Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w13 2/15 pp. 31-32
  • “Abin da Ba Za a Taɓa Mantawa Ba” Ya Zo a Kan Kari

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • “Abin da Ba Za a Taɓa Mantawa Ba” Ya Zo a Kan Kari
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2013
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2013
w13 2/15 pp. 31-32

Daga Tarihinmu

“Abin da Ba Za a Taɓa Mantawa Ba” Ya Zo a Kan Kari

“ABIN da ba za a taɓa mantawa ba.” Yadda mutane da yawa suka ƙwatanta wannan wasan kwaikwayon da ake kira, “Creation Drama” ke nan. Ya zo a kan kari, kuma waɗanda suka kalli bidiyon ba za su manta da shi ba. Wannan bidiyon ya sa an yabi Jehobah sosai kafin aka soma tsananta wa bayinsa da ke ƙasar Turai a lokacin da Hitler ya fara mulki. Amma, wane irin bidiyo ne “Creation Drama”?

A shekara ta 1914, hedkwatar Shaidun Jehobah da ke Brooklyn a birnin New York a ƙasar Amirka, ta fitar da bidiyon nan “Photo-Drama of Creation.” Wannan bidiyon ya kai tsawon awa takwas, kuma majigi ne mai ɗauke da hotuna da kuma sauti. A duk duniya, mutane fiye da miliyan ɗaya sun kalli wannan bidiyon. A wannan shekarar ce kuma aka fitar da wani bidiyo “Eureka Drama.” Ya yi kamar na farkon, amma bai kai tsawonsa ba. A shekara ta 1920 zuwa 1929, kayan nuna wannan majigin suka lalace. Duk da haka, mutane da yawa suna bukatar su kalla wannan bidiyon. Alal misali, waɗanda suke zama a birnin Ludwigsburg da ke ƙasar Jamus sun yi tambaya cewa, “Yaushe ne za a ƙara nuna wannan bidiyon?” Mene ne za a yi don a sake nuna wannan bidiyon?

Don a sake samun damar nuna wannan bidiyon, wasu ’yan’uwa daga Bethel da ke birnin Magdeburg a ƙasar Jamus, sun sayo kayan fim daga wani kamfanin yaɗa labarai da ke birnin Paris a ƙasar Faransa, a tsakanin shekara ta 1920 zuwa 1929. Sun kuma sayo wasu majigai daga kamfanin da ke Leipzig da kuma Dresden. Sai suka haɗa su da tsofaffin majigan “Photo-Drama of Creation” masu ɗan kyau.

Ɗan’uwa Erich Frost gwani mawaƙi ne, kuma shi ya shirya waƙar da aka saka a cikin fim ɗin da majigan. An ɗauko wasu labaran ne daga littafin nan Creation. Shi ya sa aka ba sabon bidiyon sunan nan “Creation Drama.”

Sabon bidiyon ya kai tsawon awa takwas kamar na “Photo-Drama of Creation,” kuma an nuna sashe guda a kowane dare. Wannan bidiyon ya yi bayani dalla-dalla game da ranakun halitta da tarihin Littafi Mai Tsarki da na duniya, kuma ya bayyana cewa addinan ƙarya sun kasa taimaka wa ’yan Adam. An nuna bidiyon a ƙasar Austria da Jamus da Luxemburg da Siwizalan. Wasu ’yan ƙasar Jamus da ke wurare dabam-dabam ma sun kalli bidiyon a yarensu.

Erich Frost ya ce: “A lokacin da ake nuna bidiyon, na ƙarfafa ’yan’uwa da muke aiki tare, musamman waɗanda ke sashen waƙa su yi amfani da lokacin hutu don rarraba littattafai da ƙasidu ga waɗanda suka halarta. Mun rarraba mujallu ta wannan hanyar, fiye da sa’ad da muke wa’azi gida-gida.” Ɗan’uwa Johannes Rauthe ya shirya nuna wannan bidiyon a ƙasar Polan da Jamhuriyar Czech, kuma ya tuna cewa mutane da yawa da suka halarta sun ba da adireshinsu domin ’yan’uwa su kai musu ziyara. Ta waɗannan adireshin, sun koma kuma suka tattauna Littafi Mai Tsarki sosai da su.

A tsakanin shekara ta 1930 zuwa 1939, mutane sukan yi cunƙus a duk majami’ar da aka nuna bidiyon. Kuma mutane sun yi ta taɗi game da Shaidun Jehobah. A wannan shekarar, mutane kusan miliyan sun halarci duk nuna bidiyon da ofishin reshe da ke Jamus ya shirya. ’Yar’uwa Käthe Krauss ta tuna cewa a duk kwana biyar da aka nuna bidiyon, sun yi tafiya mai nisan mil shida, suna hawa da saukowa daga kan tudu. ’Yar’uwa Else Billharz kuma ta ce wannan bidiyon ya sa ta soma ƙaunar koyarwa ta gaskiya.

Ɗan’uwa Alfred Almendinger ya ce sa’ad da mahaifiyarsa ta kalli bidiyon, ta yi farin cikin sosai, har ta sayo Littafi Mai Tsarki domin ta duba kalmar nan ‘purgatory.’ Tun da yake ba ta ga kalmar a cikin Littafi Mai Tsarki ba, ta daina zuwa coci sai kuma ta yi baftisma. “Bidiyon ya taimaka wa mutane da yawa su zama Shaidu,” in ji Erich Frost.—3 Yoh. 1-3.

Kamar yadda masu son kallon bidiyon suke ƙaruwa, hakan ma masu goyon baya mulkin Nazi ke ƙaruwa a ƙasar Turai, kuma sai ta da rikici suke yi. An hana ayyukan Shaidun Jehobah a ƙasar Jamus a shekara ta 1933. An ci gaba da tsananta wa bayin Jehobah a ƙasar Turai, tun daga lokacin har ƙarshen yaƙin duniya na biyu a shekara ta 1945. Erich Frost ya yi shekara takwas a kurkuku. Bayan hakan, ya yi hidima a Bethel da ke birnin Wiesbaden a ƙasar Jamus. Wannan bidiyon da ba za a taɓa mantawa ba, ya ƙarfafa ’yan’uwa da yawa da aka tsananta musu a yaƙin duniya ta biyu.—Daga tarihinmu a ƙasar Jamus.

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba