Ka Yi Biyayya Don Ka Amfana Daga Alkawuran Allah
“Tun da babu wani da ya fi [Allah] girma wanda za ya rantse da shi, sai ya rantse da kansa.”—IBRAN. 6:13.
MECE CE AMSARKA?
Me ya sa muka kasance da tabbaci cewa Allah zai cika alkawuransa?
Wane alkawari ne Allah ya yi bayan Adamu da Hauwa’u sun yi zunubi?
Ta yaya muka amfana daga rantsuwa da Allah ya yi wa Ibrahim?
1. Ta yaya alkawarin Jehobah ya bambanta da na ’yan Adam ajizai?
JEHOBAH ne “Allah na gaskiya.” (Zab. 31:5) Domin ’yan Adam ajizai ne, ba a kowane lokaci ba ne za mu iya amincewa da su. Amma, “ba shi yiwuwa Allah ya yi ƙarya.” (Ibran. 6:18; karanta Littafin Lissafi 23:19.) Allah yana cika alkawarin da ya yi wa ’yan Adam. Alal misali, Allah ya halicci kome a duniya cikin kwanaki shida na halitta kamar yadda ya faɗa da farko. Saboda haka, a ƙarshe “Allah kuma ya duba kowane abin da ya yi, ga shi kuwa, yana da kyau ƙwarai.”—Far. 1:6, 7, 30, 31.
2. Mene ne ranar hutu na Allah, kuma me ya sa ya “tsarkake ta”?
2 Bayan Jehobah Allah ya ce dukan abubuwan da ya halitta suna da kyau sosai, sai ya sanar da somawar kwana na bakwai. A wannan kwana na bakwai ne ya huta daga aikinsa. Wannan ba rana ba ce da ta ƙunshi sa’o’i 24, amma lokaci ne da ya daina halitta a duniya. (Far. 2:2) Allah yana hutu har ila. (Ibran. 4:9, 10) Littafi Mai Tsarki bai gaya mana ainihin lokacin da ya soma hutun ba. Amma, mun san cewa ya soma hutun bayan ya halicci Hauwa’u, wato, kusan shekara 6,000 da ta shige. Nan ba da daɗewa ba, Yesu Kristi zai soma sarauta na shekara dubu, kuma a lokacin, Allah zai cika alkawarinsa game da duniya. Zai mai da duniya aljanna kuma ’yan Adam kamiltattu za su kasance a cikinta har abada. (Far. 1:27, 28; R. Yoh. 20:6) Babu shakka, za ka ji daɗin rayuwa a nan gaba! “Allah ya albarkaci rana ta bakwai, ya tsarkake ta.” Hakan ya tabbatar mana cewa babu kome da zai iya hana Allah ya cika alkawarinsa a ƙarshen hutunsa.—Far. 2:3.
3. (a) Wane tawaye ne aka yi bayan Allah ya soma hutu? (b) Yaya Jehobah ya ce zai magance wannan matsalar?
3 Wasu cikin halittun Allah suka yi masa tawaye bayan ya soma hutu. Shaiɗan, wanda mala’ika ne a sama ya rinjayi wasu su bauta masa maimakon Allah. Ya yi ƙarya na farko kuma ya ruɗi Hauwa’u har ta yi wa Jehobah rashin biyayya. (1 Tim. 2:14) Bayan haka, Hauwa’u kuma ta sa mijinta ya yi wa Allah rashin biyayya. (Far. 3:1-6) Babu tawayen da ya kai wannan. Ko da yake Shaiɗan ya ce Jehobah maƙaryaci ne, amma Jehobah bai ga amfanin rantsewa cewa har ila zai cika alkawarinsa ga duniya ba. Maimakon hakan, ya yi alkawari da za a fahimta a nan gaba. Ya faɗi yadda zai warware matsalar, ya ce: “Tsakaninka [Shaiɗan] da macen kuma zan kafa magabtaka, da tsakanin zuriyarka da zuriyarta kuma: Shi [zuriyar da aka yi alkawarinta] za ya ƙuje kanka, kai kuma za ka ƙuje duddugensa.”—Far. 3:15; R. Yoh. 12:9.
AMFANIN RANTSUWA
4, 5. Mene ne Ibrahim ya yi don ya nuna cewa zai cika alkawarinsa?
4 Tun daga lokacin ne rantsuwa ta kasance da muhimmanci a tarihin ’yan Adam. Kamiltattun halittu da suke ƙaunar Allah da kuma koyi da shi ba sa bukatar su yi rantsuwa. Amma, suna faɗin gaskiya a kowane lokaci kuma sun amince da juna sosai. Ƙarya da ruɗu sun zama ruwan dare gama gari bayan ma’aurata na farko suka yi zunubi kuma suka zama ajizai. Sai mutane suka soma rantsuwa don su nuna cewa abin da suke faɗi gaskiya ne.
5 Ibrahim ya rantse har sau uku. (Far. 21:22-24; 24:2-4, 9) Alal misali, ya yi rantsuwa sa’ad da ya ci sarkin Elam da dukan sarakuna da suka goyi bayansa a yaƙi. Sarakunan Salem da Saduma suka fito su marabce shi. Melchizedek, sarkin Salem wanda “firist ne na Allah Maɗaukaki,” ya albarkaci Ibrahim kuma ya yabi Allah don ya sa Ibrahim ya yi nasara bisa magabtansa. (Far. 14:17-20) Sa’ad da sarkin Saduma yake son ya albarkaci Ibrahim don ya ceci mutanensa daga hannun sojoji da suka kai musu hari, Ibrahim ya yi rantsuwa ya ce: “Na rigaya na tada hannuna ga Ubangiji, Allah maɗaukaki, mai-sama da ƙasa, ba ni karɓan ko zare ko maɓallin takalmi ko komenene da ke naka, domin kada ka ce, Ni ne na arzutarda Abram [Ibrahim].”—Far. 14:21-23.
ALKAWARIN DA JEHOBAH YA YI WA IBRAHIM
6. (a) Wane misali ne Ibrahim ya kafa mana? (b) Ta yaya za mu amfana daga abin da Ibrahim ya yi?
6 Don Jehobah Allah ya tabbatar wa ’yan Adam ajizai cewa zai cika alkawarinsa, sai ya ce, “Na rantse da raina, in ji Ubangiji Yahweh.” (Ezek. 17:16) Littafi Mai Tsarki ya nuna wurare fiye da 40 da Jehobah Allah ya yi rantsuwa. Misalin da muka fi sani shi ne wanda ya yi wa Ibrahim. Jehobah ya yi wa Ibrahim alkawura da yawa, kuma ya ce zuriyar da aka yi alkawarinta za ta fito ta wurin ɗansa Ishaƙu. (Far. 12:1-3, 7; 13:14-17; 15:5, 18; 21:12) Jehobah ya gwada Ibrahim sosai, ta wurin gaya masa ya miƙa ɗansa ƙaunatacce. Ibrahim ya soma yin hakan babu ɓata lokaci, amma dab da lokacin da yake son ya miƙa ɗansa Ishaƙu, sai mala’ikan ya hana shi. Sai Allah ya yi wannan rantsuwar: “Na rantse da [raina], tun da ka yi wannan abu, ba ka kuwa hana ɗanka, tilonka ba: a kan albarka zan albarkace ka; wajen daɗuwa, zan riɓanɓanya tsatsonka kamar taurarin sama, kamar yashi kuma wanda ke a bakin teku; tsatsonka kuma za shi gaji ƙofar magabtansa; cikin zuriyarka kuma dukan al’umman duniya za su sami albarka; domin ka yi biyayya da maganata.”—Far. 22:1-3, 9-12, 15-18.
7, 8. (a) Me ya sa Allah ya rantse wa Ibrahim? (b) Ta yaya “waɗansu tumaki” za su amfana daga alkawari da rantsuwar da Allah ya yi wa Ibrahim?
7 Me ya sa Allah ya rantse wa Ibrahim cewa zai cika alkawarinsa? Domin hakan zai ƙarfafa bangaskiyar waɗanda za su zama sashe na biyu na “zuriyar” da aka yi alkawarinta, kuma za su yi sarauta tare da Kristi. (Karanta Ibraniyawa 6:13-18; Gal. 3:29) Manzo Bulus ya ce, Jehobah “ya shiga da rantsuwa a ciki: domin bisa ga abu biyu da ba su sākuwa [alkawarinsa da rantsuwarsa], inda ba shi yiwuwa Allah ya yi ƙarya, mu mu sami abin ƙarfafawar zuciya mai-ƙarfi . . . domin mu kama begen da aka sanya a gabanmu.”
8 Ban da shafaffu, wasu ma sun amfana daga rantsuwa da Allah ya yi wa Ibrahim. Jehobah rantse cewa ta wurin “zuriyar” Ibrahim, “dukan al’umman duniya za su sami albarka.” (Far. 22:18) Mutanen sun haɗa da “waɗansu tumaki” da suka yi biyayya ga Kristi, kuma suna da begen rayuwa a aljanna a duniya har abada. (Yoh. 10:16) Ko da kana da begen rayuwa a sama ko kuma duniya, ka “kama” begen ta wurin yin biyayya ga Allah.—Karanta Ibraniyawa 6:11, 12.
WANI ALKAWARI KUMA DA ALLAH YA YI
9. Wace rantsuwa ce Allah ya yi sa’ad da zuriyar Ibrahim take bauta a ƙasar Masar?
9 Bayan shekaru da yawa, Jehobah ya kuma rantse cewa zai cika alkawuran da ya yi wa Ibrahim. Ya yi hakan sa’ad da ya aiki Musa ya yi magana ga zuriyar Ibrahim da suka zama bayi a ƙasar Masar. (Fit. 6:6-8) Sa’ad da Allah yake magana game da wannan lokacin, ya ce: ‘A ran da na zaɓi Isra’ila, . . . na rantse masu, na ce zan fito da su daga cikin ƙasar Masar, in kawo su cikin ƙasa wadda na tsinkayo masu, ƙasa mai-zuba da madara da zuma.’—Ezek. 20:5, 6.
10. Wane alkawari ne Allah ya yi wa Isra’ilawa bayan ya fito da su daga ƙasar Masar?
10 Bayan da Jehobah ya ceci al’ummar Isra’ila daga ƙasar Masar, ya yi wani alkawari cewa: “Idan lallai za ku yi biyayya da maganata, ku kiyaye wa’adina kuma, sa’annan za ku zama keɓaɓiyar taska a gare ni daga cikin dukan al’umman duniya; gama dukan duniya tawa ce. Za ku zama mulki na firistoci a gare ni, al’umma mai-tsarki.” (Fit. 19:5, 6) Allah ya ba Isra’ilawa matsayi na musamman! Hakan yana nufin cewa idan sun yi biyayya ga Jehobah, zai zaɓi firistoci daga cikinsu da za su yi sarauta bisa dukan ’yan Adam. Daga baya, Jehobah ya bayyana cewa ya rantse wa Isra’ila. Ya ce: ‘Na rantse maki, na kuwa yi alkawari da ke.’—Ezek. 16:8.
11. Mene ne Isra’ilawa suka yi sa’ad da Allah ya ba su gatar zama al’ummarsa ta musamman?
11 Jehobah bai tilasta wa Isra’ilawa su rantse cewa za su yi masa biyayya ba, kuma bai nace musu su ƙulla dangantaka da shi ba. Amma, su da kansu ne suka rantse cewa: “Abin da Ubangiji ya faɗi duka mu a yi.” (Fit. 19:8) Bayan kwanaki uku, Jehobah Allah ya gaya wa Isra’ilawa abin da yake son su yi a matsayin al’ummar da ya zaɓa. Da farko, ya ba su Dokoki Goma kuma ya sa Musa ya ba su wasu umurni da ke rubuce a littafin Fitowa 20:22 zuwa sura 23:33. Mene ne Isra’ilawa suka ce? “Dukan mutane fa suka amsa baki ɗaya, suka ce, Dukan zantattukan da Ubangiji ya faɗi mu a aikata su.” (Fit. 24:3) Sai Musa ya rubuta dokokin cikin “littafin alkawari” kuma ya karanta da babbar murya don dukan al’ummar su sake ji. Bayan hakan, mutanen suka yi alkawari na uku, suka ce: “Dukan abin da Ubangiji ya faɗi mu a yi, mu yi biyayya kuma.”—Fit. 24:4, 7, 8.
12. Mene ne Jehobah da Isra’ilawa suka yi sa’ad da suka yi wa juna alkawari?
12 Nan da nan, Jehobah ya soma cika alkawarin da ya yi wa Isra’ilawa. Ya zaɓi firistoci da za su yi hidima a tanti na bauta. Waɗannan firistocin za su taimaka wa ’yan Adam ajizai su ƙulla dangantaka ta musamman da Jehobah. Amma, ba da daɗewa ba, Isra’ilawa suka manta cewa sun keɓe kansu ga Allah kuma suka “cakuni Mai-tsarki na Isra’ila.” (Zab. 78:41) Alal misali, sa’ad da Musa yake karɓan ƙarin umurni a kan Dutsen Sinai, Isra’ilawa suka gaji da jiransa, suka yi rashin bangaskiya ga Allah, suna ganin cewa Musa ya yashe su. Sai suka ƙera ɗan maraƙi na zinariya kuma suka ce: “Allolinka ke nan, Ya Isra’ila, waɗanda suka fishe ka daga ƙasar Masar.” (Fit. 32:1, 4) Suka soma bauta wa gunkin, suna miƙa masa hadaya, amma kuma wai Jehobah ne suke bauta wa. Sa’ad da Jehobah ya ga hakan, sai ya gaya wa Musa: “Da sauri sun ratse daga hanya wadda na umurce su.” (Fit. 32:5, 6, 8) Tun daga lokacin ne Isra’ilawa suka soma yin alkawari ga Allah, amma ba sa cikawa.—Lit. Lis. 30:2.
ƘARIN ALKAWURA BIYU DA ALLAH YA YI
13. Wane alkawari ne Allah ya yi wa Sarki Dauda, kuma yaya muka san cewa alkawarin game da zuriyar ce?
13 A lokacin da Sarki Dauda yake sarauta, Jehobah ya yi alkawura biyu da za su amfane dukan mutanen da suka yi masa biyayya. Da farko, ya yi wa Dauda alkawari cewa sarauta ba za ta rabu da zuriyarsa ba. (Zab. 89:35, 36; 132:11, 12) Hakan yana nufin cewa za a kira Zuriyar da aka yi alkawarinsa “Ɗan Dawuda.” (Mat. 1:1; 21:9) Dauda ya kira wannan zuriyar “Ubangiji,” domin matsayin Kristi zai fi nasa.—Mat. 22:42-44.
14. Wace rantsuwa ce Jehobah ya yi game da Zuriyar da aka yi alkawarinta, kuma yaya muka amfana daga wannan rantsuwar?
14 Na biyu, Jehobah ya hure Dauda ya annabta cewa wannan Sarki na musamman zai yi hidima a matsayin Babban Firist ga ’yan Adam. Dokar da Allah ya ba Isra’ila ta ce za a zaɓi firistoci daga ƙabilar Lawi, kuma za a zaɓi sarakuna daga ƙabilar Yahuda. Hakan yana nufin cewa sarki ba zai zama firist ba. Amma, Dauda ya annabta game da Sarki na nan, ya ce: “Ubangiji ya ce ma ubangijina, Ka zauna ga hannun damana, har in maida maƙiyanka matashin sawunka. Ubangiji ya yi rantsuwa, ba kuwa za shi tuba ba, Kai Firist ne har abada bisa tabi’ar Melchizedek.” (Zab. 110:1, 4) Kamar yadda Dauda ya ce, Yesu Kristi wanda shi ne zuriyar da aka yi alkawarinta yana sarauta yanzu a sama. Kuma shi Babban Firist ne, tun da yake yana taimakon waɗanda suka tuba su ƙulla dangantaka da Allah.—Karanta Ibraniyawa 7:21, 25, 26.
SABUWAR ISRA’ILA TA ALLAH
15, 16. (a) Isra’ila guda nawa ne aka ambata a cikin Littafi Mai Tsarki, kuma wace ce Allah ya yi wa albarka a yau? (b) Wane umurni ne Yesu ya ba mabiyansa game da rantsuwa?
15 Daga baya, Jehobah ya ƙi da al’ummar Isra’ila saboda ta ƙi Yesu Kristi, kuma hakan ya sa ta yi hasarar zarafin zama “mulki na firistoci.” Yesu ya ce wa shugabannin Yahudawa: “Za a amshe mulkin Allah daga hannunku, za a bayar ga al’umma mai-fitowa da ’ya’yansa.” (Mat. 21:43) An kafa wannan sabuwar al’ummar a Fentakos na shekara ta 33 a zamanin Yesu, sa’ad da aka zuba ruhun Allah a kan almajiran Yesu guda 120 da suka taru a Urushalima. Waɗannan ne suka zama “Isra’ila na Allah,” kuma ba da daɗewa ba, mutane da yawa daga wasu al’ummai suka bi su.—Gal. 6:16.
16 Wannan sabuwar Isra’ila ta yi dabam da Isra’ila ta dā, domin ta ci gaba da yin biyayya ga Allah. Wani umurni da waɗanda suke cikin sabuwar Isra’ila suka bi shi ne game da rantsuwa. Sa’ad da Yesu yake duniya, mutane sun mai da rantsuwa abin wasa, sukan yi rantsuwa a kan abin da ba gaskiya ba, da kuma abin da bai taka kara ya karye ba. (Mat. 23:16-22) Yesu ya ce wa mabiyansa: “Ba za ku yi rantsuwa ko kaɗan ba . . . bari zancenku ya zama, I, i; da A’a, a’a: abin da ya wuce waɗannan duka daga wurin Mugun ne.”—Mat. 5:34, 37.
17. Waɗanne tambayoyi ne za a amsa a talifi na gaba?
17 Shin hakan yana nufin cewa rantsuwa ba shi da kyau? Mene ne zancenka E ya zama E yake nufi? Za a ba da amsar waɗannan tambayoyin a talifi na gaba. Bari mu ci gaba da yin biyayya ga Jehobah yayin da muke bimbini a kan Kalmarsa. Shi kuma zai albarkace mu har abada bisa ga rantsuwa da kuma alkawarin da ya yi.
[Bayanin da ke shafi na 26]
Jehobah yana cika alkawuransa
[Hoto a shafi na 24]
Nan ba da daɗewa ba, Ibrahim zai ga cewa Jehobah ya cika alkawuransa