Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • mrt talifi na 14
  • Yohanna mai Baftisma ya Taba Wanzuwa Kuwa?

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Yohanna mai Baftisma ya Taba Wanzuwa Kuwa?
  • Karin Batutuwa
  • Makamantan Littattafai
  • Wane ne Yohanna Mai Baftisma?
    Amsoshin Tambayoyi Daga Littafi Mai Tsarki
Karin Batutuwa
mrt talifi na 14
Yohanna Mai Baftisma yana yi wa mutane baftisma.

Yohanna Mai Baftisma Ya Taba Wanzuwa Kuwa?

Linjila ta ambaci wani mutum mai suna Yohanna Mai Baftisma, wanda ya yi wa’azi game da Mulkin Allah a Yahudiya. Abin da Littafi Mai Tsarki ya ce game da mutumin gaskiya ce? Bari mu yi la’akari da wadannan:

  • Littafi Mai Tsarki ya ce: “Yohanna Mai Baftisma ya fito yana wa’azi a cikin dajin yankin Yahudiya, yana cewa: ‘Ku tuba, gama mulkin sama ya kusa.’” (Matiyu 3:​1, 2) Masana sun tabbatar da hakan kuwa? Kwarai kuwa.

    Wani masanin tarihi mai suna Flavius Josephus ya yi bayani a kan wani mutum mai suna “Yohanna da ake ce da shi Mai Baftisma,” wanda ya “gargadi Yahudawa su yi rayuwa da ta dace,” su yi “sujjada ga Allah,” kuma “su zo a yi musu baftisma.”​—Jewish Antiquities, Book XVIII.

  • TBaibul ya nuna cewa Yohanna ya tsauta wa Hirudus Antibas wanda shi hakimin Galili da Firiya ne. Hirudus Bayahude ne da ke da’awa cewa yana bin Dokar Allah. Yohanna ya gaya wa Hirudus cewa bai dace da ya auri Hirudiya, matar dan’uwansa ba. (Markus 6:18) Bayanin nan ya jitu da abin da masana suka ce.

    Josephus ya ce Antibas “ya yi sha’awar Hirudiya” kuma ya yi “zancen aure da ita.” Sai Hirudiya ta amince, ta bar mijinta kuma ta auri Antibas.

  • Littafi Mai Tsarki ya ce “sai mutanen Urushalima da na yankin Yahudiya duka, da na dukan kasashen yankin kogin Yodan, suka yi ta zuwa wurinsa [Yohanna], yana yi musu baftisma a Kogin Yodan.”​—Matiyu 3:​5, 6.

    Josephus ma ya amince da wannan bayanin, kuma ya rubuta cewa “jama’a” sun zo wurin Yohanna domin “koyarwarsa ta ratsa zuciyarsu sosai.”

Babu shakka, Josephus wanda shi masanin tarihi ne a karni na farko ya yarda cewa Yohanna Mai Baftisma ya taba wanzuwa. Mu ma mun amince da hakan.

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba