Daga Tarihinmu
Yin Tafiya Tare da Masu Kula Masu Ziyara
“BA ZAN iya yin wa’azi ƙofa-ƙofa ba!” Sababbin ɗaliban Littafi Mai Tsarki da yawa suna jin hakan game da yi wa mutum da ba su sani ba wa’azi. Amma ba sabon ɗalibin Littafi Mai Tsarki ba ne yi furta waɗannan kalmomin ba, wani ƙwararren ɗan’uwa ne mai kula mai ziyara da ke ba da jawabai da kuma koyar da Kalmar Allah.
Mutane da yawa da suke karanta Hasumiyar Tsaro ta Sihiyona kuma suka daina zuwa coci sun yi ɗokin kasancewa tare da waɗanda suke da irin ra’ayinsu don su koyi gaskiyar Littafi Mai Tsarki. Mujallar ta shawarce su su yi wannan taron a kai a kai. Somawa daga shekara ta 1894, ƙungiyar Jehobah ta tura masu kula masu ziyara su riƙa tuntuɓar ƙananan rukunoni da suke bukatar ziyara. An zaɓi waɗannan ’yan’uwan domin suna da tawali’u da ilimin Littafi Mai Tsarki da iya yin magana da koyarwa, kuma sun amince da hadayar fansa ta Yesu. Wannan ziyarar yana ɗaukan kwana ɗaya ko biyu. A rana ta farko da Ɗaliban Littafi Mai Tsarki da yawa sun fita yin wa’azi, sun rarraba takardar da ke gayyatar mutane zuwa jawabin da mai kula mai ziyara zai yi. Bayan an kammala wannan jawabin a wata makaranta, Ɗan’uwa Hugo Riemer, wanda daga baya ya zama ɗaya cikin ’yan Hukumar da ke kula da ayyukan Shaidun Jehobah ya amsa tambayoyi har bayan ƙarfe 12 na dare. Ko da yake ɗan’uwan ya gaji sosai, amma ya yi farin ciki don yadda taron ya kasance.
Hasumiyar Tsaro ta Sihiyona ta ce ainihin manufar aikin masu kula masu ziyara shi ne su ƙarfafa bayin Jehobah ta wajen yin taro a gidajen ’yan’uwa. Ɗaliban Littafi Mai Tsarki da suke kewayen suna taro don su saurari jawabai da kuma sashen tambayoyi ana ba da amsoshi. Ana kuma nuna ƙauna ga baƙi. Sa’ad da Maude Abbott take ƙarama, ta halarci wani taro da safe, bayan da aka kammala taron, sai kowa ya zauna kewaye da teburi a cikin gidan. “Aka ba mu naman alade da soyayyen kaza da burodi iri-iri da fanke da kuma kyat. Kowa ya ci abincin da yake so. Da misalin ƙarfe biyu na rana sai muka sake yin wani taro don mu saurari wani jawabi. Amma a lokacin, kusan kowa ya riga ya yi barci.” Wani ɗan’uwa wanda ya daɗe yana hidimar mai kula mai ziyara ya ce: ‘Da a ce na ci dukan abincin da aka ba ni, da tuni na riga na gama hidimata.’ Amma daga baya, sai hedkwatar da ke Brooklyn ta aiko da wata wasiƙa ga ’yan’uwa mata. A cikin wasiƙar, an shawarce su cewa zai fi dacewa su riƙa dafa wa masu kula masu ziyara abinci daidai wa daida, kuma yin hakan zai taimaki matan su riƙa samun lokacin yin barci sosai.
Masu kula masu ziyarar sun ƙware sosai wajen yin amfani da taswira da hotuna ko kuma kowanne abu da zai taimaki masu sauraro su fahimci koyarwar. Ɗan’uwa Richard Harvey Barber yana ba da jawabai masu daɗi sosai. Ɗan’uwa Walter J. Thorn yana magana cikin ƙauna kamar yadda uba yake wa yaransa magana kuma hakan ya yi kama da uban iyalai na zamanin dā. Wata rana da Ɗan’uwa Shield Toutjian yake tuƙa mota ƙirar Ford samfurin A, sai ya yi ihu farar ɗaya, “Tsaya!” Sai ya sauko daga motar, ya tsinka fure ya soma koya musu game da halittar Jehobah.
Hidimar mai kula mai ziyara yana tattare da ƙalubale sosai, musamman ga waɗanda suka soma tsufa. Ƙalubalen wasu kuma shi ne canjin da aka yi a hidimarsu. An ce su riƙa ja-gora a yin wa’azi gida-gida. Hasumiyar Tsaro ta 15 ga Maris, 1924 ta ce: ‘Wani aiki na musamman na Kiristoci na gaske shi ne su ba da shaida ga Mulkin. Kuma dalilin da ya sa ake aika masu kula masu ziyara ke nan.’
Wasu masu kula masu ziyara ba su so hakan ba kuma sun daina hidimar. Wasu ma sun je sun buɗe nasu cocin. Robie D. Adkins ya tuna abin da wani mai kula mai ziyara wanda ya iya jawabi sosai ya ce: “Ni dai abin da na iya yi shi ne yin wa’azi a kan bagadi. Ba zan iya yin wa’azi ƙofa-ƙofa ba!” Ɗan’uwa Adkins ma ya tuna abin da ya faru a lokacin: “Daga baya na gan shi a taron gunduma da aka yi a birnin Columbus, Ohio, a shekara ta 1924. Shi ne ya fi baƙin ciki a wannan ranar. Akwai dubban ’yan’uwa a wurin da suke farin ciki, amma ya tsaya shi kaɗai a ƙarƙashin wata ƙaramar bishiya. Tun daga ranar, ban sake ganinsa ba. Ya daina bauta wa Jehobah.” Akasin haka, “’yan’uwa da yawa masu farin ciki suna kai littattafai cikin motarsu,” sun ƙosa su yi wa’azi gida-gida.—A. M. 20:20, 21.
Masu kula masu ziyara da yawa suna jin tsoro kamar waɗanda aka ce su je su koyar, amma duk da haka, sun yi wa’azi da ƙwazo. Wani mai kula mai ziyara ɗan ƙasar Jamus mai suna Maxwell G. Friend ya yi magana game da wa’azi gida-gida. Ya ce: “Wannan sashe na aikin mai kula mai ziyara yana sa mu samu albarka sosai.” John Adams Bohnet ya ce yawanci ’yan’uwa sun amince da wannan gyaran da aka yi cewa a fi mai da hankali ga yin wa’azin Mulkin Allah. Ya ce, “yawancinsu sun kasance da ƙwazo sosai, kuma suna son su yi ja-gora a wannan hidimar.”
A cikin shekaru da yawa, waɗannan masu kula masu ziyara suna ƙarfafa ’yan’uwa maza da mata. Wani ɗan’uwa da ya daɗe yana bauta wa Jehobah mai suna Norman Larson ya ce: “Babu shakka, hidimar masu kula masu ziyara ya kawo sakamako mai kyau, ko da yake ni yaro ne a lokacin. Sun taimaka mini.” Har yau, masu kula masu ziyara suna da aminci kuma suna ba da kansu don taimaka wa ’yan’uwa su ce, “Za mu iya yin wa’azi ƙofa-ƙofa!”
[Bayanin da ke shafi na 32]
Mun yi farin ciki sosai a ranar da masu kula masu ziyara suka ziyarce mu!
[Hoto a shafi na 31]
A shekara ta 1905, Benjamin Barton yana da wurare 170 da zai kai ziyara
[Hoto a shafi na 32]
Walter J. Thorn mai kula mai ziyara ne, kuma ana kiransa Pappy, wato, Baba domin yana wa ’yan’uwa magana kamar yadda uba yake wa yaransa magana
[Hoto a shafi na 32]
An tura J. A. Browne yin hidimar mai kula mai ziyara a ƙasar Jamaica a shekara ta 1902 don ya ƙarfafa ƙananan rukunoni 14
[Hoto a shafi na 32]
Hidimar majagaba tana ƙarfafa bangaskiya da haɗin kai tsakanin Kiristoci, kuma tana sa ’yan’uwa su kasance a cikin ƙungiyar Jehobah