Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w12 9/15 pp. 28-32
  • Jehobah Yana Tattara Mutanensa Masu Farin Ciki

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Jehobah Yana Tattara Mutanensa Masu Farin Ciki
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2012
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • MUHIMMAN TARO DA AKA YI A ZAMANIN DĀ DA KUMA YANZU
  • LOKATAN YIN FARIN CIKI
  • ME YA SA YA KAMATA MU ƊAUKI TARON GUNDUMA DA MUHIMMANCI A YAU?
  • Taron Yanki Yana Ba Mu Damar Nuna Ƙauna
    Littafin Taro Don Rayuwa ta Kirista da Hidimarmu—2021
  • “Yarensu Dabam Amma Ƙauna ta Haɗa Su”
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2007
  • Taron Gunduma da Muke Yi Suna Ba da Shaida Mai Kyau Game da Gaskiya
    Hidimarmu Ta Mulki—2012
  • Tarurrukan Gunduma—Lokacin Yin Bauta da Farin Ciki
    Hidimarmu Ta Mulki—2010
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2012
w12 9/15 pp. 28-32

Jehobah Yana Tattara Mutanensa Masu Farin Ciki

‘Ka tattara jama’a, maza da mata da ƙanana da baƙo.’​—K. SHA 31:12.

MECE CE AMSARKA?

Waɗanne misalai ne suka nuna cewa tun da daɗewa, taron gunduma yana da muhimmanci ga bayin Jehobah?

Waɗanne sadaukarwa ne Isra’ilawa da yawa suka yi don su halarci idodi a Urushalima?

Me ya sa ya kamata ka tabbata cewa ba ka fasa halartar kowane sashe na taron gunduma ba?

1, 2. Mene ne za mu koya game da taron gunduma a wannan talifin?

A CIKIN shekaru da yawa, Shaidun Jehobah suna halartan taron ƙasashe da na gunduma. Yawancinmu mun halarci waɗannan taron, wataƙila ma sau da sau.

2 Mutanen Jehobah ma sun halarci irin waɗannan taron shekaru dubbai da suka shige. Yanzu za mu tattauna game da taron da mutanen Allah suka yi da aka rubuta a Littafi Mai Tsarki, kuma za mu koyi yadda suke da nasaba da taron da muke yi a yau. Kuma za mu koya game da abin da ya sa ya kamata mu halarci waɗannan taron.—Zab. 44:1; Rom. 15:4.

MUHIMMAN TARO DA AKA YI A ZAMANIN DĀ DA KUMA YANZU

3. (a) Mene ne ya faru a taro na farko da mutanen Jehobah suka taɓa yi? (b) Yaya Isra’ilawa suka san lokacin da ya kamata su taru?

3 Babban taro na farko da aka ambata a cikin Littafi Mai Tsarki shi ne wanda Isra’ilawa suka yi a Tudun Sinai, kuma Jehobah ne ya koyar da su. Wannan lokaci na musamman ne sosai a tarihin bauta ta gaskiya. A wannan taron, Jehobah ya nuna wa Isra’ilawa ikonsa kuma ya ba su Dokarsa. Wannan rana ce da ba za su taɓa mantawa ba. (Fit. 19:2-9, 16-19; karanta Fitowa 20:18; Kubawar Shari’a 4:9, 10.) A wannan ranar ce Jehobah ya canja salon dangantakarsa da Isra’ilawa. Ba da daɗewa ba bayan wannan ranar, Jehobah ya umurci Musa ya tara mutanen. Ya gaya wa Musa ya yi kakaki biyu na azurfa. Kuma duk sa’ad da aka hura waɗannan kakakin, ‘dukan jama’a za su taru a bakin ƙofar tent na taruwa.’ (Lit. Lis. 10:1-4) Ka yi tunanin irin farin cikin da mutanen suka yi a wannan taron!

4, 5. Me ya sa taron da Musa da Joshua suka yi suke da muhimmanci?

4 Sa’ad da Isra’ilawa suka kusan shekara 40 a cikin jeji, Musa ya tara al’ummar baki ɗaya. Suna dab da shiga cikin Ƙasar Alkawari. Saboda haka, Musa ya yi amfani da wannan lokacin don tuna musu dukan abubuwa masu kyau da Jehobah ya yi musu da kuma waɗanda zai yi musu bayan hakan.—K. Sha 29:1-15; 30:15-20; 31:30.

5 Wataƙila a wannan lokacin ne Musa ya gaya wa mutanen cewa za a yi wani taro na musamman. Ana bukatar dukan mazan da matan da kuma yaran har da baƙi su haɗu a wurin da Jehobah ya zaɓa. Kuma suna bukatar su yi hakan a duk shekara bakwai a lokacin Idin Bukkoki. A wannan taron, za su saurara ‘su koya, su ji tsoron Ubangiji Allahnsu, su kiyaye dukan zantattukan wannan shari’a domin su aikata.’ (Karanta Kubawar Shari’a 31:1, 10-12.) A bayyane yake cewa Jehobah yana son mutanensa su yi taro a kai a kai don su koyi dokokinsa da kuma nufe-nufensa. Bayan da Isra’ilawa suka halaka mutanen da suke Ƙasar Alkawari, sai Joshua ya tattara su. A lokacin akwai mutane masu bautar gumaka kewaye da su, kuma Joshua ya san cewa Isra’ilawa suna bukatar ƙarfafa don su kasance da aminci ga Jehobah. Sai Isra’ilawa suka yi alkawari cewa za su bauta wa Allah.—Josh. 23:1, 2; 24:1, 15, 21-24.

6, 7. Waɗanne taro masu muhimmanci ne aka yi a kwana kwanan nan?

6 A kwana kwanan nan ma, an yi taro masu muhimmanci. A waɗannan taron, an yi canje-canje a yadda ake gudanar da wasu abubuwa a ƙungiyar Jehobah da kuma yadda muke fahimtar wasu Nassosi. (Mis. 4:18) Taron gunduma na farko da Ɗaliban Littafi Mai Tsarki suka yi bayan Yaƙin Duniya na Ɗaya shi ne a birnin Cedar Point, Ohio, a Amirka, a shekara ta 1919. A wannan taron da mutane dubu bakwai suka halarta ne aka sanar cewa bayin Jehobah za su ƙoƙarta don yin wa’azi a dukan duniya. A wani taro na kwana tara da aka yi a wannan wurin a shekara ta 1922, Ɗan’uwa Joseph F. Rutherford ya ba da wani jawabi kuma a wannan jawabin, ya aririce masu sauraro. Ya ce: “Ku zama shaidun Ubangiji masu-aminci da kuma gaskiya. Ku ci gaba cikin yaƙin har sai an gama halaka Babila gaba ɗaya. Ku yi shelar saƙon a ko’ina. Dole ne duniya ta sani cewa Jehobah shi ne Allah kuma cewa Yesu Kristi shi ne Sarkin sarakuna da kuma Ubangijin iyayengiji. Wannan shi ne dukan ranar ranaku. Duba, Sarkin yana sarauta! Ku ne ma’aikatansa. Saboda haka, ku yi shela, ku yi shela, ku yi shelar Sarkin da kuma mulkinsa.” A sakamako, waɗanda suka halarci taron da kuma bayin Jehobah baki ɗaya suka soma wa’azi da ƙwazo sosai.

7 A shekara ta 1931, Ɗaliban Littafi Mai Tsarki suka sake yin wani taro a birnin Columbus a jihar Ohio kuma a wannan taron, sun samu wani sabon suna, wato Shaidun Jehobah. Sai kuma a shekara ta 1935 a birnin Washington, D.C., Ɗan’uwa Rutherford ya bayyana ma’anar “taro mai-girma” da littafin Ru’ya ta Yohanna ya ce “suna tsaye gaban kursiyin da gaban Ɗan ragon.” (R. Yoh. 7:9-17) Daga baya a shekara ta 1942 a lokacin Yaƙin Duniya na Biyu, Ɗan’uwa Nathan H. Knorr ya ba da wani jawabi mai jigo: “Peace—Can It Last?” [“Salama, Za Ta Dawwama Kuwa?”] A wannan jawabin da ya bayar, ya bayyana ma’anar bisa wanda “launinsa ja wur” ne da littafin Ru’ya ta Yohanna sura 17 ya ambata, kuma ya ce bayan yaƙin za a yi wa’azi sosai.

8, 9. Me ya sa mutane suka yi farin ciki sosai a wasu taron da aka taɓa yi?

8 A taron gunduma na “Glad Nations” [Al’ummai Masu Farin Ciki] da aka yi a shekara ta 1946, Ɗan’uwa Knorr ya ba da wani jawabi mai daɗi sosai mai jigo: “The Problems of Reconstruction and Expansion” [“Matsalolin Sake Gine-Gine da Kuma Faɗaɗa Su.”] Wani ɗan’uwa da yake kan dakalin yin magana sa’ad da Ɗan’uwa Knorr yake ba da jawabin ya bayyana yadda waɗanda suka hallara suka ji. Ya ce sa’ad da Ɗan’uwa Knorr ya sanar cewa za a faɗaɗa gidan Bethel da kuma ma’addaba da ke Brooklyn, mutane suka yi tafi sau da sau. Ya kuma ce ko da yake bai iya ganin fuskar kowa ba, amma a bayyane yake cewa sun yi farin ciki sosai. A taron ƙasashe da aka yi a shekara ta 1950 a birnin New York, waɗanda suka halarci taron sun yi farin ciki sa’ad da aka fito da juyin Littafi Mai Tsarki na New World Translation of the Christian Greek Scriptures. Wannan ne Littafi Mai Tsarki na farko na zamaninmu da aka saka sunan Allah daidai yadda yake tun asali.—Irm. 16:21.

9 An yi taron gunduma ma a wasu ƙasashe da ake tsananta wa Shaidun Jehobah a dā ko kuma ba a ƙyale su su yi wa’azi ba. Kuma waɗanda suka hallara sun yi bala’in farin ciki. Alal misali, shugaban ƙasar Jamus, Adolf Hitler ya ce zai halaka Shaidun Jehobah daga ƙasar baki ɗaya. Amma a shekara ta 1955 a birnin Nuremberg, Shaidun Jehobah 107,000 suka yi taron gunduma a wannan filin taro da Hitler yake yin taro da masu goyon bayansa a dā. Yawancin waɗanda suka halarci wannan taron sun zubar da hawaye saboda matuƙar farin ciki! A shekara ta 1989, ’yan’uwa 166,518 sun halarci taron gunduma na “Godly Devotion” [“Ibada ga Allah”] a ƙasar Folan wanda aka yi a wurare uku. Mutane da yawa sun zo daga ƙasar Rasha ta dā da Czechoslovakia da kuma wasu ƙasashe da ke Gabashin Turai. Wannan lokaci na farko ne da wasu cikinsu suka taɓa halartar taro da bayin Allah fiye da 15 ko 20 suka hallara. Kuma ka yi tunanin yadda ’yan’uwa suka yi farin ciki a taron ƙasashe na “Divine Teaching” [“Koyarwar Allah”] a birnin Kiev a ƙasar Ukraine, sa’ad da mutane 7,402 suka yi baftisma. Wannan ne taro na farko na Shaidun Jehobah a zamaninmu da aka taɓa yi wa mutane 7,402 baftisma a rana ɗaya.—Isha. 60:22; Hag. 2:7.

10. Wane taron gunduma ne ka yi farin cikin halarta sosai kuma me ya sa?

10 Wataƙila kai ma ka taɓa halartar taron gunduma da ya sa ka farin ciki sosai. Ka tuna taron gunduma na farko da ka taɓa halarta ko kuma wanda aka yi maka baftisma? Wannan lokaci ne na musamman a bautarka ga Jehobah, kuma kada ka taɓa manta da shi.—Zab. 42:4.

LOKATAN YIN FARIN CIKI

11. Wane idi ne Allah ya ce Isra’ilawa su riƙa halarta a duk shekara a dā?

11 A zamanin dā, Jehobah ya umurci Isra’ilawa su riƙa yin idi sau uku a Urushalima a duk shekara. Kuma waɗannan su ne Idin Gurasa Marar-Yeast da Idin Mako-Mako (da ake kira Fentakos daga baya) da kuma Idin Bukkoki. Jehobah ya gaya wa Isra’ilawa: ‘Sau uku a shekara dukan mazajenka za su bayana a gaban Ubangiji Yahweh.’ (Fit. 23:14-17) Mazaje da yawa sun san cewa wannan idin yana da amfani sosai, kuma suna halarta tare da iyalansu.—1 Sam. 1:1-7; Luk 2:41, 42.

12, 13. Mene ne Isra’ilawa da yawa suke yi don su halarci idin da ake yi shekara-shekara?

12 Ka yi tunanin yadda kowace iyali na Isra’ila za su yi wannan tafiya mai nisa. Alal misali, Yusufu da Maryamu sun yi tafiyar mil 60 daga Nazarat zuwa Urushalima. Idan kana riƙe da ƙananan yara, kana tsammani za ka yi kwana nawa a hanya kafin ka isa Urushalima? Littafi Mai Tsarki ya faɗa cewa akwai wani lokaci da Yesu ya halarci wannan idin sa’ad da yake ƙarami. A wasu lokatai, sukan yi wannan tafiyar tare da dangi da kuma abokai. Ka yi tunanin yadda suke yin tafiya tare, sai su dafa abinci tare kuma bayan haka, sai su nemi wurin kwana a yankunan da ba su sani ba. Mun san cewa akwai kwanciyar hankali a wurin domin iyayen Yesu sun ƙyale shi ya samu ’yanci duk da yake shi ɗan shekara 12 ne a lokacin. Ka yi tunanin yadda musamman yara za su ji daɗin wannan taron.—Luk 2:44-46.

13 Sa’ad da Isra’ilawa suka soma zama a ɓangarori dabam-dabam na duniya, har ila suna halartar waɗannan idodin. A Fentakos na shekara ta 33, Yahudawa da wasu bayin Jehobah sun nuna cewa wannan idin yana da amfani sosai. Sun yi tafiya daga ƙasashe kamar su Italiya da Libiya da Karita da Asiya Ƙarama da kuma Mesopotamiya.—A. M. 2:5-11; 20:16.

14. Wane amfani ne Isra’ilawa suke samu sa’ad da suka halarci idi na shekara-shekara?

14 Abin da Isra’ilawa masu aminci suka fi so da wannan taron shi ne cewa za su bauta wa Jehobah tare da dubban mutane da suke ƙaunarsa. Yaya hakan zai shafi waɗanda suka halarci taron? Sa’ad da Jehobah yake wa bayinsa magana game da Idin Bukkoki, ya ce: “Za ka yi murna da idinka, da kai, da ɗanka, da ɗiyarka, da bawanka, da baiwarka, da Ba-levi, da baƙo, da maraya, da gwamruwa, waɗanda ke cikin ƙofofinka. Kwana bakwai za ka yi idi ga Ubangiji Allahnka a wurin da Ubangiji za ya zaɓa: domin Ubangiji Allahnka za ya albarkace ka cikin dukan amfaninka, da dukan aikin hannuwanka, za ka fa cika da murna sarai.”—K. Sha 16:14, 15; karanta Matta 5:3.

ME YA SA YA KAMATA MU ƊAUKI TARON GUNDUMA DA MUHIMMANCI A YAU?

15, 16. Waɗanne sadaukarwa ne ka taɓa yi don ka halarci taron gunduma? Me ya sa hakan kwalliya ce da ke biyan kuɗin sabulu?

15 Waɗannan idodin da aka yi a Urushalima misalai ne masu kyau ga bayin Allah a yau. Da akwai nasaba da yawa tsakanin idodin da aka yi a dā da taron gunduma da muke yi a yau. Kamar mutanen Allah a dā, mu ma a yau muna sadaukar da abubuwa da yawa don mu halarci taro. Duk da haka, muna farin cikin yin waɗannan sadaukarwar domin kwalliya ce da ke biyan kuɗin sabulu. Har wa yau, waɗannan taron suna da muhimmanci sosai a bautarmu ga Jehobah. Waɗannan bayanai da kuma ƙarin haske da muke samu a taron suna taimaka mana mu ƙarfafa dangantakarmu da Allah. Taron na taimaka mana mu yi amfani da abubuwan da muke koya kuma yana sa mu guje wa matsaloli. Har ila, suna sa mu daina alhini da yawa, kuma suna motsa mu mu biɗi abubuwan da za su sa mu farin ciki.—Zab. 122:1-4.

16 Waɗanda suke halartan taron suna yin farin ciki. A shekara ta 1946, wani rahoto ya nuna cewa abin ban sha’awa ne ganin dubban Shaidun Jehobah suna taro da farin ciki a wuri ɗaya. Abin sha’awa ne sosai a ji kaɗe-kaɗe da kuma muryoyin ’yan’uwa suna rera waƙar yabo ga Jehobah. Rahoton ya kuma ce mutane da yawa sun ba da kansu don yin hidima a sashe dabam-dabam na taron. Sun yi farin ciki sosai don yi wa ’yan’uwansu hidima. Kai ma ka taɓa yin farin ciki haka sa’ad da ka halarci taron gunduma ko kuma taron ƙasashe?—Za 110:3; Ish 42:10-12.

17. Waɗanne canje-canje ne aka yi a yadda ake tsara taron gunduma a yau?

17 Akwai wasu abubuwa da suka canja a yadda ake tsara taron gunduma. Alal misali, wasu Shaidun Jehobah ba su manta da lokacin da ake taron gunduma na tsawon kwanaki takwas ba! A lokacin, ana yin sashen safe da na rana da kuma na yamma. Kuma ana fita yin wa’azi. A wasu lokatai, ana soma taron da ƙarfe tara na safe kuma a kammala da ƙarfe tara na dare. Waɗanda suka ba da kansu suna aiki tuƙuru na sa’o’i da yawa don dafa abincin safe da rana da kuma yamma. Amma a yau, an daina yin irin wannan taro na kwanaki takwas. Yawancin ’yan’uwa suna dafa abinci da kansu, kuma hakan yana sa su saurari jawaban da ake yi a taron sosai.

18, 19. Wane sashen taron gunduma kake morewa sosai, kuma me ya sa?

18 Akwai wasu abubuwa da aka daɗe ana yi a taron gunduma kuma muna yawan ɗokin ganinsu. Alal misali, muna samun ‘abinci a lotonsa’ daga jawabai da sababbin littattafai da suke taimaka mana mu fahimci annabce-annabce da koyarwar Littafi Mai Tsarki. (Mat. 24:45) Yawancinsu littattafai ne da za mu yi amfani da su don taimaka wa mutane su fahimci gaskiyar da ke Littafi Mai Tsarki. Wasan kwaikwayo da aka ɗauko daga Littafi Mai Tsarki yana kuma taimaka wa matasa da kuma tsofaffi su bincike kansu kuma su kāre kansu daga ra’ayin duniyar nan. Jawabin baftisma yana kuma taimaka wa dukanmu mu yi tunani a kan abin da ya fi muhimmanci a rayuwarmu. Kuma, muna farin cikin ganin waɗanda suka keɓe kansu ga Jehobah suna yin baftisma.

19 Babu shakka, an daɗe ana yin taron gunduma, kuma sashe ne na bauta ta gaskiya. Taron gunduma yana taimaka mana mu yi farin ciki kuma mu kasance da aminci ga Jehobah a mawuyacin lokatai. Yana kuma taimaka mana mu yi ayyuka da yawa a hidimar Jehobah. Muna samun zarafin haɗuwa da sababbin abokai kuma muna sanin cewa muna cikin ’yan’uwanci na dukan duniya. Taron gunduma hanya ce ta musamman da Jehobah yake kula da kuma yi wa mutanensa albarka. Ya kamata kowannenmu ya tabbata cewa bai fasa halartar kowane sashe na taron gunduma ba.—Mis. 10:22.

[Hoto a shafi na 30]

Taron ƙasashe da aka yi a Birnin New York a shekara ta 1950

[Hoto a shafi na 32]

MOZAMBIK

[Hotona a shafi na 32]

KORIYA TA KUDU

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba