ABIN DA KE SHAFIN FARKO | MUNA BUKATAR ALLAH KUWA?
Me Ya Sa Ake Wannan Tambayar?
“Allah yana da muhimmanci a rayuwarka? Miliyoyin mutane ba sa ganin muhimmancinsa.” Abin da wani rukunin waɗanda ba su yarda cewa akwai Allah ba suka sa a rubuta ke nan a kan wani babban allon talla, domin a ganinsu ba sa bukatar Allah.
A wani ɓangare kuma, waɗanda suke da’awa cewa sun yi imani da Allah suna yin abubuwa kamar ba su san da wanzuwarsa ba. Wani akbishop na cocin Katolika mai suna Salvatore Fisichella ya yi bayani game da mutanen cocinsa cewa: “Wataƙila babu wanda zai gane cewa mu Kiristoci ne, domin muna rayuwa kamar waɗanda ba su yi imani da Allah ba.”
Wasu mutane ba su da lokacin damun kansu da Allah. A ganinsu, Allah ba zai iya kasancewa da wani tasiri a rayuwarsu ba domin ya yi nisa ainun. Irin waɗannan mutanen suna neman Allah sa’ad da suke da wata matsala ko kuma suke bukatar wani abu ne kawai. Kamar dai Allah wani ɗan aika ne da ke jira a gaya masa abin da zai yi.
Wasu kuma ba sa bin koyarwar addininsu, wataƙila don suna ganin yin hakan ba shi da amfani. Alal misali, kashi 76 bisa ɗari na mabiyan ɗarikar Katolika a Jamus sun yarda cewa daidai ne namiji da tamace su zauna tare kafin su yi aure. Wannan ra’ayin bai dace da koyarwar cocinsu da kuma na Littafi Mai Tsarki ba. (1 Korintiyawa 6:18; Ibraniyawa 13:4) Hakika, ba ’yan Katolika ne kaɗai suke yin rayuwa da ba ta jitu da imaninsu ba. Limaman addinai da yawa sun damu a kan yadda mabiyan ɗarikarsu suke rayuwa kamar mutanen da ba su gaskata cewa Allah ya wanzu ba.
Waɗannan misalan ne suke sa mutane yin wannan tambayar: Muna bukatar Allah da gaske kuwa? Wannan batun ba sabon abu ba ne. An ta da wannan batun a surori na farko a cikin Littafi Mai Tsarki. Don mu sami amsar wannan tambayar, zai dace mu mai da hankali ga wasu batutuwa da aka ambata a cikin littafin Farawa.