ABIN DA KE SHAFIN FARKO | MUNA BUKATAR ALLAH KUWA?
Abin da Ya Sa Muke Bukatar Allah
Masanan tsarin hankali sun ce idan mutane suna son su yi farin ciki, wajibi ne su biya wa kansu bukatun da suka wuci na zahiri kawai. Muna ganin haka a yadda mutane suke ƙoƙarin yin hidima ga wani da suke ganin ya fi su girma a rayuwa don kawai su sami gamsuwa. Wasu kuma suna amfani da lokacinsu a yin bincike a kan halittu da ƙere-ƙere da waƙoƙi da dai sauransu. Duk da haka, galibin mutane ba sa samun gamsuwa sosai daga yin waɗannan abubuwan.
Allah yana son mutane su yi farin ciki yanzu da kuma har abada
Waɗanda suke karanta Littafi Mai Tsarki sun san cewa ƙari ga bukatun ’yan Adam na zahiri, suna da wata bukata dabam. Surorin farko na littafin Farawa sun bayyana cewa bayan Allah ya halicci ma’aurata na farko, ya yi magana da su a kai a kai. Hakan ya sa suka ƙulla dangantaka mai kyau da shi. (Farawa 3:8-10) Allah bai halicci ’yan Adam don su yi zaman ba ruwansu da shi ba. Suna bukatar sadawa da shi a matsayin Mahaliccinsu. Littafi Mai Tsarki ya yi zancen wannan bukatar sau da sau.
Alal misali, Yesu ya ce: “Masu farin ciki ne waɗanda suka san cewa suna bukatar ƙulla dangantaka da Allah.” (Matta 5:3, New World Translation of the Holy Scriptures) Kalamin Yesu ya nuna cewa wajibi ne mu biya muradin da muke da shi na sanin Allah idan muna so mu kasance da farin ciki da kuma gamsuwa a rayuwa. Ta yaya za mu iya yin hakan? Yesu ya ba da amsar cewa: “Ba da abinci kaɗai ba mutum za ya rayu, amma da kowace magana da ke fitowa daga bakin Allah.” (Matta 4:4) A waɗanne hanyoyi ne maganar Allah, wato, umurnansa da ke cikin Littafi Mai Tsarki za su taimaka mana mu yi farin ciki kuma rayuwarmu ta kasance da ma’ana? Bari mu bincika hanyoyi uku.
Muna Bukatar Ja-gora Mai Kyau
Akwai mashawarta da yawa a yau da suke shirye su ba da shawara idan ya zo ga batun dangantaka da soyayya da rayuwar iyali da sulhu da farin ciki da kuma ma’anar rayuwa. Amma wane ne zai iya ba da shawara da ta fi dacewa a kan waɗannan batutuwan, ban da Mahaliccin ’yan Adam wato, Jehobah Allah?
Alal misali, a ce ka sayi wata sabuwar na’ura kamar kyamara ko kuma kwamfuta. Za ka ga littafin da ke ɗauke da bayani a kan yadda za ka yi amfani da na’urar da kyau don ka more ta sosai. Za mu iya kwatanta Littafi Mai Tsarki da wannan littafin bayanin. Yana ɗauke da bayani game da rayuwar ’yan Adam, kuma Allah Mahaliccinmu ne ya ba mu don mu yi amfani da shi. Wannan littafin bayanin ya bayyana yadda za mu yi rayuwa a hanyar da ta dace don mu ji daɗinta.
Kamar yadda yake da littafin bayani mai kyau, Littafi Mai Tsarki yana wayar da kan masu karatunsa don su guji halaye da za su ɓata rayuwarsu. Wasu za su iya ba mu shawara da muke ganin ta fi kyau. Amma kana ganin idan muka bi umurnin Mahaliccinmu, ba za mu sami sakamako masu kyau har mu guji faɗa wa matsaloli ba?
“Ni ne Ubangiji Allahnka, wanda ya ke koya maka zuwa amfaninka, wanda yana bishe ka ta hanyar da za ka bi. Da ma ka yi sauraro ga dokokina! Da hakanan ne da salamarka ta yi kamar kogi, adalcinka kuma kamar raƙuman teku.”—Ishaya 48:17, 18
Ko da yake Jehobah yana ba mu umurni da kuma ja-gora, ba ya tilasta mana mu bi su. Amma domin yana ƙaunarmu kuma yana so ya taimaka mana, ya ce: “Ni ne Ubangiji Allahnka, wanda ya ke koya maka zuwa amfaninka, wanda yana bishe ka ta hanyar da za ka bi. Da ma ka yi sauraro ga dokokina! Da hakanan ne da salamarka ta yi kamar kogi, adalcinka kuma kamar raƙuman teku.” (Ishaya 48:17, 18) A taƙaice dai, idan muka bi ja-gorar Allah, za mu ji daɗin rayuwa. Wato, muna bukatar Allah idan muna so mu yi rayuwa mai gamsarwa kuma mu kasance da farin ciki.
Muna Bukatar Amsoshi ga Tambayoyin da Ke Damunmu
Abubuwan da ke faruwa a yau suna sa mutane ganin kamar Allah bai wanzu ba. A ganinsu, bai kamata waɗannan abubuwan su faru ba idan akwai Allah kuma yana ƙaunarmu. Saboda haka, suna ji kamar ba sa bukatar Allah a rayuwarsu. Alal misali, za su iya yin tambayoyi makamancin haka: ‘Me ya sa mutanen kirki suke shan wahala?’ ‘Me ya sa ake haifar jarirai da ba su san hawa ko sauka ba da lahani?’ ‘Me ya sa rayuwa ta cika da rashin adalci haka?’ Waɗannan tambayoyin suna da muhimmanci sosai, kuma za mu amfana idan muka sami amsoshi masu gamsarwa. Amma maimakon mu yi hanzarin ɗora wa Allah alhakin waɗannan matsalolin, ya kamata mu bincika abin da Kalmar Allah ta ce a kan wannan batun.
A littafin Farawa sura ta uku, mun karanta labarin Shaiɗan wanda ya yi magana ta bakin maciji. Ya sa ma’aurata na farko su karya dokar Jehobah ta wajen cin ’ya’yan itace na sanin nagarta da mugunta. Shaiɗan ya ce ma Hawwa’u: “Ba lallai za ku mutu ba: gama Allah ya sani ran da kuka ci daga ciki, ran nan idanunku za su buɗe, za ku zama kamar Allah, kuna sane da nagarta da mugunta.”—Farawa 2:16, 17; 3:4, 5.
Ta wannan furucin, Shaiɗan ya yi da’awar cewa Allah maƙaryaci ne kuma ba ya sarauta a hanyar da ta dace. Shaiɗan ya kuma ce idan ’yan Adam suka saurare shi, zai kyautata rayuwarsu. Ta yaya za a warware waɗannan matsalolin? Jehobah ya ga cewa hakan zai bukaci lokaci, don kowa ya sami damar sanin ko tuhumar da ake masa gaskiya ce ko kuma ƙarya. Allah yana ba Shaiɗan da kuma magoya bayansa dama su nuna ko rayuwa za ta fi kyau idan ’yan Adam ba su bi ja-gorar Allah ba.
Wace amsa ce za ka ba da ga tuhumar da Shaiɗan ya yi? Shin mutane za su iya yin mulkin kansu har su more rayuwa ba tare da bin ja-gorar Allah ba? Wahala da rashin adalci da cututtuka da mutuwa da aikata laifi da rashin ɗa’a da yaƙe-yaƙe har da kisan ƙare-dangi sun addabi ’yan Adam. Hakan tabbaci ne cewa ɗan Adam ba zai iya yin mulkin kansa ba. Littafi Mai Tsarki bai nuna cewa Allah ne yake haddasa matsalolin ’yan Adam ba. Maimakon haka, ya ce: “Waɗansu sukan sami mulki, waɗansu kuwa su sha wuya a ƙarƙashinsu.”—Mai-Wa’azi 8:9, Littafi Mai Tsarki.
Saboda haka, a bayyane yake cewa zai dace mu biɗi amsoshin waɗannan tambayoyin daga wajen Allah kuma mu dangana da shi don ya magance matsalolin da ke damun mutane, ko ba haka ba? Kana ganin Allah zai yi wani abu kuwa?
Muna Bukatar Taimakon Allah
An yi shekaru aru-aru yanzu da mutane suke neman ’yanci daga rashin lafiya da tsufa da kuma mutuwa. Sun ɓad da lokaci da kuɗi kuma sun ƙoƙarta sosai don su sami wannan ’yancin, amma duk wannan haƙar ba ta cim ma kome ba. Wasu suna ganin kamar za su iya yin rayuwa har abada ta wajen shan wasu ire-iren magunguna da wani irin ruwa. Wasu kuma sun dogara ga kimiyya. Amma waɗannan abubuwan ba su taimaka musu ba.
Allah yana so mutane su ji daɗin rayuwa kuma su yi farin ciki. Abin da ya sa ya halicci ’yan Adam ke nan, kuma bai mance da hakan ba. (Farawa 1:27, 28; Ishaya 45:18) Muna da tabbaci daga Jehobah cewa tabbas zai yi duk abin da ya nufa. (Ishaya 55:10, 11) Littafi Mai Tsarki ya bayyana mana alkawari da Allah ya yi na mai da duniya Aljanna, don ta zama kamar yadda take kafin Adamu da Hawwa’u su yi zunubi. A cikin Ru’ya ta Yohanna, mun karanta waɗannan kalmomin: “[Jehobah Allah] zai share dukan hawaye kuma daga idanunsu: mutuwa kuwa ba za ta ƙara kasancewa ba; ba kuwa za a ƙara yin baƙin ciki, ko kuka, ko azaba: al’amura na fari sun shuɗe.” (Ru’ya ta Yohanna 21:4) Ta yaya Allah zai cika wannan alkawarin, kuma mene ne za mu yi don mu amfana?
Yesu Kristi Ɗan Allah ya koya wa mabiyansa su yi addu’a a yi nufin Allah a duniya. Mutane da yawa sun san wannan addu’ar har ma sukan maimaita ta sau da sau, kuma wasu suna kiranta Addu’ar Ubangiji. Ga yadda ake addu’ar: “Ubanmu wanda ke cikin sama, a tsarkake sunanka. Mulkinka shi zo. Abin da kake so, a yi shi, cikin duniya, kamar yadda ake yinsa cikin sama.” (Matta 6:9, 10) Hakika, ta wajen Mulkinsa ne Jehobah zai kawar da munanan sakamakon da sarautar ’yan Adam ta jawo, sa’an nan ya kawo sabuwar duniya da ba rashin adalci.a (Daniyel 2:44; 2 Bitrus 3:13) Mene ne ya kamata mu yi don mu amfana daga alkawarin Allah?
Yesu ya bayyana abin da ya kamata mu yi kuma hakan babu wuya. Ya ce: “Rai na har abada ke nan, su san ka, Allah makaɗaici mai-gaskiya, da shi kuma wanda ka aiko, Yesu Kristi.” (Yohanna 17:3) Babu shakka, da taimakon Allah, zai yiwu mu shiga wannan sabuwar duniya kuma mu yi rayuwa har abada a cikinta. Ya kamata sanin hakan ya tabbatar maka cewa muna bukatar Allah.
Yanzu Ne Lokacin da Za A Nemi Allah
Shekaru dubu biyu da suka gabata, Bulus ya gaya wa ’yan ilimin falsafa a kan Tudun Arasa da ke birnin Atina cewa: “Shi da kansa yana ba kowa rai, da numfashi, da abu duka; gama cikinsa muke rayuwa, muke motsi, muke zamanmu; kamar yadda waɗansu daga cikin mawaƙanku da kansu suka ce, ‘Gama mu kuma zuriyarsa ne.’”—Ayyukan Manzanni 17:25, 28.
Abin da Bulus ya gaya wa mutanen Atina gaskiya ne ma a yau. Mahaliccinmu ne yake tanadin iskar da muke sheƙa da ruwan da muke sha da kuma abinci. A gaskiya, ba yadda za mu iya yin rayuwa idan Allah bai yi mana tanadin waɗannan abubuwan ba. Amma, me ya sa Allah ya ci gaba da tanada waɗannan abubuwan ga dukan mutane, har ma da waɗanda ba su damu da shi ba? Bulus ya ce “domin su nemi Allah, ko halama su a lallaba su same shi, ko da yake ba shi da nisa da kowane ɗayanmu.”—Ayyukan Manzanni 17:27.
Za ka so ka ƙara sanin Allah, wato ka ƙara koya game da nufe-nufensa da kuma shawararsa game da yadda za mu iya jin daɗin rayuwa yanzu da kuma a nan gaba? Idan kana so ka yi hakan, za ka iya tuntuɓar wanda ya ba ka wannan mujallar ko kuma mawallafanta. Za su yi farin cikin taimaka maka.
a Don ƙarin bayani a kan yadda Mulkin zai sa a yi nufin Allah a duniya, ka karanta babi na 8 a cikin littafin nan Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa? Shaidun Jehobah ne suka wallafa kuma za ka iya karanta ko ka saukar a dandalin www.jw.org/ha.