Ita Dangin Kayafa Ce
A wasu lokatai, ’yan tone-tonen ƙasa sukan tono wasu abubuwa da ke ba da tabbaci cewa wani da aka ambata a cikin Littafi Mai Tsarki ya rayu da gaske. Alal misali, a shekara ta 2011, waɗansu masana da ke ƙasar Isra’ila sun wallafa bayani game da wani abin da aka tono da ya ba da irin wannan tabbacin. Wata taska ce da ta yi shekaru dubu biyu a wani kabari. An ajiye ƙasusuwan mamaci ne a ciki, bayan tsokarsa ta ruɓe.
A jikin wannan taskar, an rubuta: “Miriam ’yar Yeshua, ɗan Kayafa, firist na Maʹaziah daga garin Beth ʹImri.” Kayafa babban firist Ba-Yahude, yana cikin waɗanda suka hukunta Yesu. (Yoh. 11:48-50) Wani ɗan tarihi mai suna Flavius Josephus ya ce da shi “Yusufu, wanda ake kira Kayafa.” Babu shakka cewa wannan taskar ta wani danginsu ne. Wataƙila Yusufu dangin Miriam ne, tun da yake ana ganin wannan taskar da aka tono ta Yusufu ɗan Kayafaa ne.
Hukumar binciken tarihin ƙasar Isra’ila ta bayyana cewa, an ƙwato taskar Miriam ne daga hannun ɓarayin da suka tono ta daga kabari a zamanin dā. Binciken da aka yi ya nuna cewa wannan taskar da kuma abin da aka rubuta a jikinsa gaskiya ne.
Mun koyi wani abu kuma dabam game da taskar Miriam. A jikinta, an rubuta “Maʹaziah,” wanda shi ne zuriya na ƙarshe a rukunoni ashirin da huɗu na firistoci da suka yi hidima bi da bi a haikalin da ke Urushalima. (1 Laba. 24:18) Hukumar binciken ta daɗa cewa rubutun da ke jikin taskar ya nuna cewa dangin Kayafa daga zuriyar Maʹaziah ne.
An rubuta Beth ʹImri. Wannan rubutun yana iya nufin abubuwa biyu. Na ɗaya, yana iya nufin wani iyalin firistoci da ake kira ’ya’yan ’Immer. (Ezra 2:36, 37; Nehemiya 7:39-42) Wasu daga wannan iyalin ne suka zama zuriyar Maʹaziah. Na biyu, Beth ‘Imri yana iya nufin inda aka haifi Miriam ko kuma danginta. Ko ta yaya dai, taskar Miriam tabbaci ne cewa mutanen da aka ambata a Littafi Mai Tsarki mutane ne da suka rayu da gaske.
a Ka karanta game da taskar Kayafa a cikin talifin nan “The High Priest Who Condemned Jesus” a Hasumiyar Tsaro ta 15 ga Janairu, 2006, shafuffuka na 10-13 na Turanci.