Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w12 9/15 pp. 23-27
  • ‘Ba Ku San Ranar Ko Sa’ar ba’

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • ‘Ba Ku San Ranar Ko Sa’ar ba’
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2012
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • AMFANIN YIN TSARO
  • SHAFAFFU SUN NUNA SUNA A SHIRYE
  • MU NUNA CEWA MUNA A SHIRYE
  • KA CI GABA DA YIN TSARO
  • An Iske ‘Bawan Da Aminci’ A Lokacin Bincike!
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2004
  • Kana Bin Gargadin Yesu?
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2024
  • Ka Ci Gaba da ‘Yin Tsaro!’
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2015
  • “Ku Zauna A Faɗake”—Lokacin Hukunci Ya Yi!
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2005
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2012
w12 9/15 pp. 23-27

‘Ba Ku San Ranar Ko Sa’ar ba’

“Ku yi tsaro fa, gama ba ku san rana ko sa’a ba.”—MAT. 25:13.

MECE CE AMSARKA?

Me ya sa yake da kyau da ba mu san rana ko sa’ar da ƙarshen zai zo ba?

Ta yaya shafaffu suka yi tsaro?

Ta yaya za mu nuna cewa muna shirye don zuwan Kristi?

1-3. (a) Waɗanne misalai ne za su taimaka mana mu fahimci almara guda biyu da Yesu ya ba da? (b) Waɗanne tambayoyi ne muke bukatar mu amsa?

A CE wani babban ma’aikacin gwamnati ya ce ka tuƙa shi a mota zuwa wani taro na musamman. ’Yan mintoci kafin ka je ka same shi sai ka lura cewa babu isashen māi a motarka. Sai ka tafi ka sayo mān. Da ka tafi sai ma’aikacin ya iso. Ya neme ka ya rasa. Da ya ga ba zai iya jiranka ba sai ya gaya wa wani ya tuƙa shi zuwa wurin taron. Sa’ad da ka dawo, ka ga cewa ma’aikacin ya tafi ya bar ka. Yaya za ka ji?

2 A ce kai ne ma’aikacin kuma ka zaɓi ƙwararrun maza guda uku don su gudanar da sana’arka. Ka bayyana musu abin da za su yi kuma dukansu suka yarda za su yi hakan. Amma, sa’ad da ka dawo sai ka lura cewa guda biyu ne a cikinsu suka yi aikin da ka ba su. Ɗayan kuma ya ba da hujjar da ya sa bai yi aikin ba. Bai ma yi ƙoƙarin yin aikin ba. Yaya za ka ji?

3 Yanayin da muka tattauna yanzu ya yi daidai da almara guda biyu na budurwoyi da na talanti da Yesu ya ba da. Dukan almaran suna magana game da lokaci na ƙarshe kuma sun nuna dalilin da ya sa wasu Kiristoci shafaffu za su kasance da aminci da kuma hikima amma wasu ba za su yi hakan ba.a (Mat. 25:1-30) Yesu ya nanata darasin da aka koya daga cikin waɗannan almaran, yana cewa: “Ku yi tsaro fa, gama ba ku san rana ko sa’a ba.” Yana nufin cewa almajiransa ba za su san daidai lokacin da zai halaka duniyar Shaiɗan ba. (Mat. 25:13) Ya kamata mu ma mu bi wannan shawarar a yau. Yaya za mu amfana ta wajen yin tsaro kamar yadda Yesu ya ƙarfafa mu mu yi? Su waye ne suka kasance a shirye don su samu ceto? Kuma mene ne zai taimaka mana mu yi tsaro?

AMFANIN YIN TSARO

4. Me ya sa ba ma bukatar mu san ainihin lokacin da ƙarshen zai zo ba don mu yi tsaro?

4 A wasu lokatai yana da muhimmanci a san lokacin yin wani abu. Alal misali, a ce kana aiki a kamfani ko kana son ka ga likita ko kuma kana son ka shiga bas ko jirgin ƙasa, wajibi ne ka san lokacin yin waɗannan abubuwan don kada ka makara. Amma, bai kamata mutumin da ke kashe gobara ko kuma wanda yake ƙoƙarin ceton ran mutane bayan an yi bala’i ya damu da lokaci ba. A irin waɗannan yanayin, ya fi kyau a mai da hankali ga aikin da ake yi maimakon damuwa da lokaci. Hakazalika, wa’azin da muke yi yana taimaka wa mutane su san abin da Jehobah ya yi don ya ceci mutane. Wannan aikin ya fi muhimmanci yanzu domin ƙarshen wannan zamanin yana kusatowa. Da akwai hanyoyi biyar da za mu amfana don ba mu san ainihin rana ko kuma sa’ar da ƙarshen zai zo ba.

5. Ta yaya za a san abin da ke cikin zuciyarmu da yake ba mu san ranar ko sa’ar da ƙarshen zai zo ba?

5 Dalili na farko da ya sa ya dace da ba mu san lokacin da ƙarshen zai zo ba shi ne don mu nuna ainihin abin da ke cikin zuciyarmu. Jehobah yana daraja mu ta wajen ba mu ’yanci mu zaɓa ko za mu kasance da aminci a gare shi. Muna bauta wa Jehobah don muna ƙaunarsa ba domin muna son mu tsira daga ƙarshen wannan zamanin kuma mu samu rai madawwami ba. (Karanta Zabura 37:4.) Muna farin ciki idan muka yi nufin Allah kuma muka fahimci cewa yana koyar da mu domin yana son mu amfana. (Isha. 48:17) Ba ma jin cewa bin dokokinsa suna da wuya ainun.—1 Yoh. 5:3.

6. Yaya Allah yake ji sa’ad da muka bauta masa domin muna ƙaunarsa kuma me ya sa?

6 Dalili na biyu da ya sa yake da kyau da ba mu san ranar ko sa’ar ba shi ne don hakan zai ba mu zarafin faranta wa Jehobah rai. Yana da kyau mu bauta wa Jehobah domin muna ƙaunarsa ba don ƙarshen ya kusa ba. Yin hakan zai sa Jehobah ya nuna cewa magabcinsa Shaiɗan maƙaryaci ne. (Ayu. 2:4, 5; karanta Misalai 27:11.) Muna farin cikin goyon bayan sarautar Jehobah kuma mu ƙi na Shaiɗan, domin mun san cewa Shaiɗan ya jawo mana matsaloli masu yawa.

7. Me ya sa kake son ka yi amfani da rayuwarka don ka bauta wa Allah da kuma taimaka wa mutane?

7 Dalili na uku da ya sa yake da kyau da ba mu san ainihin lokacin da ƙarshen zai zo ba shi ne, yana sa mu bauta wa Allah kuma mu taimaki mutane. Wasu mutane a yau da ba su san Allah ba sun gaskata cewa ƙarshen duniya zai zo. Da yake suna jin tsoro cewa za a yi bala’in da zai halaka duniya, shi ya sa suke da ra’ayin, “bari mu ci mu sha, gama gobe za mu mutu.” (1 Kor. 15:32) Amma, mu ba ma jin tsoro. Ba ma kula da kanmu kawai. (Mis. 18:1) Maimakon haka, muna saka yin nufin Jehobah kan gaba a rayuwarmu, kuma muna yin amfani da kome da muke da shi har da lokacinmu da ƙarfinmu don mu gaya wa mutane game da Mulkin Allah. (Karanta Matta 16:24.) Bauta wa Allah tana sa mu farin ciki, musamman sa’ad da muka taimaka wa mutane su koya game da shi.

8. Wane misali ne da ke cikin Littafi Mai Tsarki ya nuna cewa muna bukatar mu dogara gabaki ɗaya ga Jehobah da kuma Kalmarsa?

8 Dalili na huɗu da ya sa yake da kyau da ba mu san ranar ko sa’ar ba shi ne don hakan yana taimaka mana mu dogara ga Jehobah gabaki ɗaya kuma mu yi iya ƙoƙarinmu mu yi abin da ke cikin Kalmarsa. Da yake mu ajizai ne, yana da sauƙi mu dogara ga kanmu. Bulus ya gargaɗi dukan Kiristoci: “Wanda ya ke maida kansa yana tsaye, shi yi lura kada ya fāɗi.” Ya ambata Isra’ilawa guda 23,000 da suka yi wa Jehobah rashin biyayya kuma suka mutu kafin su shiga Ƙasar Alkawari. Bulus ya ce, “waɗannan al’amura . . . aka rubuta su domin gargaɗi garemu, mu waɗanda matuƙan zamanu sun zo a kanmu.”—1 Kor. 10:8, 11, 12.

9. Ta yaya gwaje-gwaje za su ƙarfafa bangaskiyarmu da kuma abotarmu da Jehobah?

9 Dalili na biyar da ya sa yake da kyau da ba mu san lokacin da ƙarshen zai so ba shi ne don zai sa mu koyi darasi daga matsalolin da muke fuskanta kuma hakan zai ƙarfafa bangaskiyarmu. (Karanta Zabura 119:71.) Littafi Mai Tsarki ya ce a kwanaki na ƙarshe “miyagun zamanu za su zo.” (2 Tim. 3:1-5) Mutane da yawa a cikin duniyar Shaiɗan sun tsane mu, saboda haka, suna iya tsananta mana domin imaninmu. (Yoh. 15:19; 16:2) Idan muka kasance da tawali’u kuma muka nemi ja-gorar Allah a lokacin da muke fuskantar gwaji, za mu ƙarfafa bangaskiyarmu kamar yadda maƙeri yake sa ƙarfe a wuta don ya mulmula shi. Kuma ba za mu karaya ba. Maimakon haka, za mu kusaci Jehobah sosai yadda ba mu tsammani ba.—Yaƙ. 1:2-4; 4:8.

10. Me zai sa lokaci ya shige da sauri?

10 Lokaci yakan shige da sauri ko kuma ya yi jinkiri. Lokaci yakan shige da wuri idan muka shagala da aiki kuma ba ma kallon lokaci. Haka nan ma, idan muka shagala a yin aikin da Jehobah ya ce mu yi, ƙarshen zai zo da wuri fiye da yadda muke tsammani. Yawancin shafaffu sun kafa mana misali mai kyau a wannan batun. Bari mu ɗan yi bitar abin da ya faru bayan da aka naɗa Yesu Sarki a shekara ta 1914 da kuma yadda wasu suka kasance a shirye kuma wasu ba su yi hakan ba.

SHAFAFFU SUN NUNA SUNA A SHIRYE

11. Me ya sa wasu shafaffu suke ganin Yesu ya makara bayan shekara ta 1914?

11 Ka tuna da almarar Yesu game da budurwoyi da kuma talanti. Da a ce budurwoyi ko kuma bayi da ke cikin almarar Yesu sun san lokacin da angon ko kuma shugabansu zai zo, da ba za su bukaci yin tsaro ba. Suna bukatar su kasance a shirye da yake ba su san lokacin da shugabansu zai zo ba. Shekaru da yawa yanzu, shafaffu sun san cewa shekara ta 1914 za ta zama shekara ta musamman, amma ba su fahimci ainihin abin da zai faru ba. Sa’ad da abubuwa ba su faru ba yadda suke tsammani, wasu cikinsu suka soma tunani cewa Yesu ya makara. Wani ɗan’uwa ya tuna abin da ya faru, “wasu cikinmu suna ganin cewa za mu tafi sama a mako na farko na watan Oktoba a wannan shekarar.”

12. Ta yaya shafaffu suka kasance da aminci da hikima?

12 Babu shakka, wasu sun yi sanyin gwiwa don ƙarshen bai zo ba yadda suke tsammani! Bugu da ƙari, ’yan’uwan sun sha wahala sosai domin an tsananta musu a lokacin Yaƙin Duniya na ɗaya. An kusan daina aikin wa’azi gabaki ɗaya. A alamance, kamar dai shafaffun sun yi barci. Amma a shekara ta 1919, wani abu ya sa suka farka! Yesu ya zo ya bincika dukan waɗanda suke da’awa su Kiristoci ne. Yesu ya samu wasu cikin shafaffun da aibi kuma saboda haka ba za su ƙara yi masa aiki ba. (Mat. 25:16) Ba su yi tsaro ba, suna kama da budurwoyi marasa hikima da ba su saka māi a cikin fitilunsu ba. Kuma kamar bawa wanda ba shi da aminci ga shugabansa, ba sa shirye su yi sadaukarwa don Mulkin. Amma yawancin shafaffu sun kasance da aminci kuma suna da ƙwazon yi wa Shugabansu hidima ko a shekarun da ake wahala sosai don yaƙi.

13. Wane hali ne shafaffu suka kasance da shi bayan shekara ta 1914 da kuma a yau?

13 Bayan shekara ta 1914, mujallar Hasumiyar Tsaro ta bayyana halin yawancin shafaffu a lokacin. Ta ce waɗansu da suke da halin kirki ba su yi sanyin gwiwa ba. Mujallar ta ci gaba da cewa: “Ba ma son a yi nufinmu. Saboda haka, sa’ad da muka fahimci cewa abin da muke sa rai zai faru a watan Oktoba ta shekara ta 1914 ba daidai ba ne, mun yi farin ciki cewa Ubangiji bai canja nufinsa don ya dace da ra’ayinmu ba. Ba ma son ya canja nufinsa.” Shafaffun suna son su fahimci nufin Allah sosai. Shafaffu a yau suna da irin wannan halin tawali’u kuma suna son su yi nufin Allah. Ba sa da’awa cewa an hure su. Suna son su yi aikin da Yesu ya ce su yi a duniya. Kuma yanzu Kiristoci da suke da begen yin rayuwa har abada a duniya, wato, “taro mai-girma” da suka fito daga “waɗansu tumaki” suna yin koyi da misalinsu.—R. Yoh. 7:9; Yoh. 10:16.

MU NUNA CEWA MUNA A SHIRYE

14. Me ya sa yake da kyau mu yi biyayya ga abin da bawan nan mai aminci, mai hikima yake koyarwa?

14 Kamar yadda Kiristoci shafaffu suke a faɗake, hakan ma taro mai girma suke manne wa bawan nan mai aminci, mai hikima da ke koya mana game da Jehobah. A sakamako, yana kamar su ma suna cika fitilunsu da māi daga Kalmar Allah da kuma ruhunsa. (Karanta Zabura 119:130; Yohanna 16:13.) Kuma hakan zai ƙarfafa su su kasance a shirye sa’ad da Kristi zai dawo. Kuma suna da ƙarfin kasancewa da aminci har a cikin yanayi mai wuya sosai. Alal misali, ’yan’uwa suna da Littafi Mai Tsarki guda ɗaya tak, a cikin wani sansani na ’yan Nazi. Saboda haka, suka yi addu’a su samu ƙarin littattafai. Ba da jimawa ba, suka ji cewa wani ɗan’uwa da aka kawo cikin sansanin ba da daɗewa ba yana da wasu kofi na Hasumiyar Tsaro da ya ɓoye a cikin ƙafarsa ta katako. Wani ɗan’uwa shafaffe mai suna Ernst Wauer wanda ya tsira a lokacin ya ce Jehobah ya taimaka wa ’yan’uwan a hanya mai ban al’ajabi don su haddace abubuwa da za su ƙarfafa su a cikin talifofin. Ya ƙara cewa: “Yanzu yana da sauƙi a samu tanadi da zai taimaka mana mu ci gaba da dangantakarmu da Allah, amma muna nuna godiya don wannan tanadin kuwa? Ina da tabbaci cewa a nan gaba Jehobah zai albarkaci waɗanda suka dogara a gare shi da kasance da aminci, da kuma suka ci gaba da yin amfani da tanadinsa.”

15, 16. Ta yaya aka albarkaci wasu ma’aurata don ƙwazonsu a hidima, kuma wane darasi ne za ka iya koya daga labarinsu?

15 Waɗansu tumaki suna taimaka wa ’yan’uwan Kristi su ci gaba da aikin wa’azi. (Mat. 25:40) Ba su aikata ba kamar mugun bawan nan mai ƙyuya da ke cikin almarar Yesu. Suna a shirye su yi aiki sosai kuma su yi sadaukarwa don su saka al’amura na Mulkin farko a rayuwarsu. Alal misali, an gaya wa Jon da Masako su je su yi wa mutanen Sin da ke ƙasar Kenya wa’azi. Da farko ba sa son su je. Amma, bayan sun yi la’akari da yanayinsu kuma suka yi addu’a game da batun, suka tsai da shawara su ƙaura zuwa wurin.

16 Jehobah ya sa suka samu albarka mai yawa domin ƙwazonsu a hidima. “Muna jin daɗin wa’azinmu a nan” in ji su. Sun soma nazarin Littafi Mai Tsarki da mutane bakwai kuma sun samu sakamako masu kyau. Sun daɗa cewa: “Muna godiya ga Jehobah kowace rana don yadda ya sa muka zo nan.”’Yan’uwa da yawa sun nuna cewa suna son su shagala a bauta wa Allah ko da a wane lokaci ne ƙarshen zai zo. Ka yi la’akari da ’yan’uwa da yawa da suka sauke karatu daga Makarantar Littafi Mai Tsarki na Gilead ko kuma waɗanda suka ba da kansu don yin hidima a wasu ƙasashe. Za ka iya samun ƙarin bayani game da yin hidima a inda ake da bukata sosai ta wajen karanta talifin nan “Sun Ba da Kansu da Yardar Rai a Ƙasar Ecuador” da ya fito a Hasumiyar Tsaro ta 15 ga Yuli, 2012. Yayin da ka karanta abin da ’yan’uwa da suke hidima a wata ƙasa suka faɗa, ka yi tunanin yadda za ka ƙara yin hidima ga Allah. Hidimarka za ta sa a yabe Jehobah kuma ka ƙara farin ciki.

KA CI GABA DA YIN TSARO

17. Ta yaya rashin sanin ranar ko sa’ar da ƙarshen zai zo ya zama albarka a gare mu?

17 Bai kamata mu yi sanyin gwiwa don ba mu san ainihin rana ko kuma sa’ar da ƙarshen wannan zamanin zai zo ba. Maimako, hakan ya kasance albarka a gare mu. Ya taimaka mana mu shagala a yin nufin Allah kuma mun daɗa yin abota da Ubanmu Jehobah mai ƙauna. Muna farin ciki a bautarmu ga Jehobah domin mun mai da hankali ga aikin da Yesu ya ce mu yi kuma mun guji abubuwa masu raba hankali.—Luk 9:62.

18. Me ya sa za mu kasance da aminci a hidimarmu ga Allah?

18 Ƙarshen wannan zamanin ya kusa sosai, saboda haka ya kamata mu kasance da aminci a hidimarmu ga Allah. Ba ma son mu sa Jehobah ko Yesu baƙin ciki. Sun ba mu aiki mai ban al’ajabi da za mu yi a waɗannan kwanaki na ƙarshe. Muna godiya don yadda suka amince da mu!—Karanta 1 Timotawus 1:12.

19. Ta yaya za mu kasance a shirye don ƙarshen wannan zamanin?

19 Ko muna da begen yin rayuwa a sama ko kuma cikin Aljanna a duniya, za mu ci gaba da yin biyayya ga umurnin Allah na yin wa’azi da kuma almajirantarwa. Ba ma bukatar mu san ainihin rana ko lokacin da ranar Jehobah za ta zo ba. Za mu iya kasancewa a shirye kuma za mu yi hakan! (Mat. 24:36, 44) Muddin muka dogara ga Jehobah kuma muka saka Mulkinsa farko a rayuwarmu, muna da tabbaci cewa ba za mu yi da-na-sani ba.—Rom. 10:11.

[Hasiya]

a Ka duba Hasumiyar Tsaro ta 1 ga Maris, 2004, shafuffuka na 26-30.

[Hoto a shafi na 26]

Ka nemi tanadin da zai ƙarfafa dangantakarka da Jehobah ko a lokacin wahala

[Hoto a shafi na 27]

Lokaci yana shigewa da sauri idan muka shagala a hidimarmu ga Allah

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba