Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w12 8/15 p. 30
  • Ka Tuna?

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Ka Tuna?
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2012
  • Makamantan Littattafai
  • Jehobah Ya Ba Samson Karfi
    Darussa daga Littafi Mai Tsarki
  • Sarkin Ƙarfi
    Littafina na Labarun Littafi Mai Tsarki
  • Ka Dogara ga Jehobah Kamar Samson
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2023
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2012
w12 8/15 p. 30

Ka Tuna?

Ka ji daɗin karanta talifofin Hasumiyar Tsaro na kwanan bayan nan? Ka ga ko za ka iya amsa tambayoyi na gaba:

Shin gashin kan Samson ne ya sa shi ƙarfi?

Ba gashin kan Samson ba ne ya sa shi ƙarfi ba. Amma, abin da gashin yake wakilta ne, wato, dangantakarsa da Jehobah a matsayinsa na Banazare. Samson ya rasa dangantakarsa da Jehobah sa’ad da Delilah ta sa aka haske gashinsa.—4/15, shafi na 9.

Waɗanne abubuwa uku ne za su iya shafar zuciyarmu ta alama kamar yadda yake faruwa da zuciyarmu ta zahiri?

(1) Abinci. Kamar yadda zuciyarmu take bukatar abinci mai kyau don ta zama lafiyayye, muna bukatar cin abinci mai kyau na Kalmar Allah. (2) Motsa jiki. Muna bukatar mu riƙa motsa zuciyarmu ta alama ta wajen kasancewa da ƙwazo a hidima. (3) Mahalli. Muna samun kwanciyar hankali sa’ad da muke tare da ’yan’uwanmu da suke kula da mu.—4/15, shafi na 16.

Idan miji ya ci amanar matarsa ko kuma mata ta yi hakan, ta yaya za su sake amincewa da juna?

Ya kamata su (1) gaya wa juna gaskiya; (2) ba junansu haɗin kai; (3) gyara halinsu da (4) su san sa’ad da ya kamata su mance da abin da ya faru don su warware matsalar.—7/1, shafuffuka na 18-21.

Me ya sa ba zai dace ɗan’uwan da ke ba da jawabin jana’iza ya karanta Zabura 116:15 kuma ya ce wannan ya shafi mamacin ba?

Ayar ta ce: “Mutuwar ɗaya daga cikin tsarkakansa, abu mai daraja ne!” Hakan yana nufin cewa Jehobah ba zai ƙyale a halaka dukan amintattun bayinsa ba domin yana ɗaukansu da tamani. Ba zai ƙyale a halaka amintattun bayinsa gabaki ɗaya daga duniya ba.—5/15, shafi na 22.

Su waye ne colporteurs?

Kafin shekara ta 1931, ana kiran majagaba na kullum da wannan sunan.—5/15, shafi 31.

Su waye ne “dukan waɗannan mulkokin” da littafin Daniyel 2:44 ya ambata?

Yana nufin mulkoki ko gwamnatoci, da ke wakiltar ɓangarori dabam-dabam na sifar ƙarfe da Daniyel ya bayyana.—6/15, shafi na 17.

A wane lokaci ne Biritaniya da Amirka suka zama masu mulkin duniya na bakwai da aka kwatanta a cikin Littafi Mai Tsarki?

Biritaniya da Amirka sun soma sarauta tare sa’ad da suka haɗa kai a Yaƙin Duniya na Ɗaya.—6/15, shafi na 19.

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba