Abin Da Ke Ciki
15 ga Agusta, 2013
© 2013 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania. All rights reserved.
NA NAZARI
30 GA SATUMBA, 2013–6 GA OKTOBA, 2013
SHAFI NA 3 • WAƘOƘI: 125, 66
7-13 GA OKTOBA, 2013
Kada Ka Kuskura Ka Yi Gunaguni da Jehobah
SHAFI NA 10 • WAƘOƘI: 119, 80
14-20 GA OKTOBA, 2013
Mu Riƙa Kula da Kuma Ƙarfafa Juna
SHAFI NA 18 • WAƘOƘI: 124, 20
21-27 GA OKTOBA, 2013
Wane Irin Mutum Ne Ya Kamata Ka Zama?
SHAFI NA 23 • WAƘOƘI: 61, 43
TALIFOFIN NAZARI
▪ An Tsarkake Ka
A matsayin bayin Jehobah, an tsarkake ko kuma ware mu don yin hidimar Allah. A wannan talifin za mu tattauna littafin Nehemiya sura ta 13. Za mu bincika abubuwa huɗu da za su iya taimaka mana mu kasance da tsarki.
▪ Kada Ka Kuskura Ka Yi Gunaguni da Jehobah
A wannan talifin, za mu tattauna abubuwa biyar da za su iya sa Kirista mai aminci ya yi “gunaguni da Ubangiji.” (Mis. 19:3) Bayan hakan za mu tattauna hanyoyi biyar da za mu guji ɗora wa Jehobah laifi don matsalolin da muke fuskanta.
▪ Mu Riƙa Kula da Kuma Ƙarfafa Juna
▪ Wane Irin Mutum Ne Ya Kamata Ka Zama?
Na farko cikin waɗannan talifofin ya tattauna yadda za mu taimaka wa juna don mu kasance da ƙarfin zuciya duk da matsaloli da muke fuskanta. Talifi na biyu ya nuna yadda za mu yi nasara wajen yin tsayayya da gwajin da Shaiɗan yake amfani da shi don ya ɓata dangantakarmu da Allah.
A FITOWAR NAN
8 Amsoshin Tambayoyin Masu Karatu
9 Jehobah Yana ‘Ɗaukan Nauwayata Kowace Rana’
15 Iyaye—Ku Koyar da Yaranku Tun Suna Jarirai
BANGO: Masu shela suna wa’azi gida gida a ƙauyen Erap. Yana cikin ƙauyuka masu yawa da ke tuddan Lardin Marobe a ƙasar Papua New Guinea
PAPUA NEW GUINEA
Yawan Jama’a: 7,013,829
Abirejin Masu Shela: 3,770
Abirejin Majagaba na Kullum: 367
Abirejin Nazarin Littafi Mai Tsarki: 5,091
Waɗanda Suka Halarci Taron Tunawa da Mutuwar Yesu a Shekara ta 2012: 28,909
Fassara: Harsuna 14
A taron Tuna da Mutuwar Yesu, kowane mai shela ya marabci misalin mutane shida da suke son saƙonmu