan da aljanunsa daga sama, “mala’iku” suna tare da shi. (R. Yoh. 12:7-9) Saboda haka, za mu iya cewa a yaƙin Armageddon, rundunan Yesu za su haɗa da mala’iku masu tsarki. Shin waɗansu za su kasance cikin wannan rundunan ne? Yesu ya yi wa ’yan’uwansa shafaffu alkawari cewa: “Wanda ya yi nasara kuma, wanda ya kiyaye ayyukana kuma har matuƙa, a gareshi zan bada iko bisa al’ummai: za ya mallaka su kuma da sanda ta ƙarfe, kamar yadda a ke parpashe tukwanen mai-tukwane; kamar yadda ni kuma na karɓa daga wurin Ubana.” (R. Yoh. 2:26, 27) Saboda haka, rundunan Kristi na sama za su ƙunshi ’yan’uwansa shafaffu, waɗanda za su kasance a cikin sama a lokacin. Abokan mulkinsa shafaffu za su kasance tare da shi sa’ad da yake cim ma “al’amura na ban razana” yayin da yake halaka al’ummai.

SARKIN YANA CIN NASARA

17. (a) Mene ne farin dokin da Yesu zai hau yake wakilta? (b) Mene ne takobin da bakar suke wakilta?

17 Karanta Zabura 45:5. Sarkin ya hau wani farin doki kuma hakan yana nufin yaƙi mai adalci da marar aibi a gaban Jehobah. (R. Yoh. 6:2; 19:11) Ban da takobi da ya rataye, yana riƙe da baka. Littafi Mai Tsarki ya ce: “Na duba kuma, ga farin doki; wanda yake zaune a kansa kuma yana da baka; kuma aka ba shi rawani: a kan nasara ya fita, garin yin nasara kuma.” Takobin da bakar suna wakiltar abubuwan da Kristi zai yi amfani da su don ya halaka magabtansa.

18. Ta yaya ‘kibaun’ Kristi za su kasance “tsinana”?

18 Marubucin zabura ya annabta game da Sarkin cewa: “Kibawunka tsinana ne; Suna cikin zuciyar maƙiyan sarki. Al’ummai suna ta faɗuwa a ƙarƙashinka.” Wannan halakar za ta faru a faɗin duniya. Annabcin Irmiya ya ce: “A ran nan fa za a ga kisassun Ubangiji tun daga wannan iyakar duniya zuwa wannan iyaka.” (Irm. 25:33) Wani annabci ya ce: “Na ga wani mala’ika kuma yana tsaye a rana; ya kuwa ta da murya da ƙarfi, ya ce ma dukan tsuntsayen da ke tashi a tsakiyar sarari, Ku zo ku tattaru zuwa wurin babban buki na Allah; domin ku ci naman, da naman jarumawa, da naman ƙarfafan mutane, da naman dawakai da na mahayansu, da naman dukan mutane, ’ya’ya da bayi, ƙanana da manya.”—R. Yoh. 19:17, 18.

19. Ta yaya Kristi zai yi “hawan ɗaukaka zuwa nasara”?

19 Yesu Kristi zai yi “hawan ɗaukaka zuwa nasara” bayan ya kawo ƙarshen zamanin Shaiɗan. (Zab. 45:4, Littafi Mai Tsarki) Zai kammala yaƙin ta wajen jefa Shaiɗan da aljanunsa cikin rami marar iyaka na tsawon shekara dubu. Shi da shafaffunsa 144,000 za su yi sarauta a wannan shekara dubun. (R. Yoh. 20:2, 3) Sa’ad da aka rufe Shaiɗan da aljanunsa a cikin rami marar iyaka, za su zama kamar matattu domin ba za su iya haddasa mugunta ba. Dukan waɗanda ke duniya za su ji daɗin sarautar Sarkin kuma Shaiɗan da aljanunsa ba za su yi tasiri a kan su ba. Kafin dukan duniya ta zama aljanna, akwai wani dalili na yin farin ciki tare da Sarkin da abokan mulkinsa guda 144,000. Za mu tattauna wannan abin farin ciki a talifin da ke gaba.

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba